Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail
Rufe makarantun mata a Afghanistan abin takaici ne - Guterres
Sakatare Janar na Majalisar
Dinkin Duniya ya ce matakin Taliban na rufe makarantun sakandiren yammata a
Afghanistan abin takaici ne.
Antonio Guterres, ya bayyana
matakin a matsayin abin da zai gurbata rayuwar 'ya'ya mata a gaba.
Ya bukaci Taliban da ta sake bude
makarantun sakandiren matan ba tare da bata lokaci ba.
A yau ne aka umarci daliban da
suka koma makaranta a karon farko tun bayan da Taliban ta karbe ikon kasar
watanni bakwai da suka wuce da su koma gida, abin d aya janyo yammatan suka
rinka kuka saboda takaici.
Tsohuwar Sakatariyar harakokin wajen Amurka Madeleine Albright ta mutu
Madeleine Albright, mace ta farko da ta zama sakatariyar harkokin wajen Amurka, ta rasu tana da shekaru 84.
Albright ta zama babbar jami'ar diflomasiyya a 1997 zamanin mulkin Clinton, inda ta zama macen da ta taɓa riƙe babban muƙami a gwamnatin Amurka.
Mutum huɗu sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Kebbi
Asalin hoton, Zaidu Bala
Mutane hudu ‘yan
gida guda ne suka nutse a hatsarin kwale-kwale a jihar Kebbi da ke arewacin
Najeriya.
Hukumomi da mazauna
yankin sun ce waɗanda hatsarin ya rutsa da su suna hanyarsu ta zuwa gona
tsallaken rafi a lokacin da kwale-kwalen da suke ciki ya kife a ranar Laraba a
yankin Yauri sakamakon iska mai ƙarfin
gaske.
Mutum shida ne ke cikin kwale-kwalen, wani uba Musa Labaran da ƴaƴansa.
Ya shaida wa BBC cewa an samu gawar ƴaƴansa hudu yayin da ake ci gaba da neman gawar mutum na biyar da ba a gani ba.
An sha samun
hatsarin kwale-kwale a Najeriya
A watan Mayun
shekarar da ta gabata, sama da mutum 100 ne suka nutse a ruwa lokacin da
kwale-kwalen da suke ciki ya kife a jihar Kebbi yayin da a cikin watan Disamba
kimanin mutum 30 suka mutu a wani hatsari makamancin haka a jihar Kano.
Ana danganta irin
wannan al’amari ne da yadda ake loda wa
kwale-kwale kaya da mutane da suka wuce ƙima da rashin kula da jiragen na ruwa
da kuma rashin kyawun yanayi.
Nato za ta kara tura dakaru zuwa gabashin Turai
Asalin hoton, Getty Images
Sakatare Janar na Nato ya ce
kungiyar za ta amince da karin sojojin da aka aike zuwa gabashin Turai a wani
taron gaggawa da aka yi kan farmakin Rasha a Ukraine.
Jens Stoltenberg ya ce
za a aike tawaga hudu ta sojoji zuwa kasashen Slovakia da Hungary da Bulgaria
da Romania da ke gabashin Turai, kasashen da ke makwabtaka da Ukraine.
Abin da gwamnonin APC suka tattauna da Buhari
Asalin hoton, @GovKaduna
Gwamnonin APC
sun gana da shugaba Buhari a fadarsa da ke Abuja a ranar Laraba, ƙarƙashin
jagorancin shugaban gwamnonin kuma gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu.
Gwamnonin sun
ce sun tattauna da Bahari kan batutuwa da dama musamman game da babban taron
Jam’iyyar na ranar Asabar inda za a zaɓi shugabannin jam’iyyar.
Ganawar na zuwa a daidai lokacin da jam’iyyar APC mai
mulkin Najeriya ke ci gaba da fuskantar baraka da rashin jituwa tsakanin
jiga-jiganta kan babban taro na kasa da kuma zaben shugabanninta.
Tuni jam’iyyar ta kebe wa yankunan kasar mukamai
daban-daban – inda misali aka kebe wa yankin arewa ta tsakiya kujerar shugaban
jam’iyya na kasa.
