China ta ce za ta bunƙasa dangantakarta da Rasha

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya

  1. Nan za mu rufe wannan shafin sai kuma gobe

  2. NDLEA ta kama masu ikirarin bokanci da miyagun ƙwayoyi a Legas

    Buba Marwa

    Asalin hoton, NDLEA

    Hukumar hana sha da fataucin miagun kwayoyin ta Najeriya (NDLEA), ta ce ta kama wasu masu ikirarin bokanci, wadanda ake zargin suna cikin wata kungiya da ke safarar miyagun kwayoyi ta jirgin sama na Murtala Mohamed da ke Lagos.

    Kakakin hukumar ta NDLEA na kasa Femi Babafemi ya sanar da cewa wadanda aka kama a filin jirgin na Lagos suna dauke da kwayoyi samfurin TRAMADOL sama da miliyan ɗaya da rabi da kuma makudan kudade, kuma an kama su ne a cikin wannan wata na Maris.

  3. Giwaye sun kashe mutum 942 cikin shekara 10 a Indiya

    Wani minista a jihar Assam da ke arewa maso gabashin Indiya ya shaida wa majalisar jihar cewa giwaye sun kashe mutum 942 cikin shekara 10 da ta gabata.

    Parimal Suklabaiya, wanda shi ne ministan da ke kula da gandun daji da muhalli, ya ce giwayen sun kuma raunata fiye da mutum 770.

    Ministan ya ce giwayen na tafiya yankin Assam ne domin neman abinci, wanda ke haifar da karuwar matsala tsakaninsu da mutane.

    Jihar Assam ta kasance daya daga cikin jihohin Indiya mafi yawan dazuka inda ta ke da giwaye fiye da 5,500 da ke rayuwa cikin daji.

  4. Dan majalisar Birtaniya zai sauya jinsinsa

    Wani dan majalisa daga jam'iyyar Conservative mai mulki a Biritaniya ya ce yana shirin sauya jinsinsa domin zama dan majalisar dokokin kasar na farko da ya fito fili ya sauya jinsinsa.

    Jamie Wallis yana da shekara 37 kuma yana wakiltar wata mazaba ne a Wales.

    Ya ce an gano cewa yana fama da matsalar jinsi ta dysphoria – inda yake jin tunaninsa ya bambanta da jinsin da aka haife shi da shi.

    Sanarwarsa ta samu sakwanni na goyon baya, inda Firaminista, Boris Johnson, ya yaba wa Mista Wallis saboda jajircewarsa wajen bayyana labarinsa, yana mai cewa babu shakka zai taimaka wa wasu.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  5. An kama matar da ta sa aka ƙwaƙwalewa wa yaro ido a Kano

    SP Kiyawa

    Asalin hoton, SP Kiyawa

    Rundunar ƴan sandan Kano ta tabbatar da kama wata tsohuwa da ake zargin ta saka wani matashi mai shekara 17 ya ƙwaƙulewa wani yaro mai suna Mustapha Dahiru ido don a haɗa musu layar zana.

    Rundunar ƴan sanda ta ce ta kamo matar ne bayan koke da suka samu daga jama'ar unguwa da ƴan sa kai na yankin unguwar Dan Tsinke a karamar hukumar Tarauni a Kano.

    Tun kafin ƴan sanda su kai ga kamo matar da ake zargi da sa matashin ya cirewa yaron ido, kungiyar tsaro ta 'yan sa-kai ta Dan Tsinke da ke kusa da Unguwar Sheka suka kamo matashin da ake zargi da cirewa yaron ido ɗan shekaru 10-11.

    Matashin da ake zargi ya shaida musu cewar wata tsohuwa ce ta umarci da ya kawo mata ido don ta hada masa layar zana, kamar yadda Rabi'u Suleiman Mai Matasa mataimakin sakatare na kungiyar 'yan-sa kai ta Dan Tsinke a Kano ya cewa BBC.

    SP Abdullahi Kiyawa kakakin ƴan sanda a Kano ya tabbatar da faruwar al'amarin, ya kuma ja hankulan al'umma da su ringa sanya ido kan abubuwan da ke faruwa a kewayen su, don kaucewa afkuwar irin wannan lamari.

