Putin bai shirya kawo ƙarshen yaƙi ba - Jami'in Faransa
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau
Zelensky ya ce sojojin Ukraine 1,300 aka kashe

Shugaba Volodymyr Zelensky ya cekimamin sojojin Ukraine dubu daya da dari uku ne aka kashe tun farkon mamayar Rasha.
Da ya ke amsa tambayoyi daga wurin 'yan jarida a Kyiv ya ce adadin sojojin Rasha da aka kashe ya zarce na kasarsa inda ya yi kiyasin adadin ya ninka sau 10.
Mr Zelensky ya kuma ce daruruwan sojojin Rasha sun mika wuya.
Sai dai babuwata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da alkalumman
Mutum 60 sun mutu bayan taragon jirgin ƙasa 10 sun abka rami
Jami'ai a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo sun ce aƙalla mutum 60 ne suka mutu a wani hatsarin jirgin kasa a lardin Kolwezi da ke kudu maso gabashin kasar.
Wasu 50 sun samu raunuka bayan da taragon jirgin guda 10 suka abka cikin wani rami.
Ma’aikatan agajin gaggawa suna wurin, suna taimaka wa wadanda suka jikkata.
Jami’ai a yankin sun ce ba a bayar da cikakkiyar kulawa gaayyukan amfanin jama’a yadda ya kamata, kuma irin wannan al’amari dole ya faru babu makawa.
Saudiyya ta hana wa mutumin da aka saki bayan ɗaurin shekaru 10 kan ɓatanci ga addinin Islama fita ƙasar

Asalin hoton, Other
Saudiyya ta tabbatar da sanya dokar hana fita ƙasar ta tsawon shekaru goma kan mai rubutu a intanet Raif Badawi, wanda aka sake shi a ranar Juma'a bayan daurin shekaru goma a gidan yari bisa samunsa da laifin cin zarafin addinin Islama.
Hukuncin da aka yanke masa na asali ya kuma haɗa da haramta tafiye-tafiye na tsawon shekara 10 bayan an sake shi - wanda wani jami'in ma'aikatar harkokin cikin gida ya ce hukuncin na nan zai ci gaba har sai dai idan an yi wa Mista Badawi afuwa
Matarsa da ƴaƴansa uku suna zaune ne a Canada.
Kenyatta ya amince da Raila Odinga a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa

Asalin hoton, Raila Odinga
Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta, ya amince da tsohon abokin hamayyarsa, Raila Odinga, a matsayin ɗan takarar shugaban kasa a zaben bana.
Shugaba mai ci, wanda ba zai iya sake tsayawa takara ba, kasancewar ya riga ya yi wa'adi biyu, ya shaida wa taron dubban jama'a a Nairobi babban birnin kasar cewa, ba ya shakkar cewa Mista Odinga ne jagoran tawagar.
A watan da ya gabata jam'iyyar Jubilee mai mulki ta ƙulla ƙawance ƙarƙashin jagorancin Mr Odinga.
A shekarar 2018 Mr Kenyatta da Mr Odinga suka ayyana zaman lafiya bayan ƙazamin tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban ƙasa.
Sun kasance abokan hamayyar siyasa tsawon shekaru da dama.
Saudiyya ta zartar wa mutum 81 hukuncin kisa a rana ɗaya
Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa kan mutum 81 a rana ɗaya bayan samunsu da laifukan da suka shafi ta’addanci, kamar yadda kamfanin dillacin labaran ƙasar SPA ya ruwaito.
Wannan ya zarta adadin mutanen da aka zartarwa hukuncin kisa a bara.
Mutanen sun haɗa da waɗanda aka samu da laifin suna da alaƙa da Al Qaeda da IS da kuma mayaƙan Houthi da ke yaƙi a Yemen.
Waɗanda aka kashe suna shirin kai hare-hare a Saudiyya – da koƙarin kashe fararen hula da jami’an tsaro, kamar yadda kamfanin dillacin labaran Saudiyya SPA ya ruwaito.
Mutum 73 daga cikin 81 ƴan asalin Saudiyya ne, bakwai kuma ƴan Yemen da kuma mutum daya ɗan ƙasar Syria.

Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Irin wannan matakin ya haifar da zanga-zanga a Amurka shekaru uku da suka gabata Putin bai shirya kawo ƙarshen yaƙi ba - Jami'in Faransa

Asalin hoton, EPA
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya buƙaci shugaba Putin na Rasha ya kawo ƙarshen yaƙi a tattaunawar da suka yi ta wayar tarho tsakaninsu tare da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Schulz.
Amma wani jami'in fadar Faransa wanda kamfanin dillancin labaran Reuters ya ambato ya ce da alama Putin bai shirya kawo karshen yakin ba.
Ƙasashen na Turai guda biyu sun sake nanata kiran tsagaita wuta a matsayin sharaɗin tattaunawa.
Shugaban Faransa kuma ya zargi Putin da "ƙarya" bayan ya ce sojojin Ukraine da alhakin keta haƙƙin ɗan adam, kamar yadda kamfanin dillacin labaran AFP ya ruwaito.
Amurka ta saka wa 'yan Rasha takunkumi kan taimaka wa nukiliyar Koriya ta Arewa
Amuka ta sanya takunkumi kan kamfanoni uku na Rasha da wasu 'yan kasuwa biyu da take zargi da taimakon Koriya ta Arewa sake inganta makaman nukiliyarta.
Matakin na zuwa ne kwana ɗaya bayan Amurkar da Koriya ta Kudu sun sanar da cewa Arewa ta yi gwajin makami mai linzami wanda ya saba haramcin da Majalisar Dinkin Duniya ta sanya mata.
Hukumomin Amurka sun ce 'yan tsirarun kamfanoni da 'yan kasuwar da ke taimakon Koriya ta Arewa da suka fito daga birnin Vladivostok na kasar Rasha suna da makudan kudade.
Gwamnatin Shugaba Biden ta kira gwajin a matsayin tsantsar takalar fada da rashin son zaman lafiya, yayin da Pyongyang ta ce gwajin wani bangare ne na inganta tauraron dan Adam na leken asiri.
Saudiyya ta kashe mutum 81 da kotu ta yanke wa hukuncin kisa

Asalin hoton, Getty Images
Saudiyya ta sanar da cewa ta ƙaddamar da hukuncin kisa a kan mutum 81 da kotu ta yanke wa hukunci kan laifuka da suka shafi ta'addanci da fyaɗe da kisa, kamar yadda kamfanin labarai na ƙasar SPA ya ruwaito.
Wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin cikin gida ta ce daga cikin mutanen akwai mambobin ƙungiyar ISIS da Al-Qaeda da Houthi.
"Mutanen da suka kai 81, an yanke musu hukunci ne kan laifuka daban-daban, ciki har da kashe mutane maza da mata da yara ƙanana," in ji sanawar.
"Laifukan sun haɗa da shiga ƙungiyoyin ta'adddanci na ƙasashen waje kamar ISIS da Al-Qaeda da Huothi da ke kai hare-hare a cikin ƙasa (Saudiyya) da kuma zuwa wuraren rikici don taya ƙungiyoyin ta'addanci yaƙi."
Ta ƙara da cewa an kama mutanen ne sannan aka yi musu shari'a a Saudiyya ƙarƙashin jagorancin alƙalai 13 a mataki uku daban-daban na shari'a kan kowane ɗayansu.
An dakatar da Abramovich a matsayin daraktan Chelsea

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar da ke kula da gasar ƙwallon ƙafa ta Premier League a Ingila ta dakatar da Roman Abramovich a matsayin babban daraktan ƙungiyar Chelesea.
Hukumar ta ɗauki matakin ne bayan gwamnatin Birtaniya ta saka masa takunkumi a matsayin martani ga ƙasarsa Rasha game da mamayar da take yi a Ukraine.
An bai wa kulob ɗin dama ta musamman don ci gaba da buga wasanni duk da takunkumin da aka saka wa Abramovich.
Sai dai ta ce dakatarwar da aka yi wa attajirin ba za ta hana Chelsea atasaye ba ko kuma buga wasanni.
Rasha ta yi iƙirarin harbe jiragen Ukraine biyar
Ma'aikatar Tsaro ta Rasha ta faɗa a yau Asabar cewa ta kai wa wata tashar sojojin sama ta Ukraine hari a Vasylkiv da kuma wata cibiyar sadarwa da ke Brovary da makamai masu linzami.
Dukkan wuraren na kusa da Kyiv babban birnin Ukraine, kamar yadda kamfanin labarai na Anadolu ya ruwaito.
Sai dai BBC ba ta iya tabbatar da faruwar hakan ba ko kuma tasirin da harin ya yi.
"Da safiyar 12 ga watan Maris, an kai wani hari da makamai masu linzami masu dogon zango kan kayayyakin soja a Ukraine," in ji mai magana da yawun ma'aikatar mai suna Igor Konashenkov yayin taron manema labarai a Moscow.
"An lalata tashar sojan sama ta Vasylkiv da kuma tashar sadarwa ta sojojin Ukraine da ke Brovary."
Ya ƙara da cewa makaman tsaron sama na Rashar sun kakkaɓo jirage marasa matuƙa na Ukraine biyar.
Ba gwamnoni ne suka hana ruwa gudu a APC ba - Gwamnan Jigawa

