Taliban ta haramta wa ma’aikatan da ba su da gemu shiga ofis

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Aisha Shariff Bappa and Awwal Ahmad Janyau

  1. Saudiyya za ta samar da abincin buɗa baki ga Musulmi a ƙasashe 34

    Yarima mai jiran gado

    Asalin hoton, Getty Images

    Saudiyya za ta ƙaddamar da shirin buɗa baki a ƙasashe 34, kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ruwaito a ranar Lahadi.

    Manufar shirin shi ne samar da abincin buɗa baki ga Musulmi a cikin watan Ramadan, wanda ake fatan soma wa a ranar 2 ga watan Afrilu.

    Ana sa ran mutum miliyan 1.2 za su ci gajiyar shirin.

    Rahotannin sun ce Ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci, ta yi dukkanin shirye-shiryen da suka wajaba domin ganin shirin ya shafi ɓangarorin duniya, ko da yake ya dogara daga neman bukatar.

    Za a aiwatar da shirin ne tare da hadin gwiwar ofisoshin jakadancin Saudiyya da cibiyoyin addinin Musulunci na ma'aikatar.

  2. Gaskiyar bidiyon da aka yaɗa na harin ƴan bindiga a filin jirgin saman Kaduna

    Kaduna

    Asalin hoton, Getty Images

    Sashen binciken ƙwaf na BBC ya bi diddigin bidiyon da aka yi ta yaɗawa na harin ƴan bindiga a filin jirgin saman Kaduna.

    Ya gano cewa tun shekarar 2018 aka yaɗa shi a Tuwita.

  3. Za a rufe ofisohin gwamnati ƙarfe 1 a Najeriya saboda wasan Super Eagles da Ghana

    Rahotanni sun ce gwamnatin Najeriya ta umarci ma’aikata su tashi aiki ƙarfe 1 na rana a ranar Talata saboda wasan ƙwallon ƙafa da Najeriya za ta yi da Ghana a Abuja.

    Wata sanarwa daga Ofishin shugaban ma’aikata na Najeriya da ke yawo ta ce akwai buƙatar nuna goyon baya ga ƴan wasan Super Eagles.

    A ranar Talata ƴan wasan Super Eagles za su fafata da tawagar Black Stars na Ghana a wasan neman gurbin gasar cin kofin duniya a Qatar. Wasan na da muhimmanci ga Najeriya bayan ta kasa cin Ghana a Kumasi a wasan farko da suka fafata da aka tashi babu ci.

    s

    Asalin hoton, Others

    Tuni aka bayyana cewa an ware tikitin wasan 20,000 kyauta ga masu sha'awar shiga kallon wasan a Abuja.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  4. Mutum 5,000 aka kashe a Mariupol

    Magajin Garin Mariupol na kudu maso gabashin Ukraine ya ce mutum 5,000 suka halaka tun bayan da Rasha ta fara yi ma birnin kofar rago kusan wata guda da ya gabata.

    Ya kuma ce an lalata kashi casa'in na gine-ginen birnin, kuma kashi 40 na gine-ginen birnin sun ruguje baki daya.

    Akwai kimanin fararen hula 160,000 da rikicin ya rutsa da su a birnin, wanda sojojin Rasha suke wa luguden wuta babu kakkautawa.

    Sojojin Ukraine da ke kare birnin sun ki mika wuya, kuma faduwar birnin zai karfafa ikon da Rasha ke da shi a yankin Donbas da yankin Crimea.

  5. Taliban ta haramta wa ma’aikatan da ba su da gemu shiga ofis

    Taliban

    Jami'an ma'aikatar kula da al'umma a Afghanistan na gudanar da bincike a gaban ofisoshin gwamnati domin duba ko tsawon gemun ma'aikata ya kai wanda hukuma ta umarta, kuma suna sanya kayayyaki kamar yadda Musulunci ya buƙata.

    Ma'aikatar yaɗa Kyawawan Halaye da Hana Aikata Laifuka ta gargaɗi ma'aikatan gwamnati cewa za su iya rasa ayyukansu idan ba su mayar da hankali kan wadannan dokokin ba.

    Wannan na cikin sabbin dokokin da ƴan Taliban suka kafa a ƴan makonnin nan.

    An kulle makarantun sakandare na mata cikin sa'o'i bayan da daliban suka koma hutu a makon jiya.

