Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Amurka ta yi gargaɗi ga China kan goyon bayan Putin

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Sani Aliyu and Awwal Ahmad Janyau

  1. Nan za mu rufe wannan shafin da muke kawo rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

    Sai gobe.

  2. Hare-haren Rasha ta sama sun kashe mutum 9 a Ukraine

    Gwamnan lardin Rivne da ke arewa maso yammacin Ukraine, ya ce hare-haren jiragen saman Rasha kan wani gidan talbijin a yankin ya yi sanadin mutuwar akalla mutum tara.

    Mista Vitaliy Koval, ya ce wasu mutum tara kuma sun samu rauni yayin dabaraguzan gini suka danne wasu da dama.

    Magajin garin Kharkiv, birni na biyu mafi girma a Ukraine, ya ce har yanzu birnin na fuskantar luguden wuta.

    An kashe wani yaro dan shekara 15 , a lokacin da Rasha ta kai hari kan wata makarantar yara da ke kusa dagarin Chuguiv.

    'Yan awaren da Rasha ke goyon baya a gabashin Ukraine, sun ce makamai masu linzamin da Ukraine ta harba sun kashe mutum 17 a birnin Donetsk. Amma Ukraine ta musanta.

  3. Ƴan bindiga sun yi wa jami’an tsaro kwanton ɓauna

    Rahotanni daga Burkina Faso na cewa akalla jami'an tsaro 13 ne suka mutu a lokacin da wasu 'yan bindiga suka yi musu kwanton bauna a jiya Lahadi.

    Harin ya faru ne a kusa da garin Taparko, wanda mayakan jihadi ke yawan kai hari cikinsa.

    Tun da fari a ranar Asabar din karshen mako, wata motar bus ta taka nakiyar da aka dasa ta a tsakiyar hanya, inda mutum biyu suka mutu.

    Gwamnatin soji da ke mulki a Burkina Faso, ta sha nanata babban abin da ta sanya a gaba shi ne magance matsalar mayakan jihadi.

  4. Amurka ta yi gargaɗi ga China kan goyon bayan Putin

    Amurka ta ce ta yi gargaɗi ga China cewa babu wata ƙasa da za sha a koƙarinta na ceto ƙasar Rasha daga halin da ta shiga na takunkuman da aka ƙaƙaba mata kan hare-haren da ta ke kai wa a Ukraine.

    Mai ba da shawara kan sha'anin tsaro na amurka Jake Sullivan ya ɗauko batun kai-tsaye inda ya bayyana damuwarsa a lokacin da yake tattaunawa da jami'in diflomasiyyar China Yang Jiechi, a birnin Rome na Italiya.

    Ya ce Amurka tana kallon ta inda China za ta taimakawa Putin.

    Kafin tattaunawar a Rome, Jami'an Amurka sun ce Rasha har ta nemi taimakon soji ga China. Gwamnatin China kuma ta bayyana ikirarin na Amurka a matsayin labarin kanzon kurege.

  5. ‘Yaƙin Rasha a Ukraine zai haifar da mummunar yunwa a duniya’

    Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya yi gargadin cewa yakin da Rasha ke yi a Ukraine ka iya janyo abin da ya kira mummunar yunwa da kuma karancin abinci a duniya baki daya.

    Ya ce, yawancin kasashen Afirka da kuma kasashe matalauta sun dogara kacokam a kan alkamar da Rasha da Ukraine ke samarwa.

    Ya ce, ''abinci da man fetur da kuma takin zamani duk farashinsu ya yi tashin gwauron zabo, sannan karancin kudade da kuma jinkiri wajen shigar da kaya ko fitar da su duk matsala ce.”

    Ya ce duk wadannan ka iya jefa kasashe matalauta cikin garari.

    Wadannan kasashe sun hada da Burkina Faso da Somalia da kuma Yemen wadanda tuni suke fadi-tashin yadda zasu ciyar da al'ummarsu.

