An kai wani mummunan hari kan wani bene mai hawa tara a Kyiv
Akalla mutum daya ya rasa ransa kuma mutum uku sun sami raunuka bayan wani hari da aka kai kan wani ginin da fararen hula ke zama a Kyiv babban birnin kasar Ukraine, kamar yadda wata tashar talabijin mallakin gwamnatin kasar ta ruwaito.
Kawo yanzu hukumar bayar da agaji ta Ukraine ta ce an gano wasu gawarwaki biyu baya ga wasu mutum uku da aka kai asibiti bayn harin da aka kai da karfe 7:40 agogon Kyiv.
Hotunan da hukumar ta raba wa manema labarai sun nuna hayaki na tashi daga gini mai hawa tara yayin da 'yan kwana-kwana ke amfani da tsani domn ceto mazauna benen.