    An kuma hana mata yin tafiye-tafiye a jiragen sama na cikin gida ko masu zuwa kasashen waje ba tare da muharrami ba tare da hana cuɗanyar mata da maza a wuraren shaƙatawa

  6. An sauya rigar Ka’aba saboda Ramadan

    @theholymosques

    Asalin hoton, @theholymosques

    Kamar yadda aka saba an sauya rigar Ka’aba domin shirin azumin watabn Ramadan.

    Za a samu ƙaruwar masu ibada a Masallacin Ka’aba a Makka, bayan ɗage dokokin korona a Saudiyya.

    @theholymosques

    Asalin hoton, @theholymosques

  7. Attajirin Rasha Roman Abramovich na fama da rashin lafiya mai alaƙa da guba

    Roman Abramovich

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni sun ce attajirin kasar Rasha Roman Abramovich na sha fama da rashin lafiya da ake zargin guba ce.

    Roman Abramovich mai shiga tsakanin rikicin Ukraine ya nuna alamu na cutar guba bayan ganawar tattaunawar zaman lafiya a farkon wannan watan, kamar yadda rahotanni suka bayyana

    Abramovich tare da wani dan kasuwa na Rasha, sun shiga tattaunawar tare da dan majalisar a yankin Crimean Rustem Umerov.

    Mutum uku da suka halarci tattaunawar a Kyiv daga ranar 3 zuwa 4 ga Maris sun nuna alamun rashin lafiyar daga makami mai guba, kamar yadda aka ruwaito.

    An ruwaito cewa idanunsu sun ja kuma suna kwalla da saba a fata da hannu, amma sun ce suna samun sauki kuma rayuwarsu ba ta cikin hatsari.

    Sai dai Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, wanda ya gana da Abramovich bai kamu ba.

  8. Mutane na tserewa muhallansu saboda harin 'yan tawaye a Congo

    Jami'ai daga lardin Kivu dake arewacin kasar sun ce mayakan kungiyar M23, sun afakwa kauyukan Tchanzu da Runyoni.
    Bayanan hoto, Jami'ai daga lardin Kivu dake arewacin kasar sun ce mayakan kungiyar M23, sun afakwa kauyukan Tchanzu da Runyoni.

    Daruruwan al'ummar Jamhuriyar Dimkradiyyar Congo ne suka tsere zuwa Uganda bayan hare haren da 'yan tawaye suka kai kan gidajensu.

    Jami'ai daga lardin Kivu dake arewacin kasar sun ce mayakan kungiyar M23, sun afakwa kauyukan Tchanzu da Runyoni.

    Rahotanni sun ce an kai hari kan wani sansanin soji da ke kasar ma.

    Kungiyar 'yan tawayen M23, wadda ta hada da kabilun 'yan Tutsis, na fada a gabashin Congo inda ta kwace babban birnin yankin Goma a shekarar 2012.

    Daga bisani an zauna tare da mamabobin kungiyar da na gwamnati don tattaunawa to amma kungiyar ta ce ba a cika mata bukatunta ba.

    A baya dai Majalisar Dinkin Duniya ta zargi Uganda Rwanda da goyon bayan 'yan tawyen M23.

  9. Rasha ta ƙwace agogunan ƙasaita na miliyoyin daloli a wasu shaguna

    An kwace agogunan kasaita a Rasha

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, An kwace agogunan kasaita a Rasha

    Jami'ai a Rasha sun rawaito cewa an ƙwace agogunan ƙasaita da kudinsu ya kai na miliyoyin daloli.

    Kafar yada labaran kasar ta ce jami'an tsaro ne suka je shagon da aka ajiye agogunan a ranar Talata inda suka zargi cewa an saɓa wa dokokin shige da ficen kaya.

    Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan Switzerland ta yi watsi da kiraye-kirayen kasashen yamma na bin sahunsu domin a ƙaƙaba wa Rasha takunkumi saboda mamayar da take yi wa Ukraine.

    Agogunan da aka ƙwace na da matuƙar tsada, a inda ake sayar da duk guda ɗaya a kan dala dubu 920.

  10. Kotu ta yi watsi da bukatar bayar da belin Abba Kyari

    Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ki amincewa da bukatar belin  Abba Kyari
    Bayanan hoto, Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ki amincewa da bukatar belin Abba Kyari

    Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ƙi amincewa da buƙatar bayar da beli da dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari yake nema.

