Zelensky ya ce a shirye yake ya tattauna da Putin gaba da gaba

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Awwal Ahmad Janyau

  1. Nan za mu dakatar da kawo labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

    Sai gobe!

  2. Amurka ta ce an yi wa ƴan Rohingya kisan kiyashi

    Amurka ta amince cewa aika aikar da sojojin Bama suka yi akan tsiraru 'yan kabilar Rohinja daidai yake da laifin take hakkin bil’adama da kuma kisan kiyashi.

    Dubban mutane aka kashe, sannan wasu dubban sun gudu zuwa Bangladesh tun bayan da sojojin suka afka musu a 2017.

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya ce akwai rana da zata zo ga su wadanda suka aika wanann aika aikar da za su amsa laifinsu na cewa cewa suna son kawar da musulmi 'yan kabilar Rohinja ne yasa suka yi haka.

    Ya ce, hari a kan 'yan kabilar Rohinja yana da yawan gaske kuma kamar tsararren abu ne, wanda shi aka duba wajen yanke shawara akan cewa abin da aka aikata ya yi kama da laifukan take hakkin bil adama.

    Shaidar da aka samu ta nuna karara cewa akwai batun kisan kiyashi a ciki.

    Mr Blinken, ya ce Amurka zata samar da dala miliyan daya domin gudanar da bincike akan kisan kiyashin.

    Tuni masu fafutuka da kuma 'yan Rohinjan suka yi maraba da matakin Amurkan.

  3. An ba ma’aikatan da ke son takara a Neja wa’adi su ajiye aiki

    Gwamna Sani Bello

    Asalin hoton, @abusbello

    Gwamnatin Neja ta ba ma’aikatan gwamnati da ke son takara a zaɓen 2023 wa’adi su ajiye aiki.

    Wata sanarwa daga ofishin sakataren gwamnatin jihar ta ce gwamna Abubakar Sani Bello ya bayar da umarni ga duk wani ma’aikaci da ke da niyyar takara ya ajiye aikinsa kafin 31 ga watan Maris na 2022.

    Gwamnan ta ce wannan na ƙarƙashin dokar zaɓe da shugaba Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu da ta ce duk wani ma’aikaci ko mai riƙe da muƙamin gwamnati ya ajiye aikinsa kafin gudanar da zaɓen fitar da gwani na jam’iyyu.

  4. Hare-haren Rasha sun kashe mutumin da ya tsarewa kisan ƴan Nazi

    Mutumin da ya tsira a kisan da 'yan Nazi suka yi wa Yahudawa ya mutu sakamakon hare haren da Rasha ta kai birnin kharkiv da ke gabashin Ukraine.

    Iyalan Boris Romantschenko, sun ce ya mutu ne a gidansa ranar Juma’a bayan Rasha ta jefa bam.

    Mutumin mai shekara 96, dakarun Nazi sun ma shi kofar rago inda aka kamashi aka kai shi sansanin da aka yi wa Yahudawa kisan gilla shi da wasu.

    A lokacin da ya kai ziyara sansanin a shekarar 2012, ya rera wani take ga wadanda suka rayu domin samar da kyakkyawan tunani da zaman lafiya har da samun 'yancin gashin kai.

  5. Zulum ya hana a saka wa sabon ginin makaranta sunansa

    Gwamna Zulum

    Asalin hoton, Borno state Govt

    Gwamnan Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi watsi da sunansa da aka saka a ginin wasu ɗakunan kwanan ɗalibai a Kwalejin fasaha ta Ramat a Maiduguri na gwamnatin jihar.

    Zulum ya yi watsi da karamcin ne lokacin da yake ƙaddamar da ginin da ma’aikatar ilimi ta gyara.

    A sanarwar da gwamnatin Borno ta fitar, Zulum ya ce “Ba zan yarda a saka sunana a wani aikin gwamnati ba, a lokacin da nake kan mulki. Ya kamata ko za a yi sai na gama wa’adi na.”

    Maimakon sunansa, gwamna Zulum ya buƙaci a sauya zuwa “ɗakin kwanan ɗalibai maza.”

  6. Kotu ta tuɓe ƴan majalisar jihar Cross Rivers 20 da suka sauya sheƙa

    Kotu

    Asalin hoton, Other

    Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta kori ƴan majalisar dokokin jihar Cross River guda 20 da suka sauya sheƙa.

