Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan Najeriya su bar Buhari ya yi ta mulki har abada - Sule Lamido
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.
Rahoto kai-tsaye
Aisha Shariff Bappa and Awwal Ahmad Janyau
'Yan Najeriya su bar Buhari ya yi ta mulki har abada - Sule Lamido
Tsohon gwamnan Jihar Jigawa a arewa maso yammacin Najeriya Alhaji Sule Lamido ya ce "ƴan Najeriya idan sun ga dama su bar Buhari ya tabbata a mulki har a bada."
Ya fadi hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da BBC Hausa a kwanakin baya.
Tsohon gwamnan ya kuma ce "jam'iyyar APC annoba ce a Najeriya, ta kawo masifa marar iyaka, gyaran barnar APC nan gaba aiki ne babba, tun da yake ta kawo gaba tsakanin ɗa da uwa, da tsakanin wa da ƙani da tsakanin gari da gari, dangi da dangi, addini da addini da kudu da arewa."
"Amma duk inda ake son mu bayar da gudunmowa za mu bayar wallahi," a cewarsa.
BBC Hausa ta tuntuɓi mai magana da yawun fadar shugaban Najeriya Garba Shehu don jin ko za su mayar da martani, amma ya ce yanzu ba ta tasa suke ba, sai daga baya za su yi martani.
Sule Lamido ya ce saboda kaunar Buhari da ƴan Najeriya suka so ya yi mulki "an ce mana arne, an ce mana kirista, an ce ba ma son Musulunci, ba ma son arewa, komai an yi, an ma ce mu da ƴaƴanmu ɓarayi ne.
"An ce Buhari waliyyi ne, ma'asumi ne, kaza-kaza duk an yi, an ɓata mu."
Ya ce "idan dai har yanzu ƴan Najeriya ba su dawo rakiyar APC ba to sai su tabbatar da Buhari ya yi ta mulki har abada."
"Tun da suna ganin ya kyauta, to duk mu taru mu ce Buhari don Allah ya ci gaba da mulki har abada."
Jigon na babbar jam'iyyar adawar ƙasar ta PDP dai ya yi zargin cewa APC mai mulki ta rusa dukkan ginshiƙan da aka gina ƙasar a kai don tabbatar da haɓakarta.
A cewarsa, hakan ta sa PDP ta duƙufa don ganin ta karɓe mulki da kuma sake lale da nufin ceto Najeriya.
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido na cikin mutanen farko da aka kafa PDP da su tun 1998, kuma a tattaunawarsu da Ibrahim Isa ya ce PDP ce kaɗai za ta fitar da Najeriya daga ƙangin da take ciki.
Ga dai cikakkiyar hirar a ƙasa sai ku latsa ku saurara.
Senegal ta samu gurbin gasar cin kofin duniya bayan ta doke Egypt
Senegal ta samu gurbin zuwa gasar cin kofin duniya bayan ta doke Egypt a bugun fanariti.
Senegal ta doke Egypt ne 3-1 a fanariti bayan sun tashi wasan jimilla 1-1.
Senegal ta rama ƙwallon da Egypt ta ci ta a wasan farko, makon da ya gabata.
Sadio Mane ne ya ci wa Senegal ƙwallo ta uku a bugun fanariti bayan ƴan wasan ƙasar biyu sun ɓarar da ƙwallo biyu.
Mohamed Salah na cikin ƴan wasan da suka ɓarar wa Egypt da fanariti.
Labarai da dumi-dumi, Ghana ta haramta wa Najeriya zuwa gasar cin kofin duniya a Qatar
Najeriya ba za tatafi gasar cin kofin duniya ba bayan Ghana ta riƙe ta 1-1 a Abuja.
Sakamakon na nufin Ghana na cikin sahun kasashen da za su wakilci nahiyar Afirka a gasar kwallon kafa ta duniya da kasar Qatar za ta dauki nauyinsa daga 21 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan Disambar wannan shekarar.
Ghana ta samu gurbin ne saboda ƙwallon da ta ci Najeriya a Abuja, bayan sun tashi babu ci a Kumasi a Ghana.
Rasha za ta rage yawan dakaru a Ukraine
Rasha ta ce za ta rage yawan dakarunta a kusa da biranen kyiv da Chernihiv a arewacin Ukraine.
Wannan sanarwar ta biyo bayan tattaunawar zaman lafiya da kasashen biyu suka yi a Turkiyya.
Ministan tsaro na Rasha Alexander Fomin ya ce dalilin yin haka shi ne domin Rasha na son samar da yanayin da zai haifar da amincewa tsakaninta da Ukraine.
