Rundunar an sandan Najeriya ta babban birnin tarayyar asar Abuja ta ce arayi ne suka shiga wani rukunin gidaje a Unguwar Karsana suka yi sata ba masu satar mutane ba kamar yadda wasu rahotanni suka ce.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Abuja, Josephine Adeh, ta shaida wa BBC cewa "ba 'yan bindiga ba ne, ɓarayi ne kuma ba su saci kowa ba, sai kayayyaki da suka sata."
Tin da fari rahotanni daga wasu jaridun asar sun ce wani gungun 'yan fashi dauke da makamai ne suka kai hari rukunin gidaje na Efab Queens da ke Karsana Abuja da safiyar yau Litinin.
Amma wasu mazauna unguwar sun ce wa BBC 'yan fashi wanda akalla sun kai 30 ne suka je rukunin gidajen dauke da makamai inda suka rinka ɓalla ƙofofin gidaje suna shiga.
Mazauna wajen da BBC ta tuntuba sun ce, 'yan fashin ba su saci kowa ba, sai dai sun saci talbijin da sauran muhimman kayayyaki daga gidajen da suka shiga.
"Ba su kashe kowa ba, amma sun raunata mutum guda", inji mazauna unguwar, kuma daga baya jami'an 'yan sanda sun je sun fatattake su, ko da yake ba su kama kowa daga cikinsu ba.