    Mr Guterres, ya yi kiran da a gaggauta tsagaita wuta domin guje wa fadawa matsalar karancin abinci a duniya.

  6. Birtaniya ta nemi taimakon Saudiyya kan tsadar fetur

    Gwamnatin Birtaniya za ta tattauna yadda za ta samar da wasu hanyoyi na samar da mai bayan matsalar da yaƙin Ukraine ta haifar, kamar yadda gwamnatin ƙasar ta bayyana.

    Farashin fetir da direbobin Birtaniya ke saye ya kai sama da fam 1.60 a kowace lita a cikin ‘yan kwanakin nan.

    Mai magana da yawun Firaiministan Birtaniya ya ce tattaunawar da Saudiyya za ta diba yadda za a magance matsalar a kasuwa.

    Wannan na zuwa bayan Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa kan mutum 81 a ranar Asabar.

    Ofishin ministan harakokin waje ya ce gwamnatin Birtaniya ta damu da kisan, tare da jadadda adawa da zartar da hukuncin kisa a ko wane yanayi.

    Mamayar Rasha a Ukraine ne ya haifar da tsadar farashin ɗanyen mai da kuma tsadar fetir a Birtaniya.

  7. Ƴan Sudan na zanga-zangar adawa da tsadar burodi

    Jami'an tsaro a Sudan sun harba hayaki mai sa hawaye kan masu zanga-zangar adawa da ƙarin farashin burodi da man fetur.

    An gudanar da zanga-zanga a faɗin Sudan.

    Masu zanga-zangar sun ce an yi amfani da harsashi a birnin Damazin da ke kudu maso gabashin kasar.

    A ranar Lahadi, farashin burodi ya karu da sama da kashi 40, haka ma an kara kudin man fetir.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ɗaya bisa uku na yawan al'ummar Sudan na dogaro ne da tallafi. Matsalar ta ƙara ƙamari tun juyin mulkin bara wanda ya sa masu bayan da tallafi suka dakatar da tallafawa ƙasar.

  8. An ɗage tattaunawar Rasha da Ukraine zuwa Talata

    An ɗage tattaunawar jami'an Rasha da Ukraine karo na hudu,a yayin da Rasha ke ci gaba da mamaya.

    Jagoran masu tattaunawar daga Ukraine, Mikhailo Podolyak, ne ya ɗage tattaunawar kan wasu dalilai.

    Tun da farko ya bayyana tattaunawar a matsayin mai tsauri.

    Ya ce bangarorin biyu sun bayyana wa juna matsayarsu kan yakin da ake gwabzawa.

    Ya ce a takaice mun koma teburin tattaunawa tare da wakilan Rasha. A tattaunawar ta zagaye ta hudu, za mu nuna musu cewa kwanaki 19 da aka shafe ana yaki, mu a wajenmu ba muji dadinsu ba.

    Bangaren Ukraine ya jaddada batun tsagaita wuta da kuma janye dakarun Rasha ba tare da bata lokaci ba.

    A baya bayan nan bangarorin biyu sun bayyana cewaya kamata a rubuta yadda za a cimma matsaya.

    Tattaunawa uku da aka yi a bayata mayar da hankali ne a kan batutuwan da suka shafi bayar da kafa ga fararen hula su fice daga wuraren da rikici ya yi kamari.

    Shugaban Ukraine, wanda ke son tattaunawa kai tsaye tare da takwaransa na Rashaya bayyana hanyar tattaunawar a matsayin mai wuyar gaske, amma ta zama dole.

  9. Layukan lantarki sun sake lalacewa a Chernobyl - Ukraine

    Kamfanin samar da makamashi a Ukraine ya ce dakarun Rasha sun lalata wani babban layin da ke hada wa tashar Chernobyl da manyan turakan da samar da hasken lantarki a kasar.

    Matsalar ta auku ne jim kadan bayan da aka mayar da hasken lantarki ga tashar, sai dai BBC ba ta iya antance sahihancin wannan rahoton ba.