    Ko a makon da ya gabata sai da aka sami waji matashi da ya tura 'yar uwarsa a cikin rijiya, a yankin karamar hukumar Rimin Gado a Kano, tare da wani matashi da ya kashe wata yarinya, yar makwabcin gidansu, bayan da ya nemi kudin fansa.

  6. Kayan yaƙi da hukumomin Najeriya suka kama a Legas

    Drone

    Asalin hoton, Nig Custom

    Hukumar yaƙi da fasa ƙwauri ta Najeriya da ke tashar jiragen sama shiyyar NAHCO a birnin Legas ta kama tufafin sojoji masu yawa da ƙananan jiragen leƙen asiri na yaƙi marasa matuƙa masu yawa.

    Konturola Sambo Kayilil Dangaladima mai kula da shiyyar hukumar kwastam a tashar jiragen sama ta Murtala Muhammad ne ya bayyana wa BBC hakan a jiya Talata.

    Akwai kuma ƙwayar Tramadol ta sama da naira biliyan biyu da kuma wani ganyen shayi mai fitar da hankali da ake zargi an shigo da shi Bangladesh da kuma kusa da wani sashe na Saudiyya.

    kwastam

    Asalin hoton, Nug Custom

    ganyen shayi

    Asalin hoton, Nig Custom

    Hukumar kwastom ta hannunta wadannan makaman da kakin soje ga rundunar sojen Najeriya da kuma kwayoyi a hannun hukumar yaki da shan miyagun kwayoyi da kuma hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta NAFDAC.

  7. China ta ce za ta bunƙasa dangantakarta da Rasha

    Shugaban Rasha da na China

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan harkokin wajen China Wang Yi ya ce China ta dukufa domin bunkasa dangantakarta da Rasha.

    Yana jawabi ne bayan da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov ya sanar da shi halin da ake ciki a yakin Ukraine.

    Dukkan jami'an sun yi Allah-wadai da takunkuman da kasashen yamma suka kakaba wa Rasha, inda suka kira su marasa halarci.

    Wang Yi ya bayyana halin da ake ciki a matsayin "mai daure kai", kuma sakamakon "yakin cacar baki" ne.

    Mista Lavrov na halartar wani taron koli kan kasar Afghanistan ne da China ke daukar nauyinsa.

  8. Burundi ta ɗage haramcin hana BBC watsa labarai

    Burundi ta ɗage haramcin da ta yi wa BBC na watsa labarai tsawon shekaru uku bayan umarnin dakatar da ayyukanta a kasar.

    Hukumar yaɗa labaran Burundi ce ta janye lasisin bisa zargin keta dokokin aikin jarida da nuna rashin da'a.

    An haramta wa ƴan jarida yin aiki da BBC ta kowace hanya.

    Shugaban hukumar kula da harkokin yaɗa labarai ya ce a yanzu BBC ta cika sharuɗɗan da gwamnati ta gindaya kuma shugaba Evariste Ndayishimiye ya fara ɗage haramcin da aka sanya wa kafafen yaɗa labarai.

    Kasar Burundi dai tana ɗaya daga cikin ƙasashen da ƴancin jarida ke fuskantar ƙalubale

  9. Bruce Willis ya yi ritaya daga fitowa a fim

    Bruce Willis

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗaya daga cikin fitattun ƴan fim a Hollywood, Bruce Willis mai shekara 67 ya yi ritaya daga sana'arsa ta fitowa a fim.

    A wata sanarwa da iyalansa suka fitar, sun ce an gano cewa yana fama da matsalar magana a sanadiyar matsalar ƙwaƙwalwa.

    Willis ya yi fice wanda aka fi sani da sunan John McClane a fim dinsa da ya yi fice 1988, Die Hard.

  10. NFF ta bayyana takaicinta kan tarzomar filin wasan kwallon kafa a Abuja

    Abuja

    Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF, ta bayyana takaicinta kan tarzomar da ta biyo bayan wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da kungiyar kasar ta Super Eagles ta yi da Black Stars ta Ghana jiya Talata a filin wasa na tunawa da Mashood Abiola da ke Abuja inda aka tashi 1-1.