Shirinmu na Gane Mani Hanya na makon nan ya tattauna da Gwamna Mohammed Badaru Abubakar na Jihar Jigawa a arewacin Najeriya kan halin da jam'iyyar APC ke ciki.
A Najeriya a yayin da jam’iyyar APC mai mulkin kasar ke shirin gudanar da babban taronta a karshen wannan watan, wani jigo a jam’iyyar ya ce ba suda wani zabi illa bin dan takarar da shugaba Muhammadu Buhari ya ke goyon baya.
Gwamnan jihar Jigawa, Muhammadu Badaru Abubakar ya ce babu gaskiya a zargin da ake musu ne cewa wasu daga cikin gwamnonin arewa sun yi kane-kane sun hana ruwa gudu a jam’iyyar ta APC.
A tattaunawa da Editan BBC Hausa Aliyu Abdullahi Tanko, gwamnan ya soma ne da bugun kirji cewa jam’iyyar APC ta taka rawar gani tsawon lokacin da ta shafe a kan mulkin.
Sai dai mun naɗi wannan hirar kafin sabuwar ɓarakar da ta kunno kai a APC a farkon wannan makon.
Rasha ta tsaurara hare-hare a wajen birnin Kyiv

Asalin hoton, Getty Images
Kamar yadda muka ruwaito muku cewa dakarun Rasha na ƙoƙarin yi wa birnin Kyiv zobe, yanzu kuma mun fahimci cewa sun zafafa kai hare-hare a zagyen birnin.
Kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito gwamnan Kyiv da na yankin Donetsk na cewa hare-hare sun tsananta a wuraren da ake sa ran za a tsagaita wuta don bai wa fararen hula damar tserewa.
Tuni aka tsara cewa Rasha za ta tsagaita wuta a garuruwan da suke hannunta, ciki har da Mariupol da ke Donetsk.
"Jirgin dakon kaya yana kan hanyar zuwa Mariupol yanzu, za mu ba ku bayanin abin da ke faruwa...Lamarin ba mai sauƙi ba ne, ana ta ci gaba da luguden wuta," in ji Gwamnan Donetsk Pavlo Kyrylenko cikin hirarsa da wata kafar labarai ta Ukraine.
Tattaunawa da ma'abota BBC Hausa
Shirin Ra'ayi Riga da muke kawo muku ta rediyo duk ranar Juma'a na wannan makon ya bai wa masu sauraronmu dama ne don su bayyana irin soyayyarsu ga BBC Hausa yayin da muke cika shekara 65 da fara yaɗa shirye-shiye.
Kuna iya sauraron shirin idan kuka latsa hoton ƙasa:
Bayanan sautiTattaunawa da ma'abota sauraron BBC Hausa 'Yan gudun hijirar Ukraine fiye da miliyan 2.5 ne suka tsere

Asalin hoton, Getty Images
'Yan Ukraine sama da miliyan biyu da rabi ne suka yi gudun hijira domin tsere wa yakin da ake yi akasar.
Moldova ta ce duk yara kananan da ake gani a iyakokinta 'yan gudun hijira ne, sannan a kowacce rana 'yan Ukraine na kara kwarara kasar.
'Yan gudun hijira fiye da 100,000 ne suka shiga Moldova, abin da ya kara kashi 4 cikin 100 na adadin 'yan kasar.
Ministan harkokin wajen Moldova, Nicu Popescu, ya shaida wa BBC cewa kasar ba ta da karfin arzikin da za ta dauki dawainiyar 'yan gudun hijirar makociyar tasu.
Kuma tuni suka fara karaya, sakamakon harin da Rasha ta kai birnin Odesa mai nisan mil 30 da iyakarsu, wanda ka iya sanya mazauna yankin kwararowa cikin gari domin neman mafaka.
'Yan fashi sun sace mata da ƙananan yara a Zamfara tare da ƙona gidaje