Shugaban Buhari na kokarin ganin an kauce wa kada kuri’a
wajen zaben shugabanni, a maimakon haka yake neman a sasanta tsakanin ‘yan
takara, yayin da gwamnonin jihohi ke cewa za su goyi bayan duk wanda shugaba
Buhari ya ce a ba kujerar shugabancin jam’iyyar.
Sai dai wasu kusoshin jam’iyyar sun bayyana cewa ba su
yarda da wannan tsari ba, kamar tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari,
wanda ya ce zai ci gaba da fafutikar neman kujerar shugaban jam’iyyar duk da cewa
ba yankinsu ne aka kebe wa kujerar ba, kuma a ganinsa bai wa wani yanki ko wani
mutum mukamin ba tare da zabe ba, rashin adalci ne.
Gwamnan Kebbi Abubakar Atiku Bagudu, ya yi wa Ishaq
Khalid karin bayani kan ganawarsu da shugaba Buhari.
Bayanan sautiGwamnan Kebbi Abubakar Atiku Bagudu
An gano ɗaya daga cikin akwatin naɗar bayanai na jirgin China
Asalin hoton, Reuters
Masu aikin ceto a China sun gano ɗaya
daga cikin akwatin nadar bayanan da ke cikin jirgin saman kasar dauke da
fasinjoji fiye da dari da ya yi hadari.
Akwatin ya lalace sosai, sannan
ba a kai ga gano abin da ya haddasa hadarin jirgin ba.
Babu wanda ya tsira da ransa a
cikin jirgin, kodayake ana ci gaba da neman tarkacen jirgin duk da ruwan saman
da ya warwatsa su.
Jirgin ya yi hadarin ne a ranar
Litinin din da ta wuce inda ya fada kan wani yanki mai tsaunuka.
Putin ya ce da kuɗin Rasha za a yi cinikin gas
Asalin hoton, Reuters
Shugaba Vladimir Putin ya
ce Rasha za ta tabbatar da ƙasashen da ke gaba da ita sun biya kuɗin cinikin
gas da roubles.
Ya ba Babban Bankin Rasha mako ɗaya ya
samar da hanyar da za a sauya tsarin biyan kuɗin na Rasha maimakon wasu
kuɗaɗen.
Ya ce sauyin zai shafi biyan kuɗi ne kuma
za a ci gaba da samar da gas. Sai dai ba a san tasirin da wannan matakin zai yi
ba.
Yaƙi a Ukraine zai jawo ƙaruwar masu cutar tarin fuka a ƙasar - WHO
Jami'an lafiya da masu gangami a Ukraine sun ce akwai yiwuwar mamayar da Rasha ke yi za ta kara yawan masu fama da cutar tarin TB a watanni masu zuwa.
Ana samun mutum 30,000 da ke kamuwa da tarin TB a Ukraine duk shekara, abin da ya sa ta samar da sabbin hanyoyin yi wa masu cutar magani.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce Ukraine ta samar da sabbin hanyoyi masu inganci na y iwa masu tarin TB magani.
Jami'an WHO sun nuna fargabar cewa faɗa da ake yi a kasar zai iya janyo koma-baya a kokarin kasar na shawo kan cutar.
Dokar Zaɓe a Najeriya: Majalisa za ta ɗaukaka ƙara kan umarnin kotu na goge sashe na 84(12)
Asalin hoton, NASS
Majalisar Wakilan Najeriya ta yanke shawarar ɗaukaka ƙara kan hukuncin da Kotun Tarayya ta yi na bai wa Ministan Shari'a Abubakar Malami umarnin goge sashe na 84(12) na Dokar Zaɓe ta 2022.
Majalisar ta nemi ministan shari'ar kuma antoni janar da ya dakatar da aiwatar da umarnin har sai an kammala ɗaukaka ƙarar.
Ita ma Majalisar Dattawa ta ce za ta ɗaukaka ƙarar bayan sanatoci da dama sun bijiro da buƙatar yin hakan a zamansu na yau Laraba.
