Muhimman abubuwan da suka faru kawo yanzu tsakanin Rasha da Ukraine
Ga wadanda yanzu suka fara bibiyar mu, ga wssu cikin muhimman abubuwa da suka auku kan yakin da ake gwabzawa tsakanin Rasha da Ukraine:
- Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya musanta ikirarin da Rasha ke yi cewa ana hada makamai na guba da na kisan kiyashi a Ukraine.
- Rasha ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta gana a yau Juma'a domin duba wannan ikirarin na Rasha
- Hotunan da aka dauka daga tauraron dan Adam na nuna sojojin Rasha na matsawa sannu a hankali, kuma suna kara kusantar birnin Kyiv
- Dakarun Rasha na kuma yi wa wasu biranen Ukraine kawanya, inda ma'aikatan agaji ke cewa matakan za su hana shiga da abinci cikin biranen kamar yadda lamarin yake a birnin Mariupol
- A karon farko, tattaunawar da Rasha da Ukraine suka yi a Turkiyya ta kare ba are da yarjejniya ba, sai dai ministocin harkokin wajen kasashen sun ce ba su ga wata hanyar kawo karshen rikicin ba nan kusa
- Kamfanoni masu yawa daga yammacin Turai sun yanke huldar kasuwanci da Rasha ciki har da Western Union, JPMorgan Chase da Warner Music a ranar Alhamis