Asalin hoton, Daily Trust
Wasu 'yan bindiga da ake zaton 'yan fashin daji ne sun sace mata da ƙananan yara tare da ƙona gidaje da dama a garin Yar Katsina na Jihar Zamfara.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC Hausa cewa maharan sun afka wa garin ne da ke cikin Ƙaramar Hukumar Bungudu da misalin ƙarfe 1:00 na ranar Laraba, inda suka harbi mutane da dama.
Sadik Abdullahi "Yar Katsina ya ce mutum ɗaya ya mutu sannan an kai uku asibiti sakamakon raunukan da suka ji daga harbe-harben.
Haka nan 'yan bindigar sun tafi da mata da ƙananan yara kusan 15 bayan harin.
"Yanzu haka mutum kusan 3,000 sun tsere daga garin zuwa maƙota kamar garin Gusau da Wanke da Bungudu," in ji Sadik.
Rundunar sojan Najeriya ta ce ta kashe 'yan fashin dajin da take kira 'yan ta'adda kusan 100 a yankin arewa maso yammacin ƙasar cikin mako biyu da suka gabata.
Sai dai duk da nasarar da jami'an tsaron ke cewa suna samu, har yanzu 'yan bindigar na ci gaba da karkashe mazaiuna ƙauyuka kusan a kullum.
Muhimmancin hutu a rayuwar mata
Bayanan sautiKu latsa hoton sama don sauraron shirin Mace tana bukatar ta samu lokaci na musamman da zata dinga hutawa saboda muhimmancin hakan ga lafiyarta.
Likitoci sun bayyana wasu hanyoyi wadanda mata za su dinga bi wajen kaucewa matukar gajiya a yayin ayyukansu na yau da kullum.
Sun kuma jaddada muhimmancin cewa mace ta fara kulawa da kanta domin ta yin haka ne za ta samu kuzari da walwala da koshin lafiyar kulawa da iyali da sauran wadanda ke da nauyi a kanta.
Wasu daga cikin hanyoyin sun hada da yin kebe lokaci na musamman na hutawa. Haka zalika tsara yadda mace za ta yi ayyukanta zai taimaka wajen yin ayyuka masu ma'ana.
Ukraine ta ce Rasha ta kai hari kan asibitin kula da cutar kansa
Wani jami'in lafiya a Ukraine ya ce sojojin Rasha sun yi wa wani asibiti luguden wuta a birnin Mykolayiv.
Maksym Beznosenko wanda shi ne shugaban hukumar lafiya na yankin, ya ce asibitin na kula da masu cutar daji ne wato kansa.
"Azzalumi ne kaɗai zai kai wa maras ƙarfi hari. Waɗan nan marasa ƙarfin marasa lafiyarmu ne. Yanzun nan waɗan nan azzaluman suka kai wa asibitin cutar kansa hari wanda ke kula da mutane a baki ɗayan yankin Mykolayiv," a cewarsa cikin wani saƙo a Facebook.
"Da a ce tsanar abokin gaba za ta haɗa kan al'umma, da mu ne ƙasa mafi haɗin kai a duniya. Idan Rasha tana kallon marasa lafiya a matsayin abokan gabarta ba marasa lafiya ba, to abin da zai ci gaba da ƙarfafa mana gwiwa ke nan."
Saura kilomita 25 dakarun Rasha su shiga tsakiyar Kyiv - Birtaniya

Asalin hoton, Maxer
Bayanan hoto, Bataliyar sojojin Rasha mai tsawon kusan kilomita 64 a Ukraine Cikin bayanan da ta saba fitarwa, Ma'aikatar Tsaro ta Birtaniya ta ce "dandazo" dakarun Rasha na gab da shiga Kyiv babban birnin Ukraine, inda ya rage musu kilomita 25 kacal.
Ta ce bataliyar da ke arewacin birnin ya rarrabu - "babu mamaki don su taimaka wajen zagaye birnin".
"Babu mamaki kuma Rasha ta yi haka ne don ta rage haɗarin kai wa sojojinta hari daga dakarun Ukraine, waɗanda har yanzu suke ƙara nuna turjiya," a cewar ma'aikatar.
A gefe guda kuma, garuruwan Chernihiv, da Kharkiv, da Mariupol a zagaye suke sannan kuma suna ci gaba da fuskantar luguden wuta daga dakarun Rasha.
Kauce wa XYa kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Hare-haren Rasha sun hana farar hula da ke son guduwa ficewa daga Mariupol - Ukraine
Gwamnatin Ukraine ta ce hare-haren Rasha sun kara janyo farar hula da ke son ficewa daga kudancin birnin Mariupol, mai tashar ruwa, sun gagara ficewa alhalin suna cikin mawuyacin hali.
Hukumomi sun ce kawo yanzu sama da mutum 1,500 aka kashe a Mariupol, wadanda suke raye kuma suna fama da matsanancin sanyi, babu wutar lantarki sannan abinci da ruwan da suke da shi ya kusa karewa.
A jawabin da ya saba yi wa 'yan kasar, Shugaba Zelensky ya yi Allah-wadai da matakin Rasha na hana farar hula ficewa, da hana kai kayan agaji ga mutanen ke tsananin bukata.
