Me zai faru a yau a wajen raba kasashen da za su gasar cin kofin duniya?

Kasashe 32 ne za su halarci wannan gasa.
Kuma a wannan yammaci ko wacce kasa za ta san inda ta dosa, a wane rukuni kuma take.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.
Umar Mikail and Umaymah Sani Abdulmumin

Kasashe 32 ne za su halarci wannan gasa.
Kuma a wannan yammaci ko wacce kasa za ta san inda ta dosa, a wane rukuni kuma take.
Hukumomin Saudiyya sun fitar da sanarwar tabbatar da ganin watan Azumin Ramadan a wasu yankunan ƙasar. Wannan na nufin gobe Asabar 2 ga watan Afrilu zai kasance 1 ga watan Ramadana.

Asalin hoton, EPA
Ministan Harkokin Waje na Rasha Sergei Lavrov ya ce kasarsa ta ji dadin yadda Indiya ke goyon bayanta a yakin da take yi a Ukraine.
Ministan na magana ne a birnin Delhi tare da takwaransa na Indiya, Subrahmanyam Jaishankar, wanda ya ce Indiya ta fi son ganin an sasanta dukkan matsaloli ta hanyar tattaunawa tsakanin masu takaddama da juna.
"Rasha ta ji dadin yadda Indiya ke kallon wannan matsalar kamar yadda ya dace, wato tana kallon duka bangarori, ba bangare daya ba," in ji Mista Lavrov.
Tattaunawar tasu za ta fi mayar da hankali kan yadda Rasha za ta sayar wa Indiya man fetur mai araha ba tare da Indiyar ta karya takunkuman da aka kakaba wa Rasha ba.

Asalin hoton, State House
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karɓi baƙuncin jagoran gwamnatin Chadi Janar Mahamat Idiss Derby a Abuja yau Juma'a.
Kodayake fadar shugaban ba ta yi ƙarin bayani kan abin da shugabannin biyu suka tattauna ba, Najeriya da Chadi na fuskantar hare-haren 'yan Boko Haram.
Kazalika, a ziyarar da ya kai Abuja jim kaɗan bayan ya hau mulki, Shugaba Buhari ya tabbatar wa shugaban wanda ɗan tsohon Shugaba Idriss Deby ne cewa Najeriya za ta taimaka wa ƙasarsa iya bakin ƙoƙarinta wajen komawa kan mulkin dimokuraɗiyya.
Haka nan, Buhari ya gana da jakadan Qatar a Najeriya, Dr Ali Bin Ghanem Al-Hajri.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Getty Images
Rasha ta ce ba za ta katse iskar gas da take sayarwa Turawan Yamma ba tukunna game da sharaɗin da ta sanya musu cewa sai dai su dinga biyan kuɗin cinikin da kuɗinta na rouble maimakon dala ko yuro.
A ranar Alhamis ne Shugaba Putin ya sanya wa wata doka hannu da ke tilasta wa masu sayen gas da man fetur ɗinta buɗe asusun ajiya da bankinta sannan kuma su biya kuɗin da rouble daga yau Juma'a.
Fadar Kremlin ta ce dokar ba za ta shafi odar da aka riga aka biya kuɗinta ba, amma zai shafi wadda aka yi bayan 1 ga watan Afrilu ko kuma zuwa tsakiyar watan.
Ƙasar na yunƙurin farfaɗo da darajar kuɗinta na rouble yayin da takukuman da ƙasashen Turai da Amurka suka ƙaƙaba mata suka dabaibaye tattalin arziƙinta.

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta samu kiraye-kirayen neman ɗauki fiye da 10,000 cikin kwana huɗu da suka wuce kacal ta manhajar kai ɗaukin gaggawa da ta ƙaddamar mai suna Rescue Me App.
An ƙaddamar da manhajar ce a shekarar da ta gabata don sauƙaƙa wa 'yan sanda kai ɗaukin gaggawa a wuraren aikata laifuka wadda ke amfani da layin sadarwa na GPS ko kuma intanet.
Sai dai rundunar ta ce ta dinga samun rahotanni na boge daga jama'ar gari, abin da ke hana manhajar yin aiki yadda ya kamata.
Kakakin 'yan sanda, Muyiwa Adejobi, ya ce tarin rahotannin na boge da ke kan manhajar "na haddasa mata damuwa da kuma kawo tsaiko".
Wasu 'yan Najeriya sun yi ƙorafin cewa manhajar ba ta aiki yadda ya kamata. Sai dai 'yan sanda sun ce "tana aiki yadda ya kamata", amma akwai "cunkoso" a kanta na rahotannin boge da ke jawo tsaiko.

