Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

'Yan Najeriya su bar Buhari ya yi ta mulki har abada - Sule Lamido

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Aisha Shariff Bappa and Awwal Ahmad Janyau

  1. Kamfanin jirgin saman Azman ya dakatar da zirga-zirga a Kaduna

    Kamfanin jrgin saman Azman ya dakatar da zirga-zirga a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya kwanaki kadan bayan harin da wasu 'yan bindiga suka kai filin jirgin saman jihar inda suka kashe masu gadi da wasu ma'aikata

    Kamfanin ya wallafa a shafinsa na Tuwita cewa zai dakatar da zirga-zirga a Kaduna daga ranar Litinin din da ta wuce.

    Kamfanin ya ce ya dauki matakin saboda yanayi na tsaro a filin jirgin saman.

    Matakin kamfanin dai ya sa matafiya sun yi cirko-cirko a filin jirgin saman na Kaduna saboda karancin jiragen da za su kai su inda za su je.

    Hukumar gudanarwar kamfanin ta sanar da cewa za a dakatar da zirga-zirgar ce zuwa wani lokaci ma'ana kafin yanayin tsaro ya inganta a filin jirgin saman na Kaduna.

  2. Ya kamata tattaunawar da za a yi ta kasance mai amfani - Erdogan

    Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce dukkan shugabannin Ukraine Zelensky da na Rasha Putin "abokai ne masu muhimmanci", a yayin da yake share fagen tattaunawa da su a Istanbul a safiyar nan.

    Ya ce samun ci gaba a tattaunawar zai share hanyar ganawar shugabannin - kuma Turkiyya za ta iya karbar bakuncinsu.

    Ya kuma shaida wa tawagar Rasha da ta Ukraine cewa dukkan bangarorin suna da "damuwa ta hakika amma mun kai wata gaba da ya kamata tataunawar da za a yi ta kasance mai amfani na hakika".

  3. Barkanmu da hantsi

    Aisha Shariff Bappa ce take muku mabara da kasance da mu a wannan shafin da muke kawo maku labarai da rahotanni kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Za mu mayar da hankali kan abubuwan da ke faruwa a Rasha da Ukraine, da kuma Najeriya da makwabtanta.