An yaɗa wani bidiyon ƙarya na Zelensky yana miƙa wuya ga Rasha

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Sani Aliyu

  1. 'Yan Najeriya na kokawa saboda nau'ororin samar da lantarki sun sake lalacewa

    Electricity pole with a linesman on it

    Asalin hoton, Getty Images

    Lalacewar da tsarin samar da hasken lantarki ke yi ya ci gaba da saka 'yan Najeriya cikin duhu.

    Masu amfani da lantarki a gidajensu ko a wuraren aiki a biranen Legas da Enugu da Ibadan da Anambra da Abuja na rayuwa cikin wannan duhun saboda na'urorin samar da hasken lantarki sun sake gazawa.

    Wannan lamarin da ke faruwa ya zama ruwan dare gama duniya, kuma kamfanonin da ke samarda lantarki sun tabbatar da haka.

    Yini na biyu ke nan a jere da ake samun wannan matsalar ta lalacewar na'urorin samar da lantarki a fadin Najeriya.

    Matsalar na faruwa ne dadai lokacin da Najeriya ke fuskantar matsalar man fetur da wanda jirgin sama ke amfani da shi.

  2. Hotuna: Rasha na ci gaba da mamayar da ta ke yi a Ukraine

    Wata mata na kuka a cikin wani jirgin kasa da ke kan hanyar zuwa Poland, wani mutum na tuka kekensa a gaban wani ginin da bam ya ragargaza, sai wata tankar yaki da ke sintiri a wani layin da kusan babu koa cikinsa - wadannan ne batutuwan da muka kawo hotunansu gareku a yau.

    Many, like this woman, have been leaving the western city of Lviv for Poland

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Yawancin mazauna birnin Lviv na tserewa kamar yadda wannan matar ke yi
    Volnovakha, in the Donetsk region, has suffered heavily from the shelling

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Garin Volnovakha da ke yankin Donetsk ya sha wahala daga bama-baman da Rasha ke jefawa cikinsa
    Parts of the historical quarter of Odesa are filled with anti-tank hedgehogs

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ani bangare na unguwar Odesa da aka tara karafa domin hana tankunan yaki wucewa
    Many buildings in Volnovakha lie in ruins

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, An ruguza gine-gine masu yawa a garin Volnovakha
    First responders in a building hit by a rocket attack in Kharkiv

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Ma'aikatan bayar da agaji cikin wani gini da roka ya fada wa a Kharkiv
  3. Shin me ke faruwa ne a Ukraine?

    Ukraine's President Volodymyr Zelensky

    Asalin hoton, Facebook/Zelensky

    Idan yanzu ku ka fara bibiyar BBC, ga wasu muhimma abubuwan da suke faruwa a yakin da ake gwabzawa a Ukraine.

    • Sojojin Rasha na ci gaba da jefa bama-bamai a manyan biranen Ukraine inda suke rusa gine-gine a babban birnin kasar Kyiv a wannan safiyar
    • Mutum biyu sun sami raunuka bayan da bama-bama suka fada kan wani bene mai hawa 12 a gundumar Shevchenko.
    • An kafa dokar hana fita a birnin Kyiv yayin da Magajin Garin birnin Vitali Klitschko ke gargadi cewa an shiga wani yanayi "mai hatsari da wahala."
    • Sai dai akwai alamun ana samun ci gaba a tataunawar da Ukraine ke yi da Rasha inda shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ke cewa ya fara samun karfin gwuiwa
    • A birnin Mariupol kuwa na kudancin kasar da aka yi ma kawanya, mataimakin Magajin Garin birnin ya ce Rashawa na tsare da 'yan garin 400 cikinsu akwai likitoci da marasa lafiya "a wani yanayi da ya yi kama da na garkuwa aka yi da su"
    • Ma'aikatar tsaro ta Birtaniya ta ce dakarun Rasha na fuskantar matsaloli yayin da suke kokarin kutsawa cikin yankuna da biranen Ukraine da kawo yanzu ba sa hanunsu.
  4. Barkanmu da wayewar gari yau Laraba!

    Masu bibiyar mu a wannan shafi muna muku barka da safiya da fatan an tashi lafiya.

    Sani Aliyu ke fatan kasancewa da ku a wannan yini domin kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya daban daban, ciki har da yakin da ake gwabzawa tsakanin Rasha da Ukraine, da kuma wasu batutuwan da ke wakana a gida Nijar da Kamaru da Chadi da Ghana da kuma Najeriya.

    Muna fatan za ku ci gaba da kasancewa da mu!