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan tsakiyar Manchester United Bruno Fernandes ya tsawaita zamansa a ƙungiyar da shekara ɗaya.
Ɗan ƙwallon mai shekara 27 wanda ya koma ƙungiyar a Janairun 2020 kan kuɗi fan miliyan 47 biyan farko, yanzu yana kan yarjejeniya zuwa 2026 kuma wannan kwantaragin na da zaɓin tsawaita shi da shekara ɗaya.
Fernandes ya ci wa United ƙwallo 49 a wasa 117 a dukkan gasanni. Kazalika, ya bayar an ci ƙwallo 39.
"Ina son cimma ƙarin wasu abubuwan da yawa a nan, kuma haka su ma sauran ma'aikata da 'yan wasan," a cewarsa.
"Fiye da komai, muna son mu bai wa magoya baya haƙƙinsu."

Wasu hotuna da suka karaɗe duniya na nuna yadda sojojin Rasha ke harbin wani mutum yayin da hannayensa ke ɗage a sama kan wata babbar hanya da ke wajen birnin Kyiv a farkon watan Maris.
An kori sojojin Rasha daga yankin bayan mamayar da suka yi masa na wani ɗan lokaci.
Mun kirga gawarwakin mutum 13 akan wata hanya mai ban tsoro da ba ta wuce mita 200 ba tsakanin Mria da Myla, ƙauyukan da sunayensu ke nufin Buri da Sanyin Zuciyaa harshen Ukrane– ko kuma Dream and Sweetheart a Turance.
Biyu daga cikin wadanda aka kashe an tabbatar da fararen hular Ukraine ne, wadanda sojojin Rasha suka kashe. Amma har yanzu ba a tantance sauran ba –suna kwance a inda aka kashe su – saidai biyu daga cikinsu ne kawai ke sanye da kakin sojin Ukraine.
Tawagar BBC ta samu damar zuwa inda lamarin ya faru a kan babbar hanyar E-40 zuwa birnin Kyiv, saboda sojojin Ukraine sunƙwace yankin ne cikin sa'o'i 10 kacal da suka wuce.
Akwai alamomin yaki da luguden wuta a ko'ina a yankin. Gidajen mai da wani hotel da ya yi fice wajen shakatawa da gidajen abinci sun kasance a ɗaiɗaice. Luguden wuta ya bar alamomi a kan hanyoyin biyu.
An bar gawarwakin cikin wani hali na rashin kulawa, akwai alamar, tambayoyi da damuwa game da ko su wane ne su da kuma yadda suka mutu.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta rantsar da wani kwamati da zai bincika abin da ya faru bayan tashi daga wasa tsakanin Najeriya da Ghana, inda wasu 'yan Najeriya suka kutsa tsakiyar fili tare da kai hare-hare kan mutane.
Jim kaɗan bayan hura usur ɗin ƙarshe a yammacin Talata da ta gabata, dubban 'yan kallo suka afka wa filin wasan na Moshood Abiola National Stadium ƙunshe da fushin doke su da tawagar Black Stars ta yi a wasan neman shiga gasar Kofin Duniya ta 2022.
Wasu bidiyo da aka dinga yaɗawa a shafukan zumunta sun nuna magoya baya na lalata wasu kayayyaki na filin wasan da kuma yin watsi da kayan wasanni.
'Yan Najeriya da dama sun yi Allah-wadai da wannan ɗabi'ar, suna masu cewa "wasa ba hauka ba ne".
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Larson Fungate
Wata matashiya a arewacin Mozambique da aka zaci ta mutu kuma aka yi jana'izarta a watan Nuwamba ta bayyana a gidansu da ke ƙauyen Lindi.
Mazauna ƙauyen na cewa an taso gawar Eurélia Manuel Benjamim ne daga matattu, amma ita ta ce ta je yin aiki ne a gonar wani kawunta na 'yan watanni.
Wani jami'in gwamnatin yankin Montepuez ya faɗa wa kafar yaɗa labarai ta gwamnatin ƙasar cewa: "Sun yi dukkan bikin jana'izarta - da jana'iza da kuma ziyarar ƙabarinta - kuma alamu sun nuna ba a taɓa ƙabarin ba."
An tura tawagar ƙwararru zuwa Lindi don gudanar da bincike kan abin da aka binne a ƙabarin nata.