    Ta kuma bayyana alhini kan mutuwar wani jami’in hukumar kwallon kafa ta CAF a yayin wasan, tare da musanta ikirarin cewa tarzomar da aka samu ce ta yi sanadin mutuwarsa.

    Sakatare Janar na hukumar ta NFF, Muhammad Sanusi, ya shaida wa BBC cewa suna bai wa ‘yan Najeriya hakuri kan sakamakon wasan da ba kasar rashin cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta bana da za a yi Qatar.

  11. Saudiyya ta tsagaita wuta a yaƙin Yemen don zuwan Ramadan

    MBS

    An tsagaita wuta a yakin da ake gwabzawa a Yemen tsakanin hadakar kasashen da Saudiyya ke jagoranta da 'yan tawaye 'yan Houthi.

    Wannan matakin ya biyo bayan sanarwar da Saudiyyar ta fitar ne da ta ke cewa za ta daina kai hare-hare kan sansanonin 'yan Houthin saboda karatowar watan azumi na Ramadan.

    A halin da ake ciki, ana can ana gudanar da wani babban taro kan makomar kasar ta Yemen a Riyadh babban birnin kasar ta Saudiyya.

    Jakada na musamman na Majalisar Dinkun Duniya a Yemen Hans Grundberg ya ce ƴan Yemen na bukatar ganin yaƙin nan ya ƙare.

    "Kuma suna son zaman lumana mai dorewa ya wanzu. Suna kuma fatan ganin an tsagaita wuta nan take baya ga ɗaukar matakan rage tasirin yakin kan fararen hula.

  12. Jam'iyyar ƙawance a Pakistan ta sauya sheka daf da kaɗa ƙuri'ar yanke ƙauna a majalisar kasar

    Mambobin babbar jam'iyyar da ta ƙulla ƙawance da jam'iyya mai mulki a Pakistan, sun sauya sheka ana daf da kaɗa wata ƙuri'ar yanke ƙauna a majalisar kasar, matakin da ya jefa Firaminista Imran Khan cikin wani mawuyacin hali.

    Jam'iyyar MQM ta ce ta kulla wata yarjejeniya da jam'iyyar adawa ta kasar kuma za ta fitar da cikakken bayani nan ba da jimawa ba.

    Wakiliyar BBC Urdu ta ce jam'iyyu masu adawa da gwamnatin kasar na zargin Mista Khan da rashin iya gudanar da tattalin arzikin kasar da lalata dangantakar kasar da kasashen waje, baya ga cin zarafin masu sukar salon mulkinsa.

    Babu firaministan da ya taba kammala wa'adin mulkinsa a Pakistan, kuma a gobe Alhamis majalisar kasar za ta fara muhawara kan tsige firaministan daga mukaminsa.

  13. Rwanda ta karbi 'yan ci-rani 120 da ke Libya

    'Yan ci-ranin da suka hada da maza da mata da kananan yara

    Asalin hoton, UNHCR/Mohame Alalem

    An kwashe 'yan ci-rani kusan 12 daga Libya da ke neman mafaka zuwa Rwanda a karon farko a irin wannan mataki a jiragen sama.

    'Yan ci-ranin da suka hada da maza da mata da kananan yara - mafi kankanta daga cikinsu shi ne dan shekara daya - sun fito ne daga Eritrea, Sudan, Sudan ta Kudu da Somalia.

    Yawancinsu suna zaune ne a yankunan da ke kusa da Tripoli, babban birnin Libya sannan kuma an tsare wasu daga cikinsu tsawon watanni.

    An kwashi 'yan ci-ranin ne ranar Talata da daddare kuma za su hadu da 'yan gudun hijira 269 da masu neman mafaka a Gashora, inda hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya take bayar da taimakon da ya hada da wurin zama da abinci da magunguna.