    Mai shari’a Emeka Nwite ne ya ƙi amincewa da bukatar ba da belin yayin yanke hukunci kan bukatar a yau Litinin.

    An gurfanar da Abba Kyari da wasu mutum shida a gaban kotu bisa zargin safarar hodar iblis.

    Mai shari’an, Emeka Nwite ya bayyana cewa hujjoji da hukumar Hana sha da fatucin miyagun kwayoyi NDLEA ta gabatar mata sun kai ta ki bada belin Abba Kyarin da wasu mutum shida.

    Hukumar ta NDLEA da take kawo hujjojin neman yin fatali da bukatar neman beli da Abba kyari ya yi, ta ce ta yi la’akari da ƙwaƙƙwarar shaida da yanayin da ke tattare da zargin da ake masa, bai kamata kotun ta bayar da belinsa ba.

    NDLEA ta fada wa kotun kuma cewa yanayin lafiyar Abba Kyari abu ne wanda za ta iya kula da shi da kuma bai fi karfinta ba, wanda kuma hakan yasa kotun taki amincewa da bukatar beli da Abba Kyari yake nema a gabanta.

    Idan za a iya tunawa dai, Ana zargin Abba Kyari da wasu ‘yan sanda shida da hannu a safarar hodar iblis.

    Ana kuma zargin Kyari da karɓar cin hanci a hannun matashi ɗan Najeriya kuma mazaunin Amurka mai suna Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppy, Sai dai ya musanta zarge-zargen.

  11. Yakin da Rasha ke yi ya ja wa Ukraine asarar dala biliyan 564

    Yakin Rasha a Ukraine ya lalata gine gine masu muhimmanci da kuma durkushewar ci gaban tattalin arzikinta.

    Asalin hoton, DSNS.GOV.UA

    Bayanan hoto, Yakin Rasha a Ukraine ya lalata gine gine masu muhimmanci da kuma durkushewar ci gaban tattalin arzikinta.

    Yakin Rasha a Ukraine ya ja wa Ukraine asarar fiye da dala biliyan 564 ya yanzu.

    Yakin ya lalata mata gine-gine masu muhimmanci da kuma durkushewar ci gaban tattalin arzikinta.

    Rasha na ci gaba da cewa tana gudanar da wani babban farmaki a Ukraine da nufin durkusar da sojojinta.

    Ukraine da kawayenta sun ce wadannan kalamai na Rasha wani uzuri ne na mamayar da take yi babu gaira ba dalili.

  12. Kamfanin giya na Heneiken ya janye daga Rasha saboda mamayar da ta yi wa Ukraine

    Kamfanin barasa na Heneiken ya ce ya kammala dukkan shirye shirye na daina duk wata huldar kasuwanci a Rasha.

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Kamfanin barasa na Heneiken ya ce ya kammala dukkan shirye shirye na daina duk wata huldar kasuwanci a Rasha.

    Kamfanin da ke samar da barasa na Heneiken ya ce ya fice daga Rasha.

    Kamfanin ya kasance na baya baya bayan nan daga cikin jerin kamfanonin kasashen Yamma da suka dauki irin wannan mataki sakamakon mamayar da Rashan ke yi a Ukraine.

    A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar, ya ce ya kammala dukkan shirye-shiryensa na daina duk wata huldar kasuwanci a Rasha.

    Tuni dama kamfanin da dakatar da sayar irin kayayyakinsa dama samar da su a Rasha, sannan ya kuma soke duk wani batu na zuba jari a kasar tun farkon watan da muke ciki.

    Akwai kamfanoni da dama da suka janye daga Rasha kamar Ikea da Coca-Cola da kuma MacDonalds.

  13. Yaduwar korona ta sa an sake kulle birnin Shanghai na kasar China

    Jami'an lafiya
    Bayanan hoto, Jami'an lafiya

    Dokar yaki da cutar korona a babban birni mafi hada-hadar kasuwanci a duniya wato Shanghai da ke China.

    An sanar cewa rabin mazauna birnin da ke yammaci su zauna a gida tsawon kwanaki biyar, yayin da za a ci gaba da gwaji.

    Rahotanni sun ce a yanzu an raba birnin mai mutane miliyan 25 kashi biyu, sannan an fara gwajin gama- gari.

    Kantunan sayar da kaytan masarufi ne kadai aka amince su bude, sannan ma'aikatan lafiya ne kadai aka maince su fita sai kuma wadanda fita ta kama su dole.