Asalin hoton, Ma'aikatar bayar da agajin gaggawa ta Rasha
Rasha ta yi zargin cewa wasu jirage masu saukar-ungulu na Ukraine sun kai hari kan wata defo din mai a wani birnin kasar.
Wani bidiyo da aka wallafa a shafin Tuwita ya nuna yadda wuta ta tashi a kusa da wasu rukunin gidaje da ke Belgorod, mai nisan kilomita 40 daga kan iyakar kasar da Ukraine.
Wasu hotuna sun nuna yadda wasu abubuwa da ake zaton rokoki ne sun kai hari a defo din man fetur.
Gwamnan yankin Vyacheslav Gladkov ya wallafa sako a Telegram yana mai cewa "wuta ta tashi a defo din man fetur saboda hari ta sama da jiragen helikwafta biyu na Ukraine suka kai, wanda ya fado kasar Rasha".
Ya kara da cewa "babu wanda aka kashe" a harin.
Hukumomin Ukraine ba su tattabar da zargin da Gwamna Gladkov ya yi ba.

Asalin hoton, @GovKaduna
Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya ce zai gana da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari bayan harin da 'yan fashi suka kai wa jirgin ƙasa na Kaduna zuwa Abuja.
El-Rufai ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyarar jaje ga mutanen Ƙaramar Hukumar Giwa ta jihar bayan hare-haren 'yan bindiga a makon da ya gabata da ya kashe fiye da mutum 50 a yankin.
"Ba wai gwamnati ba ta san abin da ke faruwa ba ne, muna sane. Kawai dai wasu ne da ya kamata su ɗauki mataki har yanzu ba su yi hakan ba," in ji shi.
Ya ƙara da cewa "za mu ci gaba da matsa wa shugaban ƙasa da jami'an tsaro don su ɗauki mataki".
Ku latsa hoton ƙasa ku saurari kalaman gwamnan:

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka Joe Biden ya bayar da umarnin fitar da yawan man da ba a taba fitar da shi ba daga ma'adanar ƙasar domin taimakawa wajen rage farashin man a duniya.
Mista Biden ya ce za a dinga fitar da ganga miliyan ɗaya a kowace rana har nan da wata shida.
Wakiliyar BBC ta ce da yake sanarwa a kan batun, Shugaba Biden ya ɗora alhakin tashin farashin mai a kan mamayar da Putin ke yi wa Ukraine, yana mai cewa Amurkawa ba za su taba shan wahala don wani dan kama-karya ya kaddamar da yaki ba.
Sai dai kuma masu sharhi na ganin cewa fitar da man mai yawa na wani lokaci ba zai amfanar da komai ba tun da Rasha wadda ita ce kasa ta biyu da take fitar da mai bayan Saudiyya ta dai na ba.

A Jihar Neja da ke arewacin Najeriya, an sake gano gawar mutum biyar da suka nitse bayan wani kwale-kwalen da suke ciki ya kife da su.
Mutanen da suka hadar da mata da yara sun nitse ne sakamakon dimauta da suka yi yayin da suke gudun harin da 'yan fashin daji suka kai musu a tsakiyar makon nan.
Shugaban hukumar agajin gaggawa ta Neja, Ibrahim Ahmed Inga, ya yi wa Aisha Bappa ƙarin bayani cewa ya zuwa yanzu an gano gawar mutum 13 a yankin Shiroro.
Latsa hoton ƙasa ku saurari hirar:
Ina kwananku, ina gajiya. Da fatan kun wayi hantsin Juma'atu babbar rana lafiya.
Umar Mikail ne ke muku maraba da shigowa shafin labarai kai-tsaye, wanda zai kawo rahotannin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.
Sai dai za mu fi mayar da hankali kan yaƙin Rasha a Ukraine da kuma Najeriya.
Ku biyo mu kawai ku sha labarai!