    Kamfanin mai suna Ukrenergo mallaki gwamnatin kasar bai sanar ko tsohuwar tashar samar makamashin nukiliyar ta rasa lantarki baki daya ba a sanadin lalacewar layin da ke samar da lantarkin.

    Kamfanin ya ce dole a ba ma'aikatanta damar shiga wurin nan take, sai dai a yanzu dakarun Rasha ne ke iko da wurin.

  10. Kwana na 19 da fara mamayar Ukraine cikin hotuna

    Bayan kusan mako uku da fara mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine, ana iya ganin yadda yaki ke daidaita wannan makekiyar kasa.

    Fiye da 'yan gudun hijira miliyan biyu da rabi sun tsere daga kasarsu tun bayan da Rasha ta fara mamayarta ranar 24 ga watan Fabrairu, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta sanar.

    Sai dai ana ci gaba da tattanawar neman sasanci tsakanin bangarorin biyu, inda Ukraine ke neman Rasha ta daina bude ma ta wuta.

    Ga hotunan wasu abubuwan da ke faruwa a Ukraine:

  11. Minista ya kira taron gaggawa kan matsalar wutar lantarki a Najeriya

    Ministan harkokin lantarkin Najeriya, Inijiniya Abubakar D. Aliyu ya kira taron gaggawa na masu ruwa-da-tsaki domin samo mafita dangane da matsalar wutar lantarki da ta tsawwala a ‘yan kwanakin nan.

    Taron ya kunshi kamfanonin samar da wutar lantarki da kuma hukumomi na gwamnati da masu zaman kansu da suke da ruwa da tsaki a harkar samar da wutar lantarki da iskar gas.

    A wurin taron, wanda aka gudanar a Abuja, Injiya Abubakar D. Aliyu ya ce gwamnati ba za ta amince ba da yadda lamarin wutar lantarki ya samu koma-baya, yana mai cewa dole a samo mafita ga dukkan matsalolin da suke kawo koma-baya ga yawan wutar lantarki da ‘yan Najeriya suke samu a kullum.

    Ministan ya kuma gargadi hukumomi da kamfanoni na harkar wutar lantarki su guji nunawa juna yatsa, su mayar da hankali wajen tallafawa juna wajen tabbatar da cewa ‘yan Najeriya suna samun isasshiyar wutar lantarki.

    Taron ya mayar da hankali ne ga duba dukkan matsalolin da suke kawo koma-baya ga harkar wutar lantarki a Nijeriya.

    Injiniya Abubakar D. Aliyu ya ce, gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari za ta ci gaba da kokarin daukar matakai domin ganin cewa an samu karuwar wutar lantarkin da ake samarwa a Najeriya.

  12. Rasha na iya karbe ikon manyan biranen Ukraine

    Kakakin Fadar Kremlin ta Rasha Dmitry Peskov ya ce Rasha ta so ta kaucewa asarar rayukan fararen hula da kwace manyan birane kamar Kyiv.

    Amma cikin kalaman da yayi a tashar talabijin ta Rossiya 24, Peskov ya ce mamaye biranen zai haifar da "rasa rayukan fararen hula masu yawa".

    Ya kuma ce jami'an Amurka da Tarayyar Turai na kokari matsa wa Rasha domin ta afka wa manyan biranen Ukraine domin a dora mana alhakin mace-macen fararen hular kasar."

    "A ganinmu wannan matakin ya kasance na tsokanar fada ne."

  13. An hana 'yan Kamaru shan shisha

    Hukumomin Kamaru sun hana 'yan kasar shan shisha, suna cewa hayakin na da hatsari ga lafiyar matasa da ke shan ta a gidajensu da ma a shaguna.

    Kimanin kashi 46 cikin 100 na matasan Kamaru na shan shisha, kamar yadda ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar ke cewa.