    Jam’iyyar PDP ce ta shigar da ƙarar ‘yan majalisar kan sauya sheka da suka yi zuwa jam’iyyar APC.

    A ranar litinin ne kotun ta zartar da hukuncin, kamar yadda jaridun Najeriya suka ruwaito.

    Alƙalin kotun ya ce, ƴan majalisar su bar kujerunsu bayan sun yi watsi da jam’iyyar da ta ɗauki nauyinsu har suka samu muƙaman.

    Ƴan majalisar dai na da damar ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin kotun.

  7. Rasha ta haramta Facebook da Instagram

    Facebook

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kotu a Moscow ta haramta Facebook da Instagram a ƙasar inda ta bayyana ayyukansu “masu tsauri,” kamar yadda rahotanni suka bayyana.

    Alƙalin kotun Olga Solopova ya ce: mun amince da buƙatar masu shigar da ƙara na haramta ayyukan kamfanin Meta, kamar yadda kamfanin dillacin labaran Tass na Rasha ya ruwaito.

    Ofishin babban mai gabatar da ƙara ya ce ana yaɗa abubuwa da dama a kafofin sadarwa da ke kiran farwa ƴan Rasha da suka haɗa da sojojin da ke Ukraine.

    Tun da farko an toshe Facebook da Instagram a Rasha kan abin da gwamnatin Moscow ta bayyana “labaran ƙarya” da ake yaɗawa kan mamayar Ukraine.

    Kamfanin Meta mallakin Facebook da Instagram ya ce zai ba ƴan wasu ƙasashe damar kiran yaƙi da shugaba Vladimir Putin da kuma sojojin Rasha, inda ya bayar da dama ta wuccin gadi a wallafa bayanai kamar “kisa ga sojojin Rasha masu mamaya,” wanda ya saɓa ƙa’idojinsa.

    Alƙalin kotun ya ce hukuncin bai shafi kafar WhatsApp ba, mallakin kamfanin Meta.

  8. Zelensky ya ce a shirye yake ya tattauna da Putin gaba da gaba

    BBC

    Mai magana da yawun shugaba Putin ya ce har yanzu babu wani ci gaba a yayin tattaunawa da Ukraine a kan rikicin da kasashe ke yi tsakaninsu.

    Dmitry Peskov, ya ce akwai bukatar a samu ci gaba sosai a tattaunawar kafin Mr Putin da takwaransa na Ukraine Volodomyr Zelensky su tattauna kai tsaye.

    Ya bukaci masu ruwa da tsaki da su matsawa Ukraine a kan ta tsaya domin a cimma wani abu a tattaunawar.

    Mr Zelensky ya nanata cewa a shirye yake ya tattauna gaba da gaba da Shugaban Rasha.

  9. Buhari ya kira Ministan lantarki kan matsalar wutar da ake fama da ita a kasar

    NP

    Asalin hoton, NP

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kira Ministan Lantarki na kasar Abubakar Aliyu wata ganawar sirri a fadar gwamnatin kasar.

    Ana sa ran shugaban zai tattauna da shi kan matsalar wutar lantarki da ake fama da ita a fadin kasar a halin yanzu.

    Hakan na dauke ne cikin wata sanar da mai magana da yawun shugaban Garba Shehu ya fitar a ranar Litinin.

    Shugaban ya kuma kira Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo da mai ba shi shawara kan tattalin arziki Doyin Salami, domin ganawa da su.

  10. Najeriya ce kasa ta 114 cikin a jerin kasashen 146 da mutanensu suka fi jin dadi a duniya

    BBC

    Najeriya ce kasa ta 114 cikin jerin kasashe 146 da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da 'yan kasarsu suka fi jin dadi.

    Uganda ta zarce Tanzania da Kenya a jerin kasashen da mutanensu suka fi jin dadi a duniya.

    Kenya ce ke matsayi na 119, wanda hakan ke nufin ta kara yin kasa daga matsayi na 86 a bara, yayin da ita kuma Uganda take kasa da Kenya a shekarar da ta gabata da mataki biyu inda take matsayi na 83 .

    Tanzaniya ta dawo matsayi na 134 daga na 94 da take a baya.

    A jerin sunayen da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, Rwanda ita ce kasa ta karshe da mutanenta suke da karancin jin dadi a kasashen yankin, inda take matsayi na 147.

    Ba a sanya sunan kasahen Burundi da Sudan ba cikin jerin kasashen da mutanensu ke jin dadin rayuwa a duniya ba.