Kakakin Majalisa Femi Gbajabiamila ya koka kan dalilin da ya sa aka kai ƙarar kotun da ke Jihar Abiya a kudancin Najeriya, yana mai cewa "majalisa ce kaɗai ke da ikon sauyawa ko yin doka a kundin tsarin mulkin Najeriya".
Wakilin BBC da ya halarci zaman a Majalisar Dattawa ya ce an samu 'yar hatsaniya a lokacin da Sanata Sani Musa daga Jihar Neja ya buƙaci a cire sunansa daga jerin waɗanda suka amince a ɗaukaka ƙarar.
Sanatan da ke wakiltar Mazaɓar Neja ta Tsakiya na cikin 'yan takarar neman shugabancin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya a zaɓen da a gudanar ranar 26 ga watan Maris.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Dakarun Ukraine sun ƙwato gari a kusa da Kyiv
Asalin hoton, Reuters
Dakarun Ukraine na mayar wa da na Rasha martani a wasu yankunan, inda wasu rahotanni ke cewa sun ƙwace wani gari a kusa da Kyiv babban birnin ƙasar.
Mahukunta a garin Makariv da ke yamma da Kyiv sun ce tutocin Ukraine ne ke tashi a garin ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
Wani mai sharhi kan harkokin tsaro a Birtaniya ya faɗa wa BBC cewa martanin da dakarun Ukraine ke mayarwa ka iya sa Rasha ta sauya salon kai hari.
Haka ma mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Amurka ya ce Ukraine na ƙara kama garuruwa a kudanci.
Mayaƙan sa-kai da dakarun Ukraine sun lalata wani ayarin motocin soja na Rasha a garin Voznesensk sannan suka kore su daga garin.
Haka nan, dakarun Ukraine na yunƙurin ƙwato garin Kherson wanda Rasha ta fara ƙwacewa.
Sai dai wakilin BBC a Kyiv, James Waterhouse, ya ce labarin nasarar ba wani mai girma ba ne bayan shafe kwanaki ana fafata yaƙi a wuri ɗaya da kuma ƙarin hare-hare ta sama da ruwan makaman atilare.
Atiku ya ƙaddamar da takararsa, zai mayar da hankali kan abu biyar
Asalin hoton, The Cable
Alhaji Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban Najeriya, ya ƙaddamar da takarar neman shugabancin ƙasar a babban zaɓe na 2023 mai zuwa a jam'iyyar adawa ta PDP.
Atiku, wanda ya shafe shekara fiye da 15 da suka wuce yana neman shugabancin Najeriya, ya ce zai mayar da hankali kan ɓangare uku idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.
Da ya ke jawabi yayin taron, Atiku ya ce gwamnatinsa za ta zama gada tsakanin mulkin dattijai da na matasa.
"Gwamnatinmu za ta zama kamar gada ce [da za ta haɗa] tsakanin mulkin dattijai da na matasa."
Ya ci gaba da cewa: "A ƙarƙashin mulkina, zan mayar da hankali kan ɓangare biyar masu muhimmanci; haɗin kan Najeriya, tsaro, tattalin arziki, ilimi, ciyar da ɓangarorin gwamnatin tarayya gaba da ƙara musu iko."
Bikin ya gudana a International Conference Centre da ke Abuja a yau Laraba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
NDLEA ta kama ƙwayar Tramadol miliyan biyu a Legas
Asalin hoton, NDLEA
Hukumar NDLEA mai yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ce ta kama ƙwayar Tramadol kusan miliyan biyu tare da maganin tari na Codeine a filin jirgin sama na Muratala Muhammad da ke Legas.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar a yau Laraba ta ce an shigar da ƙwayoyin ne daga Pakistan da kuma Birtaniya.
Ta ƙara da cewa an ƙwace kayan a ranar 10 ga watan Maris, inda aka samu ƙwaya samfurin Co-codamol 349,800 wadda gwamnati ta haramta.
