Rufewa
Anan nake bakwana da ku sai kuma gobe da yardar Allah...Umaymah Sani Abdulmumin ke muku fatan alheri. A kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.
Umar Mikail and Umaymah Sani Abdulmumin
Anan nake bakwana da ku sai kuma gobe da yardar Allah...Umaymah Sani Abdulmumin ke muku fatan alheri. A kwana lafiya.

Sarkin Musulmi a Najeriya, Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar ya yi kira ga dukkan Malamai da Limamai su mutunta dokoki da tsarin addinin Musulunci wajen gudanar da wa'azi ga dukkan darussa addini cikin watan Ramadan.
Sanarwa da ya fitar dauke da sa hanun wazirin Sokoto, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ta kuma umarci malamai suke lura da tsaro da dokokin Korona a lokacin gudanar da Tafsirai da wa'azi.
Sarkin ya kuma yi kira ga al'umma Musulmi su mayar da hankali wajen yi wa kasa addu'a don samun zaman lafiya da aminci cikin kwanciyar hankali da tsaro.

Asalin hoton, KSGV
Gwamnan jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, Nasir Ahmed El-Rufai ya ce 'yan Boko Haram ne suka tsara tare da aiwatar da hari kan jirgin kasa a Abuja zuwa Kaduna a jiharsa.
Gwamna ya bayyana haka ne a wannan Juma'a lokacin da ya ke yiwa manema labarai bayani kan sakamakon ganawarsu da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa.
El-Rufai ya ce harin ya yi sanadi mutuwar aƙalla Fasinjoji takwas da raunatar wasu 40 da kuma garkuwa da wasu da ba a san adadinsu ba.
Ya kuma shaida cewa an samu tattaunawa tsakanin iyalai da wadanda aka yi garkuwa da su, sai dai har yanzu 'yan bindigar ba su tambaye kuɗi ba, illa daga wajen mutum guda.
Amma gwamnan ya ce yana zargin watakil daga wajen gwmanatin za su neman diyya, ba daidaikun mutane ba ko iyalansu.

'Yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 17 a wasu hare-hare da suka kai kauyuka hudu da ke karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara.
Mazauna yankunan sun ce 'yan bindigar sun bude wuta kan mai uwa-dawabi a kauyen Kadaddaba da tsakar rana.
Rahotanni na cewa sun isa kauyukan ne akan babura suka buɗe wa mutane wuta lokacin da suke fitowa daga masallaci bayan sallah Azahar.
Har yanzu dai rundunar 'yan sanda ba su yi tsokaci ba kan hare-haren.
Wannan ne karo na uku da Ingila za ta hadu da Amurka a kofin duniya a mataki na rukuni,, sun hadu a 1950 sai kuma 2010.
Wannan ne karo na uku da Ingila ke haduwa da wata kasa sau uku a gasar kofin duniya daban-daban.
Ingila ta ci 8 daga cikin wasannin da ta yi 11 da USA ta yi canjaras 1 ta kuma yi rashin nasara 2, amma duka nasara 8 din da ta yi a wasannin sada zumunta ne.

Asalin hoton, KH
Za a sake haduwa tsakanin Ghana da Uruguay, masana da magoya baya ba za su kasa mantawa da kwallon da Suarez.
Kwallon da ta hana Black Stars zuwa wasan kusa da na karshe a 2010.
Tarihi mara dadi ga mutanen Ghana

Rukunin A: Qatar, Ecuador, Netherlands, Senegal
Rukinin B: England, Iran, USA, Scotland/Wales/Ukraine
Rukinin C: Argentina, Saudi Arabia, Mexico, Poland
Rukinin D: France, UAE/Australia/Peru, Denmark, Tunisia
Rukinin E: Spain, Costa Rica/New Zealand, Germany, Japan
Rukinin F: Belgium, Canada, Morocco, Croatia
Rukinin G: Brazil, Serbia, Switzerland, Cameroon
Rukinin H: Portugal, Ghana, Uruguay, South Korea
Portugal
Uruguay
South Korea
Qatar
Senegal
Netherlands
Ecuador
France
Denmark
Tunisia
UAE/Australia/Peru
Belgium
Morocco
Croatia
Spain
Germany
Japan
France
Denmark
Tunisia
Argentina
Mexico
Poland
England
Iran
USA
Qatar
Senegal
Netherlands
Abin sha'awa manyan kociyoyi sun fara karasawa dakin taron da za a raba rukunin kasashen da za su gasar cin kofin duniya a Qatar.
Kocin Faransa Didier Deschamps wanda ke rike da kofin duniya a isa wajen... daki ya dauki harama







Asalin hoton, Fifa
Wannan gasdar za ta iya zama ta karshe da Messi da Ronaldo za su iya halarta.
A gasar da za a yi mai zuwa da za a yi a North America Ronaldo zai kai shekara 41 da haihuwa a duniya.
Si kuwa dan wasan Argentina Messi zai cika 39 a lokacin.
Shi akwai alamar daya daga cikinsu zai iya cin gasar a karon farko a tarihi?