    Tsubirin Mauritius shi ne na daya cikin jerin kasashen Afrika da mutanensu suka fi jin dadi inda take matsayi na 44 a duniya.

    Finland itace ke matsayi na daya a duniya cikin shekaru hudu a jere kenen inda Denmark ke biye mata da Switzerland da Iceland da kuma Netherlands.

  11. Mutum 95 ne suka jikkata a hadarin jirgin kasa a Tunisia

    AFp

    Asalin hoton, AFP

    Adadin mutanen da suka jikkata a wani hadarin jirgin kasa a Tunis na Tunisia ne suka jikkata.

    Babu rahoton mutuwa ko guda sai dai tuni aka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti, kamar yadda tawagar masu ba da agajin gaggawa suka bayyana.

    "An garzaya da wadanda suka ji rauni zuwa asibiti amma babu wanda ya mutu zuwa yanzu," in ji kamfanin dillancin labarai na AFP.

    Daya daga cikin jiragen na dauke da fasinjoji dayan kima babu kowa ciki, in ji Moez Triaa kakakin hukumar tsaro ta Civil Defence.

  12. Mutum shida sun mutu a harin da Rasha ta kai wani kantin zamani a Kyiv

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'an Ukraine sun ce mutum 6 sun mutu an kuma lalata gidaje masu yawa a wani hari da dakarun Rashasuka kai wani baban kantin zama da ke garin Podilsky a yankin Kyiv.

    Cikin hotunan da aka wallafa, an nuna masu kashe wuta na ta ceto mutane.

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

  13. An sanya dokar hana fita a kananan hukumomin Jama'a da Ƙaura a Kaduna

    El rufai

    Asalin hoton, El rufai

    Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta sanya dokar hana fita a kananan hukumomin Jama'a da Ƙaura bayan shawarar da hukumomin tsaro suka ba ta, kuma ta ce dokar za ta fara ne nan take.

    Cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Samuel Aruwan ya fitar, tace nan gaba za a bayyana wasu sauran dokoki da suka shafi wadannan yankuna biyu.

    Wannan wani mataki ne da aka dauka domin taimakawa jami'an tsaron da ke aiki a yankin, su kare rayuka da dukiyoyin mutane tare da tabbatar da doka da oda.

    Cikin wata sanarwa da ma'aikatar cikin gida da harkokin tsaro ta fitar tace jami'an tsaro na da cikakken ikon aiwatar da dokar.

    Gwamnati ta nemi mutanen yankin da su bayar da hadin kai domin aiwatar da dokar wajen taimakawa a dawo da zaman lafiya a yankin.

    Gwamnatin jihar ta yi Allah-wadai da duk wani abi na tashin hankali a yankin.

  14. Labarai da dumi-dumi, Akalla mutum 65 ne suka jikkata a hadarin jirgin kasa a Tunisia

    Akwalla mutum 65 ne suka jikkata yayin da wasu jiragen kasa biyu suka yi taho mu gama da juma a kudancin Tunis babban birnin Tunisia.

    Babu rahoton mutuwa ko guda sai dai tuni aka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti, kamar yadda tawagar masu ba da agajin gaggawa suka bayyana.

    "An garzaya da wadanda suka ji rauni zuwa asibiti amma babu wanda ya mutu zuwa yanzu," in ji kamfanin dillancin labarai na AFP.

    Daya daga cikin jiragen na dauke da fasinjoji dayan kima babu kowa ciki, in ji Moez Triaa kakakin hukumar tsaro ta Civil Defence.

  15. Da alama Arsenal ta saki maciji a ciyawa

    Barcelona

    Asalin hoton, Barcelona

    Wata hanya daya da Barcelona ke son nuna ta fara dawowa hayyacinta karkashin tsohon dan wasanta da ke horar da kungiyar a yanzu Xavi Hernandez itace sanya magoya bayan Real Madrid yin tsit a filin wasa na Bernabeu a wasa mafi daraja El Clasico.

    Kungiyar na farfadowa a wasanin da take bugawa na kwanan nan, lokacin da taka ledarta ke komawa na 'yan shekarun baya lokacin da Xavi ke buga kwallon da kafarsa.

    Madrid ta shiga cikin sahun kungiyoyin da Barcelona ta ci kwallo 4 a wasanninta wajen 7 da ta buga.