  14. Rasha ta kara kaimi wurin kai hare-hare a gabashin Ukraine

    Luhansk regional military leader Serhiy Haidai says a kindergarten was hit in Lysychansk

    Asalin hoton, Serhiy Haidai/Luhansk OVA

    A 'yan kwanakin da suka gabata, Rasha ta jaddada cewa za ta mayar da hankali wurin kai hare-hare a gabashin Ukraine, kuma hukumomi leken asirin Birtaniya sun ce mai yiwuwa hakan "wata hanya ce ta amince cewa" tana shan wahala wajen kai hare-hare a arewacin kasar.

    Kwace garuruwa da filayen da ke kudancin yankin shi ne babban burnin Shugaba Putin, da kuma bukatarsa ta "ceto" yankin gabashi. Tuni 'yan tawayen da Rasha take mara wa baya suka kwace fiye da kashi biyu cikin uku na yankuna biyu na gabashin kasar a 2014.

    Dakarun Rasha sun ci gaba da mamayar arewa maso gabashin yankin Luhansk, sai dai ba su da iko sosai kan Donetsk kuma jami'an tsaron hadin gwiwa na Ukraine da ke gabashi sun musanta cewa an kwace yankin.

    Sai dai Rasha ta kara kaimi wajen kai hare-hare a garuruwan da ke yammaci.

  15. Buhari da ministocinsa sun yi tsit na minti daya don juyayin harin jirgin kasan Abuja

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, da sauran ministocinsa sun yi tsit na minti daya domin nuna juyayi kan harin da 'yan bindiga suka kai a jirgin kasa da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna ranar Litinin da daddare.

    Sun yi tsit din ne yayin zaman Majalisar Ministoci a Fadar shugaban kasar da ke Abuja, babban binrin kasar.

    Sun yi addu'ar Allah ya jikan wadanda suka mutu.

    Harin dai ya yi sanadin mutuwar akalla mutum takwas yayin da fiye da mutum 20 suka jikkata kuma suke jinya a wasu asibitoci da ke Kaduna.

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi tir da kai harin kana ya bukaci jami'an tsaro su karfafa ayyukansu na kare rayukan 'yan kasar.

  16. Labarai da dumi-dumi, Babu ci gaba a tattaunawar zaman lafiya da Ukraine - Rasha

    Kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov ya yi wa 'yan jarida bayani kan tattaunawar da suke yi da Ukraine a Turkiyya jiya, kuma ya ce babu wani fatan samun ci gaba.

    Jiya ne Rasha ta ce tana da niyyar rage kai hare-haren soji a Kyiv da Chernihiv, kuma Ukraine ta ce za ta duba yiwuwar zama kasar " 'yar ba-ruwanmu".

    "Abu mafi muhimmanci shi ne yanzu Ukraine ta soma tsarawa da kuma rubuta bukatun da za ta gabatar. Kafin yanzu, ba a samu irin wannan ci gaban ba," in ji Peskov.

    "A game da sauran bayanai, a wanna halin da ake ciki ba za mu ce ana samun ci gaba ba, babu wata mafita," a cewarsa, a wani labari da kamfanin dillacin labaran kasar Interfax ya fitar.

  17. Bafalasdine ya harbe mutum biyar a Isra'ila

    Wani ma'aikacin agaji ya ce 'yan-sanda sun harbe maharin.

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wani ma'aikacin agaji ya ce 'yan-sanda sun harbe maharin.

    Wani Bafalasdine dan bindiga ya harbe mutum biyar a wajen birnin Tel Aviv na Isra'ila, a hari na uku irin sa mafi muni da aka kai a kasar a mako daya.

    Lamarin ya faru ne a Bnei Brak, daya daga cikin yankunan da Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi suka fi yawa.

    Wani ma'aikacin agaji ya ce 'yan-sanda sun harbe maharin.

    An tsaurara tsaro a yankunan Isra'ila bayan kai hare-hare a ranakun Lahadi da Talata na makon jiya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutum shida.

    Hotunan bidiyon da aka fitar bayan harin Bnei Brak sun nuna mutumin sanye da bakaken kaya rike da bindiga a kan titi kuma ya kashe direban wata mota da ke wucewa a lokacin.