Sai kuma a ranar 15 ga Maris, inda jami'an NDLEA tare da haɗin gwiwar na Kwastam suka kama ƙwayar Tramadol 1,584,000 a filin jirgin.
A gefe guda kuma, NDLEA ta kama wani ɗan shekara 50 da yunƙurin shigar da hodar ibilis mai nauyin 11.91kg zuwa Ghana ta kan iyakar Seme da ke Legas.
A cewar sanarwar, waɗanda suka yi safarar ƙwayoyin sun yi amfani da motar jigilar kaya ta cikin filin jirgi mai suna Skyway Aviation Handling Compnay (SAHCO).
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Taliban ta dakatar da sake buɗe makarantun 'yan mata a Afghanistan
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Taliban ta sauya matsaya kan ƙyale 'yan mata su koma makarantun sakandare a Afghanistan, tana mai cewa har yanzu ba a yanke hukunci ba kan kayan makarantar da za su saka ba.
Tun farko an tsara sake buɗe makarantu a faɗin ƙasar watanni bayan rufe su tun bayan da Taliban ɗin ta sake ƙwace mulki a watan Agusta.
Sai dai lokaci guda ma'aikatar ilimi ta sanar cewa makarantun mata za su ci gaba da kasancewa a rufe, abin da ya jawo ruɗani.
Wasu daga cikin 'yan matan sun fashe da kuka yayin da iyaye da ɗaliban ke nuna ɓacin rai da matakin na ba-zata.
Da yawan ɗaliban sun yi ta murna za su koma azuzuwansu.
Gobara ta ƙona wurin haɗa kwalta a Kano
Wata gobara da ta tashi a birnin Kano ta yi sanadiyyar ƙona mota ɗaya tare da ƙone ramukan saukewa da haɗa kwalta.
Wutar ta fara ci ne da misalin ƙarfe 7:00 na safiyar yau Laraba a kan Titin Hadeja.
Wakilin BBC a Kano ya ce har zuwa ƙarfe 9:50 ba a kashe wutar ba.
Buhari na jagorantar Majalisar Zartarwa
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na jagorantar taron Majalisar Zartarwa da ake gudanarwa duk mako a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja babban birnin ƙasar.
Wannan ne karo na farko da Buhari ke jagorantar zaman tun bayan da ya koma Najeriya daga Landan, inda ya je ganin likita.
Ministoci da manyan ma'aikatan fadar shugaban ƙasa ne ke halartar taron na duk Laraba don tattauna ayyukan gwamnatin da kasafi da kuma tsare-tsare.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Majalisa ta nemi CBN ya tilasta amfani da kuɗin sulalla a Najeriya
Asalin hoton, Ma-shops.com
Majalisar Wakilai a Najeriya ta nemi Babban Bankin ƙasar CBN ya tilasta amfani da sulalla da zimmar daƙile hauhawar farashi da kuma inganta tattalin arziƙi.
Majalisar ta yi kiran ne yayin zamanta na Talata bayan ɗan majalisa mai wakiltar Mazaɓar Toro ta Jihar Bauchi, Umar Lawal, ya gabatar da ƙudirin neman hakan.
An shafe shekaru ba a amfani da kuɗin ƙarfe ko kuma sulalla a Najeriya waɗanda su ne kobo 50 da naira 1 da naira 2.
Mafi ƙanƙantar kuɗi a Najeriya ita ce takardar naira 5, wadda da kyar ake samun abin da za a iya saya da ita saboda hauhawar farashi.
Game da yaƙi a Ukraine zuwa yanzu...