    A gefe guda kuma masu sharhi na cewa Arsenal ta saki maciji a ciyawa, wato ana magana a kan dan wasan gaban ABrcelona tsohon dan kungiyar Arsenal din Pierre-Emerick Aubameyang.

    Dan wasan da ya ci wa Barcelona kwallo 9 a wasa 11 da ya buga wa kungiyar a duka gasa.

  16. Ukraine na ci gaba da yi wa Rasha turjiya

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Ukraine ta yi watsi da tayin da Rasha ta yi mata na bai wa mayakanta damar ficewa salin-alin daga birnin Mariupol da dakarun Rasha suka yi wa kawanya, matukar za su zubda makamansu.

    Mataimakin fira minista ya ce babu wani batu da za su aminta da shi, kawo daga ficewa da a zubda makamai.

    Andrei mazaunin Mariupol ne, wanda ke haka rami don binne makoftansa da suka mutu;

    Yace yana fatan za a shirya yi musu jana'za, wannan ta wucin gadi ce, an kashe masu 'yan uwa da bokan arziki.

    A kullum kashe mutane ake yi a birnin nan lamarin kullum kara kazancewa ya ke.

    Rasha dai ta gargadi hukumomin Ukraine cewa za su fuskanci ruwan bama-bamai da nakanab atilary matukar ba su mika wuya ba.

  17. 'Rasha ta ce babbar bukatarta shi ne ta mamaye Ukraine'

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar tsaron Burtaniya tace Rasha tace babu abin da ta sanya a gaba face ta mamaye Kyiv babban birnin kasar Ukraine.

    Rasha na shirin ci gaba da harba makamanta a Kyiv nan da mako mai zuwa.

  18. Za a saurari ra'ayoyin 'yan Tunisia kan sauyi a kundin tsarin mulkin kasar

    EPA

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Tunisia ya ce ko wanne dan kasar na da damar bayyana ra'ayinsa kan sauye-sauyen siyasar da ake shirin kawowa.

    Kais Saied wanda ya dakatar da majalisar kasar ya kuma zama mai cikakken iko a bra - ya bayyana hakan ne a gidan talabijin na kasar.

    Ya ce za mu saurari ra'ayoyin jama'a kan sauya kundin tsarin mulki da za mu yi a watan Yuli.

    Wannan bayanin nasa na zuwa ne bayan dubban 'yan kasar sun gudanar da zanga-zanga a ranar Lahadi a Tunis babban birnin kasar, wasu na ta ihun "a sauke shugaban kasa".

    Masu suka na cewa shugaban na son fadada ikonsa ne tare da take wasu hakkokin fararen hula da suka samu lokacin guguwar sauyi ta 2011.

    Ya ce wannan sauyin da za a yi, zai kawo karshen koma bayan da kasar ke fuskanta ta fuskar ci gaban tattalin arziki.

  19. Labarai da dumi-dumi, An sake sanya dokar hana fita a Kyiv babban birnin Ukraine

    Magajin garin Kyiv ya sanar da sanya dokar hana fita a fadin birnin baki daya, wadda za ta fara aiki daga yammacin Litinin zuwa safiyar Laraba.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa, mutanen birnin na cikin wani matsanancin hali saboda ruwan bamabami da suke sha.

    Ministan harkokin wajen kungiyar EU Josep Borrell ya yi tir da hare-haren Rasha a Mariupol a matsayin "gagarumin laifin yaki", yayin da kungiyar za ta tattauna yadda za a kra kakabawa Rasha takunkumi.

  20. Wane ne zai gaji Nasir El-rufai a Kaduna?

    Bayanan sautiLatsa nan domin sauraron rahoton

    A Najeriya, tun bayan da hukumar zaɓen ƙasar ta fitar da jadawalin zaɓukan 2023, ‘yan siyasa da sauran masu sha’awar tsayawa takara suka bazama neman goyon baya a zaɓukan fid da gwani da ake sa ran jam’iyyu za su fara a watan gobe.

    Kaduna, wadda daya ce daga cikin jihohin arewacin Najeriya, mai al'ummu mabambanta, na daga cikin jihohin Najeriya da ba za a iya hasashen mai zai faru ba ta fuskar siyasa a 2023, har sai abin da sakamako ya nuna yayin zabukan jihar.

    A kan wannan batu abokin aikinmu, Yusuf Tijjani, ya duba mana irin wainar da ake toyawa a fagen siyasar jihar Kaduna ga kuma rahotonsa cikin sauti da ke sama, sai a latsa domin sauraro.