  14. Babu wani tsari na kwashe fararen-hula daga Ukraine a yau

    Al'ummar Ukraine

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Al'ummar Ukraine

    Mataimakiyar firaiministan Ukraine ta ce babu wani shiri na bude kafofin ficewa daga kasar domin kwashe fararen-hular da suka makale a biranen kasar a yau.

    Iryna Vereshchuk ta ce an dauki matakin ne saboda bayanan sirrin da aka samu cewa akwai yiwuwar Rasha za ta iya tare hanyoyin.

    Ta ce san samar da kafofin ficewa marasa hadari a Mariupol da Sumy kuma garuruwa da kauyukan wajen Kyiv wanda a yanzu dakarun Rasha suka kusan kewaye shi.

    Lugudan wutar da Rasha ta yi a baya sun hana kwashe fararen-hula daga biranen da aka yi wa kawanya.

  15. Ana zanga-zangar bukatar dawo da fuskar katako mai tarihi daga Faransa a Gabon

    Fuskar Katako

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, 'Yan kungiyar sirri ta Ngil ne ke amfani da fuskar katakon domin zuwa kauyuka suna tabbatar da gaskiya da adalci ga wadanda aka zalunta

    Masu fafutuka na bukatar a dawo wa Gabon wata sassaka ta fuskar katako ta karni na 19 da aka sayar a Faransa a kan kusan dala miliyan 5.

    Babu wanda ya tsammaci za a sayar da fuskar katakon a kan wannan kudi.

    Masu fafutukar sun tarwatsa wani bikin baje-koli da aka yi a birnin Montpellier da ke kudancin Faransa, suna masu cewa duk wanda ya sayi fuskar katakon to ya sayi kayan sata.

    Mai daukar naiyun baje-kolin ya ce suna yin sa ne bisa ka'ida.

    'Yan kungiyar sirri ta Ngil ne ke amfani da fuskar katakon domin zuwa kauyuka suna tabbatar da gaskiya da adalci ga wadanda aka zalunta da kuma bankado mayu.

    Kamar sauran kasashe, Gabon ma yanzu na bukatar ire-iren kayayyakinta na tarihi da aka sace a lokacin mulkin turawa.

  16. An janye dokar sanya takunkumi a Ghana

    Shugaban ya kuma cire bukatar gabatar da katin shaidar allurar rigakafin korona ga matafiyan da suka isa kasar a filin jirgin saman kasar

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Al'ummar Ghana

    Gwamnatin kasar Ghana ta janye dokar sanya takunkumi a fadin kasar.

    Shugaban kasar, Nana Akufo-Addo, ya sanar da matakin a jiya Lahadi, yana mai bayar da misalin cewa a yanzu an samu raguwa sosai na masu kamuwa da cutar korona.

    Kazalika shugaban ya kuma cire bukatar gabatar da katin shaidar allurar rigakafin korona ga matafiyan da suka isa kasar a filin jirgin saman kasar da ke Accra.

    Daga nan ya bukaci al'ummar kasar da su ci gaba da kula da tsabtar kansu da ma muhallansu da kuma kaucewa shiga taron jama'a.

    Adadin masu kamuwa da cutar ya fara raguwa sosai tun daga karshen shekarar data wuce.

    Ya zuwa yanzu an samu mutum kusan dubu dari da sittin da daya da suka taba kamuwa da korona a kasar.

    Ghana dai ta shiga cikin jerin kasashen Afirka da suka sassauta dokokin korona duk da gargadin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi cewa dage dokokin ya yi kusa.

  17. Jami'an agaji sun kasa kai wa ga mutanen da suka makale a Mariupol

    Birnin Mariupol

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Birnin Mariupol

    Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce har yanzu ta kasa shigar da kayan agaji zuwa yankin da aka yi wa kawanya na Mariupol, abin da ya sa ta bukaci bangarori biyun da ke fada - Ukraine da Rasha - da su ba da tabbacin bayar da damar shiga birnin.

    Mai magana da yawun kungiyar, Matt Morris ya shaida wa BBC cewa dole a cimma yarjejeniya da bangarorin biyu domin ba da damar kai wa ga dubban mutane da suka makale a birnin da ke tsananin bukatar agaji.

    Ya ce hukumar da ke kula da ayyukan jinkai ta duniya na bukatar a bar mutane su bar birnin, kada a turasasa musu.