Jami'an Ukraine sun gabatar da shawarar kasar za ta zama 'yar ba ruwanmu, amma tana so a tabbatar ma ta da za ta zauna cikin aminci da Rasha.
Ministan harkokin wajen Turkiyya ya ce tataunawar ta yau ta fi karfafa wa duka bangarorin biyu gwuiwa
Yadda Osinbajo ya kai ziyara tashar jirgin ƙasa a Kaduna
Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya kai ziyarar jaje tashar jirgin ƙasa a Kaduna.
Ya kuma ziyarci asibitin sojoji ta 44 domin ganin mutanen da suka jikkata a harin da ƴan bindiga suka kai wa jirgin ƙasa da ke kan hanyar zuwa Kaduna daga Abuja a ranar Litinin.
Najeriya ta farke ƙwallon da Ghana ta fara ɗurawa a ragarta a Abuja
Najeriya ta farke ƙwallon da Ghana ta fara ɗurawa a ragarta a Abuja. Idan an tashi 1-1 an fitar da Najeriya
Dan wasan tsakiya ne Thomas Partey ne ya ci Ghana ƙwallo a raga ana minti 10 da wasa.
William Troost-Ekong ya rama ƙwallon a bugun fanariti ana minti 22 da wasa.
Buhari ya tafi kallon ƙwallon Najeriya da Ghana
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tafi kallon ƙwallon kafa da Najeriya za ta fafata da Ghana a Abuja a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya a Qatar.
Titin da ya fito daga fadar shugaban ƙasar har zuwa filin ƙwallon kafa da ke birnin Abuja ya kasance shiru babu ababen hawa saboda wucewar shugaban.
Gwamnati ta samar da tikitin shiga kallon wasan kyauta ga ƴan Najeriya domin nuna goyon baya ga ƴan wasan Najeriya.
Duk ƙasar da aka ci tsakanin Najeriya da Ghana ba za ta tafi gasar cin kofin duniya ba.
Buhari ya yi Allah wadai da harin bom da aka kai wa jirgin ƙasa
Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da harin bam da aka kai wa jirgin kasa da ke ɗauke da fasinja kusan 1000 a hanyar Abuja zuwa Kaduna, yana mai bayyana al’amarin a “matsayin wani abin damuwa matuka.”
A cikin sanarwar da fadar shugaban ta fitar, Buhari ya ce, “kamar sauran ‘yan Najeriya, ina cikin jimami matuƙa da faruwar wannan lamarin, wanda shi ne irinsa na biyu, wanda ya kai ga sanadin mutuwar fasinjojin da har yanzu ba a tantance adadinsu ba da kuma wasu da suka samu raunuka.”
“Harin da aka kai kan jirgin kasa, abin takaici ne; tunani na yana kan iyalan waɗanda suka rasu da kuma addu’a ga wadanda suka jikkata,” in ji Buhari.
Shugaban ya ce ya bayar da umarnin gaggawa na tabbatar da bincike da hanyoyin magance matsalar tsaron titin jigin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna.
Sannan ya umarci jami’an tsaro su kuɓutar da fasinjojin da daka sace tare da farautar ƴan bindigar.
Bayanai sun nuna cewa kimanin mutum 1000 ne a cikin jirgin, wanda aka kai wa hari ranar Litinin da daddare.
Rahotanni sun ce an sace mutane da dama sannan an kashe wasu, abin da ya jijjiga iyalai da 'yan uwan fasinjojin da ke cikin jirgin.
Babban hafsan sojin Najeriya ya kai ziyara inda aka kai wa jirgin ƙasa hari
Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya laftanal Janar Faruk Yahaya ya kai ziyara inda aka kai wa jirgin ƙasa hari a hanyar Abuja Kaduna a ranar Litinin.
Rundunar sojin Najeriya ta wallafa hotunansa a Facebook tare da tawagarsa ta sojoji a wurin da aka kai harin.
Sanarwar ta ce ya tafi ne domin diba yanayin wurin da girman harin.
Ya kuma umarci sojoji da su tsawaita bincike domin kuɓutar da mutanen da aka sace.
Bayanai sun nuna cewa kimanin mutum 1000 ne a cikin jirgin, wanda aka kai wa hari ranar Litinin da daddare.
Rahotanni sun ce an sace mutane da dama sannan an kashe wasu, abin da ya jijjiga iyalai da 'yan uwan fasinjojin da ke cikin jirgin.
Har yanzu ba a shigar da agaji zuwa yankin Tigray ba
'Yan tawaye a yankin Tigray da ke arewacin Habasha, sun ce babu wani tallafin abinci da ya isa yankin duk da yarjejeniyar tsagaita wutar da gwamnati ta sanar a makon da ya wuce na kyale shigar da kayan agaji ga dumbin mutane da ke cikin matsananciyar yunwa.