Asalin hoton, Getty Images
Yayin da muke fara kawo rahotannin a wannan safiya, ga abubuwan da ke faruwa a taƙaice:
Ana ci gaba da ruguntsumi a tsakiyar birnin Mariupol, wanda Rasha ke yi wa luguden wuta. Gwamnatin Ukraine ta ce fararen hula kusan 100,000 ne yaƙin ya tarfa ba tare da abinci da ruwa ko abin ɗumama ɗaki ba
Sai dai Shugaban Ukraine ɗin Volodymyr Zelensky ya ce duk da fafatawar da ake yi an yi nasarar kwashe mutum 7,026 daga Mariupol ranar Talata
Rundunar sojan Ukraine ta yi iƙirarin cewa "gwiwar dakarun Rasha ta yi sanyi", kuma yanzu mahukunta a Rashar na yunƙurin ɗaukar tsofaffin sojoji don shiga yaƙin
Mai magana da yawun shugaban Rasha, Dmitry Peskov, ya ƙi ya kawar da yiwuwar amfani da makamai masu guba. Cikin wata hira da kafar yaɗa labarai ta CNN, Mista Peskov ya ce za a iya amfani da su idan aka yi wa ƙasarsa barazana
Amurka ta yi Allah-wadai da batun, tana mai cewa na "rashin kamun kai ne kuma ba haka ƙasar da ke da makamin nukiliya ya kamata ta yi ba"
Kazalika, Amurka ta ce dakarun Ukraine na samun nasarar sake ƙwace iko da wasu garuruwa daga hannun na Rasha, musamman a yankin kudancin ƙasar
Gwamnan Jihar Sokoto a arewacin Najeriya Aminu Waziri Tambuwal ya ce aikin ɗan sanda yana da muhimmanci sosai ga tsaron Najeriya, abin da ya sa zai ƙirƙirii 'yan sandan jihohi idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2023.
Da yake magana ta cikin shirin Politics Today na Channels TV ranar Talata, Tambuwal ya ce "wajibi ne a yi maganin matsalar tsaro tun daga tushe".
A cewarsa: "Ina da tsarin yadda za a yi. Dole ne mu mayar da abin [tsaro] ga matakin al'umma. Dole mu tattauna kan 'yan sandan jihohi, mu matso da tsaro ksua da al'umma."
Da aka tambaye shi ko zai gabatar da ƙudirin neman kafa dokar 'yan sandan jihohi ga majalisa, ya tabbatar da cewa zai yi hakan.
"Idan ta kama ni a matsayina na shugaban ƙasa zan iya ɗaukar ƙudirin da kaina na kai wa shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisa. Saboda na yi imanin yana ɗaya daga cikin abubuwan da muke buƙata da gaggawa don kawo ƙarshen matsalar tsaro."
Gwamna Aminu Tambuwal na neman samun tikitin takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar adawa ta PDP, inda zai fafata da irinsu Atiku Abubakar da Bukola Saraki da Gwamna Bala Muhammed na Bauchi.
An daɗe ana muwahara game da dacewa ko akasin haka ta kafa 'yan sandan jihohi a Najeriya, abin da a yanzu haka kundin tsarin mulkin ƙasar bai ba da dama ba, inda gwamnatin tarayya ce kaɗai ke iko da 'yan sandan.
Yaƙi ya jefa mutum 100,000 cikin mawuyacin hali a Mariupol - Ukraine
Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatar tsaro ta Amurka, Pentagon, ta ce sojojin Ukraine na yin nasarar sake karbe iko ta kasa daga mamayar sojojin Rasha, musamman a garuruwa da biranen da ke kudancin kasar.
Ana ci gaba da gwabza kazamin fada tsakanin dakarun Rasha da na Ukraine a birnin Mariupol mai tashar jirgin ruwa, birnin da Rasha ta zafafa yi wa ruwan wuta da makaman roka da na Atilare.
A sakon bidiyo na baya-bayan nan, Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce halin da ake ciki a Mariupol ya munana.
"Akwai kusan mutum 100,000 a birnin da ke cikin mawuyacin hali saboda an toshe su baki daya. Sama da mako ɗaya ban da ruwan bama-bamai babu abin da ake yi musu, babu abinci, babu ruwan sha, babu magani, suna cikin tashin hankali." in ji shi.
Maraba
Barkanmu da sake haɗuwa a wannan shafi na rahotanni kai-tsaye tare da ni Umar Mikail.
Ku biyo mu don sanin halin da duniya ke ciki, musamman a yaƙin Ukraine da kuma sassan nahiyar Afirka a yinin yau Laraba - ta bawa ranar samu.