    Firaministan Isra'ila Naftali Bennett ya gudanar da taron gaggawa na tsaro da jami'an tsaron kasar kuma jami'an za su sake ganawa a yau Laraba.

  18. Labarai da dumi-dumi, Mutum miliyan hudu sun tsere daga yakin Ukraine - Majalisar Dinkin Duniya

    'Yan kasar Ukraine fiye da miliyan 2.3 a halin yanzu suke Poland

    Asalin hoton, Reuters

    Sabbin bayanan da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar sun nuna cewa fiye da mutum miliyan hudu ne suka tsere daga Ukraine domin guge wa yakin kasar kawo yanzu.

    Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce 'yan kasar Ukraine 4,019,287 ne suka tsallaka iyaka tun ranar 24 ga watan Fabrairu lokacin da aka soma yakin.

    'Yan kasar Ukraine fiye da miliyan 2.3 a halin yanzu suke Poland.

  19. Da gaske 'yan bindiga sun sake kai hari a jirgin kasa a Kaduna?

    Jirgin kasa

    Wasu rahotanni da ke yawo a shafukan sada zumunta da kuma wasu jaridu a Najeriya na cewa 'yan bindiga sun sake kai hari a jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja.

    Jaridun Najeriya irin su Guardian sun rawaito cewa a karo na biyu cikin awa 24 'yan bindiga sun dasa abubuwan fashewa a layukan-dogo lamarin da ya tilasta wa wani jirgin kasa da ya tashi daga Kaduna zuwa Abuja tsayawa ranar Talata.

    Sai dai binciken da BBC Hausa ta gudanar ya nuna cewa ba a kai wani sabon hari kan jirgin kasa a kan hanyar ta Kaduna zuwa Abuja ba.

    Bayanan da muka samu daga wasu ma'aikatan tashar jingin kasa da ke Kaduna da kuma wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa jiragen ba su yi aiki ba ranar Talata.

    Hasalima babu wani jirgin fasinja da ya tashi daga Kaduna zuwa Abuja - illa dai jirgin kasa da Ministan Sufuri ya hau daga Abuja zuwa wurin da aka kai harin ranar Litinin.

    Sai dai hukumomi ba su ce komai a kan rahotannin kai hari a kan jirgin kasan a karo na biyu cikin awa 24 ba.

    Dama dai hukumar lura da jiragen kasa ta Najeriya ta fitar da sanarwa cewa ta dakatar da jigilar jiragen kasa daga Abuja zuwa Kaduna saboda harin da 'yan bindiga suka kai kan wani jirgin kasa ranar Litinin da daddare.

    Harin dai ya yi sanadin mutuwar akalla mutum takwas yayin da fiye da mutum 20 suka jikkata kuma suke jinya a wasu asibitoci da ke Kaduna.

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi tir da kai harin kana ya bukaci jami'an tsaro su karfafa ayyukansu na kare rayukan 'yan kasar.

  20. Shugaban Sudan ya kori shugabannin jami'o'in kasar

    Janar Abdel Fattah al-Burhan ya dauki matakin ne bayan ya yi amfani da wata dokar soja inda ya ruguza kwamitin amintattu na jami'o'in.

    Asalin hoton, EPA

    Jagoran sojojin Sudan Abdel Fattah al-Burhan ya nada sabbin shugabannin jami'o'in kasar 30.

    Ya dauki matakin ne bayan ya yi amfani da wata dokar soja inda ya ruguza kwamitin amintattu na jami'o'in.

    Tun watan Oktoban 2021 yake amfani da dokar soja bayan sun kawar da gwamnatin rikon-kwarya da Firaminista Abdallah Hamdok yake jagoranta.

    Farfesoshi a Jami'ar Sudan University sun ce za su soma yajin aiki domin birjirewa wannan mataki, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

    Kamfanin ya ambato shugaban jami'ar Khartoum yana bayyana matakin Janar Burhan a matsayin wanda bai halasta ba.

    Jami'o'i da makarantu na cikin 'yan gaba-gaba a zanga-zangar da ake yi domin kyamar mulkin sojin Sudan.