Zelensky ya ce a shirye yake ya tattauna da Putin gaba da gaba

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Awwal Ahmad Janyau

  1. EU za ta tattauna kan sauya dabarun tsaro a nahiyar

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    A yau ne ministocin kasashen Tarayyar Turai za su gana a Brussels, domin daddale magana guda kan matakin da Turai za ta dauka na tsaron yankin ta hanyar sauya dabaru.

    Jami'ai sun ce za a tabo batun zahirin halin da ake ciki kan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.

    Cikin wannan makon ma birnin Brussels na Belgium zai karbi bakun cin taron kungiyar tsaro ta NATO.

    Tarayyar Turai na amfani da matakan tsaron tun ma kafin Rasha ta mamaye Ukraine, sai dai jami'ai sun ce tabbas za tattauna kan abubuwan da ke faruwa a zahiri.

  2. Amurka ta ce abin da aka yi wa musulman Rohingya 'kisan kare-dangi ne'

    BBC

    Jami'an gwamnatin shuga Biden na Amirka, sun ce a hukumance gwamnati za ta ayyana kisan da sojojin Myanmar suka yi wa tsirarun kabilun Rohingya a Myanmar da na kare dangi.

    Ana sa ran sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, zai yi wannan sanarwa a yau Litinin idan ya kai ziyara gidan kayan tarihi na Holocaust da ke Washington.

    Zai bude bikin baje koli mai taken ''Hanyar da aka bi a kisan kare dangin Burma".

    Dubban musulmn Rohingya ne fadan ya tilastawa barin muhallansu da Myanmar baki daya, lokacin da sojojin kasar suka kaddamar da hari kan su a shekarar 2017.

    Sama da mutum 6000 aka kashe cikin watan farko da fara tashin hankalin a Myanmar.

  3. China ta aika da taimakon kayan agaji Ukraine

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    Tuni aka sanar da cewa hukumar agajin gaggawa ta China za ta aika kimanin dala miliyan 1.5 a matsayin taimakon jin kai ga Ukraine.

    Hakan na cikin wata sanarwa ne da kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ya fitar.

    A baya, kasar ta yi alkawarin bayar da rabin wadannan kudade a matsayin taimako ga Ukraine.,

    Wannan na nufin adadin da aka bayar na da matukar amfani a daidai wannan matsanancin yanayi.

    An ta hasashen matsayar China cikin rikicin da ke faruwa, tun lokacin da Rasha ta fara mamayar Ukraine.

    China dai ba ta cikin kasashen da suka sanya wa Rasha ta kunkumi.

  4. Harin kunar bakin wake ya kashe sama da sojin Burkina Faso 10

    BBC

    Sama da sojoji 10 ne suka mutu a wani hari da ake zargin masu ikirarin jihadi da aki wa a yankin gabashin Burkina Faso, kamar yadda rundunar sojin kasar ta bayyana.

    Hakan ya biyo wani hari da aka kai kan wata tawagar soji ta sintiri a ranar Lahadi a yankin Natiaboni, wani kauye da ake yawan kai wa hari a-kai-a-kai.

    Sojin Burkina Faso sun kwace iko da kasar ne a watan Janairu tare da hambarar da shugaba Roch Kaboré, inda suke zargin shi da kasa kawar da masu ikirarin jihari.

    Rikicin da aka fara tun 2015 ya sanadin mutuwar duban mutane tare da sanya miliyoyin tserewa sa muhallamsu.

  5. Tawagar Ecowas ta bar Mali ba tare da cimma matsaya kan zaben kasar ba

    Reuters

    Asalin hoton, Reuters

    Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya kammala ziyarar aiki ta kwanaki biyu a kasar Mali,ba tare da an cimma wata yarjejeniya kan lokacin da za a yi zaben da zai maida kasar tafarkin Dimukradiyya.

    Gwamnatin Mali da ta karbe ikon kasar shekarar 2020, ta ce ba ta ji dadin yadda aka kasa cimma matsaya ko tartibiyar magana ba.

    Mr Jonathan dai shi ke shiga tsakani a madadin kungiyar ECOWAS ko CEDEAO,ya kuma je ne da niyyar tsaida lokacin da za a yi zabe, sakamakon korafin shekaru biyar sun yi yawa karkashin mulkin soji.

    Kungiyar ECOWAS da Tarayyar Turai sun kakabawa mambobin gwamnatin rikon Mali takunkumi, ciki har da 'yan gaban goshin shugaba Assimi Goita.

  6. Rasha na ci gaba da luguden wuta a Ukraine

    BBC

    Rasha ta ci gaba da kai hare-hare biranen Ukraine, a daren jiya an yi luguden wuta a babban birnin kasar Kyiv.

    Magajin birnin Vitali Klitschko, ya ce yawancin gidaje da manyan kantunan saida kayayyaki sun ragargaje saboda makaman roka da na atilari da sojin Rasha sukai musu.

    Tetiana Lomakina ita ce mai bai wa shugaba Zelensky shawara ta al'amari na kara kazanta fiye da yadda ake zato.

    Tace kashi 90 cikin 100 na gine-ginen birnin ya lalace, ba mu san adadin mutanen da baraguzan gini suka danne ba, wanda ba za mu iya cirowa ba saboda ci gaba da luguden wutar da ake yi mana, ko a jiya bam ya fada wata makarantar yara kananan, abin akwai tada hankali..

  7. Budewa

    Masu bibiyarmu barka da tashi da fatan an wayi gari lafiya.

    Buhari Muhammad Fagge ke fatan kasancewa da ku a wannan yini, domin kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya.

    Ku kasance da mu.