An ji karar makaman atilari ta karade gefen birnin Kyiv
An ji karar fashewar abubuwa kusa da birnin Kyiv a safiyar nan.
Wakiliyarmu kan kasashen duniya Lyse Doucet ta ce lamarin ya soma ne da jin karar amsa-kuwwa, da kuma manyan kararraki daga wajen birnin wadanda ta ji daga tsakiyar birnin.
Kazalika Jeremy Bowen, wanda shi ma yana birnin Kyiv, ya wallafa sakon Tuwita da ke cewa "an ji karar makaman atilari ta mamaye gefe zuwa tsakiyar birnin".
Babu tabbas kan ko dakarun Rasha ko na Ukraine ne suka yi harbe-harbe, a cewarsa.
A jiya bayan tattaunawar sulhu, Rasha ta ce za ta rage ayyukanta a kusa da babban birnin - alwashin da shugabannin kasashen Yamma suka yi kira a yi kaffa-kaffa da shi.