    Shisha dai wani hadi ne na taba sigari da wasu sinadarai ciki har da glycerine da kayan kanshi.

    Likitoci na cewa akwai babban kuskure da mutane ke yi cewa shisha ba ya illa kamar taba sigari. Cibiyar binciken cututtukan da suka shafi zuciya ta Birtaniya na cewa shan shisha na sa'a guda daidai yake da shan kara 100 na taba sigari.

    Cibiyar ta British Heart Foundation ta ce, "shisha na dauke da taba sigari, saboda haka kamar taba sigari, shisha na dauke da sinadaran nicotine da na tar da hayakin carbon monoxide da wasu karafa kamar arsenic da lead."

    A 'yan shekarun nan kasashe kamar Tanzaniya da Sudan sun hana shan shisha - duk da yake an rika soke hanin kuma an mayar da shi sau da yawa.

  14. Hoto: Yadda ake tattaunawar sasanci tsakanin Ukraine da Rasha

    Daya daga cikin jami'an kasar Ukraine da ke tattaunawa da takwarorinsu na Rasha - wanda kawo yanzu ake zagaye na hudu - ya shaida wa BBC cewa an fara tattaunawar amma ta intanet ake ganawa maimakon kai tsaye.

    Jami'in mai suna Mykhailo Podolyak ya ce bangarorin biyu sun bayyana wa juna matsayarsu kan yakin da ake gwabzawa.

    Tun da farko ya ce tattaunawar za ta fi mayar da hankali kan tsagaita wuta da kuma janyewar dakarun Rasha, baya ga tabbatar wa Ukraine cewa ba za a sake daukan matakan yaki irin na yanzu a kanta ba.

  15. Indiya za ta sayi man fetur daga Rasha a farashi mai rahusa

    Indiya na duba yiwuwar sayen man fetur da wasu albarkatu daga Rasha a farashi mai rahuwa, inji wani rahoton kamfanin dillancin labarai Reuters.

    Rahoton na cewa wasu jami'ai biyu ne suka sanar da Reuters wannan aniyar ta Indiya.

    Kasar Indiya na sayen kashi 80 cikin 100 na dukkan albarkatun man fetur daga kasashen waje ne, kuma a ciki tana sayen kimanin kashi 2 zuwa kashi 3 cikin 100 na albarkatun man daga Rasha.

    Tana bukatar man na Rasha ne saboda farashin mai na tashin goron zabi a kasuwannin duniya, gwanatin Indiya na bukatar rage yawan kudin da ta ke kashewa kan makamashi.

    Wani jami'in gwamnatin Indiya ya ce kasar na farin cikin sayen man na Rasha kuma ba ta damu da barazanar takunkumi da kasashen yammacin duniya ke yi wa dukkan wadanda suka yi hulda da Rasha ba.

    Jmai'an na Indiya sun kuma ce aiki yayi nisa kan samar da wani tsari na sauya takardun kudin kasashen biyu wato daga Rupee zuwa Rouble.

  16. Kalli yadda uwargidan DCP Abba Kyari ta yanke jiki ta fadi a kotu

    Uwargidan mataimakin kwamishinan 'yan sanda Abba Kyari ta yanke jiki ta fadi a harabar babbar kotun tarayya da ke Abuja.

    Wasu shaidu a kotun sun shaida wa BBC Pidgin cewa matar ta fara numfashi sama-sama ne yayin da ta ke taimaka ma mijin nata taka wa. Wasu 'yan uwanta sun sanar da BBC cewa matar ta sam harin asma ne.

    Uwargidan Abba Kyarin ta halarci zaman kotun ne domin lauyoyin mai gidan nata sun bukaci kotun ta bayar da belinsa, matakin da kotun ta ce sai ranar Litin 28 ga watan Maris za ta yanke hukunci a kai.