    Ya ce yawancin wadanda ke birnin na zama ne a wuraren fakewa sannan suna fuskantar karantar abinci da ruwan sha dama magunguna.

    Ukraine dai na zargin Rasha da tursasa wa dubban fararen-hula komawa wuraren da take iko da su abin da Rasha ta musanta.

  18. An yanke wa tsohon mai ba da shawara hukuncin zaman kurkuku saboda sace kudaden aikin Hajji

    Usman Baba

    Asalin hoton, Nigeria Police Force

    An yanke wa wani tsohon mai ba da shawara ga shugaban karamar Hukumar Giwa a jihar Kaduna ta Najeriya hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara 12.

    An samu Hassan Dauda da laifin sace kudin aikin Hajji na wasu mutane da ya suka kai naira miliyan shida da dubu dari uku da arba'in da biyu.

    Babbar kotun jihar ce ta yake masa hukuncin bayan an zarge shi da cinye kudin aikin Hajjin wasu mutum 8.

    An dai zarge shi da amfani da matsayinsa na mai bada shawara na musamman ga shugaban karamar hukuma wajen karbar kudin aikin Hajjin mutanen tare da yi musu alwakrn sama musu kujera aikin Hajji a shekarar 2013.

    Alkalin kotun, Justice M.T Aliyu, ya same shi da laifin yaudara abin da ya sa aka yanke masa hukuncin shekara 7 a gidan yari, sai kuma, shekara 5, saboda amfani da matsayinsa ba bisa ka'ida ba.

  19. PDP ta yi wa APC shagube kan zaben Abdullahi Adamu a matsayin shugabanta

    Sanata Adamu

    Asalin hoton, APC

    Bayanan hoto, Sanata Adamu

    Babban jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP, ta bayyana zaben sabon shugaban jam'iyyar APC Abdullahi Adamu da aka yi a matsayin abin dariya, inda ta ce jam'iyyar ta tafka babban kuskure.

    PDP ta ce zaben da aka yi na cike da badakala kala-kala, kama daga batun yaudara da cin hanci da dai makamtansu.

    Babbar Jam'iyyar adawar ta ce za a fuskanci almubazzaranci da jefa jam'iyyar cikin halin kaka ni kayi saboda bisa dukkan alamu jagorancin jam'iyyar ta APC, ya koma hannu wadanda basu san hakkin jama'a ba.

    Sannan kuma a cikin shekara guda da ya rage wa shugaba Buhari ya sauka daga mulki, dole Najeriya ta fuskanci wasu sauye sauye marassa ma'ana saboda yanayin yadda shugabancin jam'iyya mai mulkin zai kasance in ji PDP.

    Daga nan PDP, ta bukaci 'ya'yan jam'iyyar APC, da sy fito su wanke sabon shugaban jam'iyyar ta su sanata Adamu, daga zarge zargen cin hancin da ake masa.

    PDP ta ce yana da kyau Sanata Adamu ya fito fili ya bayyana wa 'yan Najeriya dalilinsa na kin bayyana a gaban kotu a lokacin da ake shari'arsa a babbar kotun tarayya.

  20. Ana zanga-zanga a fadin duniya don nuna goyon baya ga Ukraine

    An gudanar da zanga-zanga a fadin duniya ranar Lahadi, inda ake kira a kawo karshen yakin Ukraine.

    Wasu masu zanga-zanga a wajen Majalisar Dokokin Birtaniya da ke  birnin London ranar Lahadi

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wasu masu zanga-zanga a wajen Majalisar Dokokin Birtaniya da ke birnin London ranar Lahadi
    A Lebanon, masu zanga-zanga sun daga wata babbar tuta a Beirut, babban birnin kasar

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, A Lebanon, masu zanga-zanga sun daga wata babbar tuta a Beirut, babban birnin kasar
    Wannan matar tana rike da kwalin da ke cewa yakin wata daya ya isa inda suka tsaya a Ofishin Jakdancin Rasha da ke Chisinau, Moldova

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Wannan matar tana rike da kwalin da ke cewa yakin wata daya ya isa inda suka tsaya a Ofishin Jakdancin Rasha da ke Chisinau, Moldova
    Masu zanga-zanga a Amurka sun isa ginin the National Mall da ke Washington

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Masu zanga-zanga a Amurka sun isa ginin the National Mall da ke Washington