Matasan Afirka ba su da ƙwarin gwiwa a kan alƙiblar ƙasashensu - Rahoto

Wani sabon bincike ya gano cewa kaso biyu bisa uku na matasan Afirka ba su da ƙwarin gwiwa a kan alƙiblar ƙasashensu, to amma suna cike da ƙwarin gwiwa a kan burin da suka sanya a gaba.
Masu binciken sun tattauna da matasa fiye da 4,000 a ƙasashen Afirka 15 don gudanar da binciken.
Fiye da rabinsu sun ce suna so su bar ƙasarsu su tafi wata kasa, yayin da kashi 80 cikin 100 nasu kuma ke da burin fara kasuwanci da kansu.
Matasan sun ce ya kamata gwamnatocinsu su samar da ayyukan yi masu kyau fifiko, abin da zai iya rage cin haci da rashawa da kuma yakin da ake da sauyin yanayi.
Kuma hakan zai matuƙar taimakawa kasashen wajen samun ci gaba.