    Kuna iya kallon bidiyon yadda lamarin ya auku a nan: https://fb.watch/bKTUCGRsSo/

  17. Kotu ta dage karar da Abba Kyari ya shigar zuwa 28 ga watan Maris

    Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta dage zamanta zuwa Litinin 28 ga watan Maris domin sauraron bukatar da lauyoyin mataimakin kwamishinan 'yan sanda Abba Kyari suka shigar na neman a bayar da belinsa.

    Idan ba a manta ba, hukumar NDLEA ce tagurfanar da dan sandan da wasu mukarrabansa hudu a gaban kotun saboda tuhumar da ake mu su cewa suna safara hodar Ibilis.

    Sauran jami'an 'yan sandan da ake tuhuma da DCP Abba Kyari su hada da ACP Sunday J. Ubia, ASP James Bawa, Sufeto Simon Agirigba, Sufeto John Nuhu.

  18. Harin da Rasha ta kai kusa da kan iyaka sako ne ga NATO - Poland

    Wai harin roka da Rasha ta kai kan wani sansanin sojin Ukraine kusa da kan iyakar kasar da Poland a jiya Lahadi wani kokari ne na razana kungiyart tsaro ta NATO, kmar yada mataimakin ma'aikatar harkokin waje na Poland Marcin Przydacz ya shaida ma BBC.

    Akalla mutum 35 ne suka halaka a sanadin harin da aka kai kan sansanin horar da sojoji na Yavoriv wanda ke da nisan kilomita 20 daga kan iyakar Ukraine da Poland, wadda mamba ce ta kungiyar NATO.

    Przydacz ya shaida wa BBC cewa: "Lallai suna sane cewa wannan sansanin na kusa da kan iyakarmu da Poland ne."

    Ya kuma ce, "Rashawa na son aika wa NATO sako ne a dalilin kai wannan harin... Sna son yi ma NATO gargadi ne."

    Mista Przydacz ya ce yana fargabar abin da ka iya afka ma kasarsa "da ma wasu kasashen tun da Mista Putin na yunkurin lalata wannan duniyar da muke rayuwa cikinta."

  19. Wasu kasashe na son Rasha ta kasa biyan basussukan da ake bin ta - Ministan Kudi

    Minisitan Kudi na Rasha ya tuhumi wasu kasashe, yana cewa da gangar suke son kai kasarsa wani wuri da za ta kasa biyan basussukan da ake bin ta.

    Cikin wata sanarwa minista Anton Siluanov ya ce: "Dode asusun babban bankin Rasha da na gwamnatin Rasha a kasashen waje wata alama ce ta wasu kasashe da ke son kirkirar wani dalili da gangan da zai tilasta ma Rasha gaza sauke nauyi da ke kan ta."

    An dai hana bankunan Rasha masu yawa amfani da tsarin ura kudade na kasa-da-kasa mai suna SWIFT, baya ga wasu jerin takunkumai da aka kakaba ma Rasha bayan mamayar da ta yi ma Ukraine.

  20. An ba 'yan Ukraine biza 3,000 zuwa ranar Asabar - Javid

    Sakataren kiwon lafiya na Birtaniya Sajid Javid ya bayyana a wani shiri talabiji mai suna BBC Breakfast inda yake amsa tambayoyi kan yawan bizar da aka ba 'yan Ukraine masu 'yan uwa a Birtaniya.

    Ya ce zuwa ranar Asabar, alkaluman wadanda aka ba takardun izinin shiga kasar sun kai mutum 3,000, sai dai yana ganin zuwa yau alkaluman sun karu.

    Ya kua ce daga baya Birtaniya za ta fitar da wani shirin, wanda a karkashinsa za a kyale wasu 'ya Ukraine su shiga Birtaniya amma ta hannun daman wasu kungiyoyin agaji.

    Ya ce bayan sun isa kasar, a a mika su ga wasu iyalan da za su ba su masauki.

    Za a kuma ba su izinin zama a kasar na shekara uku sannan za a basu damar yin aiki a kasar.