Sun ce jerin gwanon manyan motoci dauke da abinci da magunguna har yanzy na jira a basu damar wucewa zuwa Tigray wadda tun watan Disambar da ya wuce ba a shigar da komai ba.
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci mahukunta da su dawo da ayyukan jama'a a Tigray, ciki har da bude bankuna da kyale ma'aikatan samar da wutar lantarki da na sadarwa su je aiki.
Kungiyoyin na matukar fuskantar karancin abinci da kudi wajen gudanar da ayyukansu.
Ana dai zargin gwamnatin kasar da toshe duk wasu hanyoyin shigar da agaji zuwa yankin, zargin da suka musanta.
Ana tattauna batun komawar mata makaranta a Afghanistan
A kasar Afghanistan, wasu ministoci mata biyu daga kasashen Musulmai sun gana da wani babban jami'in Taliban domin tattauna batun samar wa mata ilimi a kasar.
Ministar harkokin wajen Indonesiya Rento Masudi da mataimakiyar ministar harkokin waje ta Qatar Lolwah Al Khater, sun gana da mukaddashin ministan harkokin waje na Taliban Amir Khan Muttaqi a Doha babban birnin kasar ta Qatar.
Ministocin biyu sun tattauna kan batutuwan jin-ƙai da ilimi a Afghanistan - kuma sun bukaci kungiyar Taliban ta kyale 'yan mata su koma makaranta.
Jakadan Amurka na musamman a Afghanistan ya ce yana fatan cikin kwanaki masu zuwa Taliban za ta sauya shawararta ta rufe makarantun mata,sannan kuma ta kyale 'yan mata su koma ajujuwansu.
A makon jiya 'yan Taliban suka kulle makarantun sakandare na 'yan mata, sa'o'i kadan bayan da hutun da suka tafi ya kare.
An sako Indiyawan da aka yi garkuwa da su a Habasha
Masu satar mutane a Habasha sun saki 'yan kasar Indian nan da suka sace domin neman kudin fansa.
An tsare Indiyawan ne a wani karamin gari da ke da nisan kilomita 30 daga Addis Ababa, babban birnin kasar.
A farkon watan Maris ne aka sace mutum 27, daga wata mahaka a kamfanin siminti.
Cikin wadanda aka sace har da indiyawa shida.
Daga bisani masu satar mutane sun saki mutum 18, inda suka ci gaba da rike da Indiyawa shida da masu musu tafinta uku.
Masu satar mutanen sun nemi a ba su dala dubu 480 a matsayin kudin fansa.
Wasu jami'ai a yankin Wayessa sun shaida wa BBC cewa an sako mutanen ba tare da wani cikakken bayani ba.
Hanyoyin da za a bi wajen magance matsalolin 'yan ta'adda a yankin Tafkin Chadi
Gwamnan jihar Borno da ke arewacin Najeriya, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya jawabi ga kungiyoyin kasashen waje da ke aiki kasashen yankin tafkin Chadi da abokan hulda daga Birtaniya da kuma sauran kasashe.
Kungiyar kasashen renon Ingila ce ta shirya taron.
Taron ya mayar da hankali ne a kan hanyoyin da ake bi wajen magance rikice-rikicen kasashen yankin Tafkin Chadi da kuma yadda za a mayar da hankali wajen ganin 'yan kungiyar Boko Haram da dama sun mika wuya.
Taron ya samu halartar sojoji da shugabannin kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi da shugabannin siyasa da na jami'oi da kuma kungiyoyin agaji daga Chadi da Najeriya da Nijar da kuma Kamaru.
Za a duba irin hanyoyin da ya kamata abi wajen magance matsalolin 'yan ta'adda da ke addabar yankin.
A jawabinsa, Gwamna Zulum ya bayyana irin yadda ake yakar masu tayar da kayar baya a Borno da kuma yadda aka sake gina jihar.
Gwamna Zulum, ya ya kuma bayyana irin illolin da yakin Boko Haram ya haifar a Borno musamman wajen lalata gine-gine da tursasawa mutane barin muhallansu da kuma irin matsalolin ayyukan jinkai da ake fuskanta a jihar.
An rusa wani gini mai muhimmanci a birnin Mykolaiv
Gwamnan birnin Mykolaiv, Vitaliy Kim, ya wallafa wasu hotuna a shafinsa na sada zumunta wanda ke nuna yadda aka ragargaza wani babban ginin gudanarwa na gwamnati a birnin.
Mahukunta a birnin sun ce an zakulo mutum 17 daga baraguzan ginin, amma kuma har yanzu akwai wasu da ba a gani ba.
Gwamnan ya ce ana ci gaba da aikin neman mutanen da ba a gani ba.
Hare-haren Rasha ne suka fada a kan ginin, inda aka lalata fiye da rabin ginin.
Gwamnan ya ce, "Da mu da wadanda harin ya rutsa da su duk muna hannun Allah, sannan da yawa daga cikin wadanda harin ya rutsa da su sun kubuta ban san ta yaya suka kubuta ba .A yanzu akwai sauran fararen hula takwas da muke fatan zakulo su daga baraguzan gini".
El-Rufai ya kai ziyara asibitin da aka kai wadanda harin jirgin kasa ya rutsa da su
Wakilin BBC da ya je asibitin ya ce ya ga gawar mutum 7, yayin da wasu 22 kuma ke kwance a bangaren kulawar gaggawa na asibitin sojoji na 44.
Tsohon mataimakin gwamnan Zamfara, Ibrahim Wakkala, na daga cikin wadanda aka harba, inda za a yi masa tiyata a kafar da aka harbe shi.
Ga wasu daga cikin hotunan ziyarar da gwamnan na Kaduna ya kai asibitin.
Labarai da dumi-dumi, Labarin sanya wa Abramovich guba wani makamin yaki ne - Kremlin
Fadar gwamnatin Rasha Kremlin ta ce labarin da ake ta yadawa cewa an sanya wa attajirin nan dan kasar Roman Abramovich guba a wurin taron neman zaman lafiya a farkon watan nan ba shi da kamshin gaskiya.
Kremlin ta ce labarin "wani makami ne na yaki".
Fadar gwamnatin Rasha ta ce Abramovich bai halarci taron tattaunwar da aka yi a Turkiyya a matsayin wakilinta - ko da yake an dauke shi a hoto tare da jami'an Ukraine.
'Kada wanda ya ci abinci ko ya sha wani abu a wajen taron tattaunawa'
Ministan harkokin wajen Ukraine, Dmytro Kuleba, ya bai wa mahalarta taron tattaunawar da ake yi da Rasha shawara cewa kada wanda ya ci ko ya sha wani abu a wajen.
Ministan ya ba da shawarar ce gabanin fara taron da za a yi a Turkiyya.
Kafar yada labaran Ukraine ce ta bayyana hakan inda ta ce ministan ya bada shawararce bayan zargin da aka yi cewa an bai wa shahararren attajirin nan Roman Abramovich guba a farkon tattaunawar zaman lafiyar da aka yi a farkon watan nan.
Akwai shakku a kan zargin da ake a kan zargin bai wa Mr Abramovich guba, inda wani jami'a a Amurka da ba a bayyana sunansa ba ya shaida wa kamfanin dillancin na Reuters cewa ba mamaki canjin yanayi ne ya shafi Mr Abramovich.
A ci gaba da tattaunawar ta yau a kan rikicin Rasha da Ukraine, Abramovich ya isa wajen a cewar kafar yadda labaran Turkiyya.
Afirka ta Kudu ta haramta sanya hoton mata a tallan barasa
Hukumar da ke sa ido kan tallace- tallace a Afirka ta Kudu ta haramta tallan wata giya mai hoton mata tana mai cewa hakan bai dace ba kuma yana jawo dabi'ar fyade.
Hukumar ta ce irin yadda ake tallan ana nuna mace ta bude baki da shan giya ya saba wa dokokinta.
Kamfanin da ke samar da giyar a kasar ne ya sanya hoton wata mata ta bude baki tana kwankwadar giya a jikin wata mota.
Hukumar ta ce ba wai shan giyar ta hana ba, a'a yadda ake amfani da hotunan mata ne bai dace ba.
Ta ce dole a rinka mutunta mata, irin wadannan tallace- tallacen bai kamata ana sa mata ba.
Za a kwashe fararen hula daga Mariupol
Ana sa ran Ukraine za ta kwashe fararen-hular da suka makale a wasu garuruwa da biranen da aka yi wa kawanya saboda yakin da ake yi a kasar.
Mataimakiyar firaministan kasar, Iryna Vereshchuk ce ta sanar da hakan.
Ta ce za a yi kokarin samar da hanyar da mutanen za su fice ba tare da an taba kowa ba a birnin Mariupol inda mutum dubu 160 suka makale.
Iryna Vereshchuk ta ce za a yi amfani motoci wajen kwashe mutanen.
A jiya dai Ukraine ta yi gargadin cewa wasu daga cikin hanyoyin da za a bi wajen ficewa da mutanen da suka makale daga kasar ba su da tabbas saboda irin hare-haren da dakarun Rasha ke kai wa.