Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Shugabannin Turai za su sasanta Rasha da Ukraine

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Sani Aliyu and Umar Mikail

  1. Sai da safenku

    Nan muke kawo ƙarshen rahotannin. Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.

  2. Youtube zai toshe tashoshin labarai na Rasha

    Dandalin sada zumunta na Youtube ya sanar da cewa zai toshe tashoshi na kafofin yaɗa labarai da ke da alaƙa da gwamnatin Rasha.

    Dandalin wanda ake saka bidiyo da fina-finai ya ce dokokinsa sun ƙunshi cewa ba za a dinga ƙaryata ko ƙanƙantar da wani abu da ya faru a tarihi ba.

    Ya ce mamayar da Rasha ke yi a Ukraine ta faɗa cikin wannan rukunin, kuma za a rufe tashoshin ciki har da RT da Sputnik.

    "Dokokinmu na amfani sun haramta ƙaryatawa, ko ƙanƙanta wani lamari na tashin hankali da ya faru a tarihi wanda kuma ake da hujja mai ƙarfi, kuma za mu cire abubuwan da suka shafi hare-haren Rasha a Ukraine da suka saɓa doka," a cewar mai magana da yawunsa Farshad Shadloo.

  3. Dubun dubatar mutane ne za su yi aikin Hajji na bana - Saudiyya

    Hukumomi a Saudiyya sun ce dubun dubatar masu ibada ne za su gudanar da aikin Hajji na bana, saɓanin adadi ƙalilan da suka yi aikin na 2020 da 2021.

    Kafar yaɗa labarai ta Haramain Sharifain ta ambato mai magana da yawun ma'aikatar aikin Hajji yana cewa "Hajjin bana zai kasance na adadi mai yawa".

    Ci gaban na zuwa ne 'yan kwanaki da Saudiyya ta cire dukkan dokokin kariya daga kamuwa da cutar korona, ciki har da ɗage wajabcin saka takunkumi a bainar jama'a.

    Mutum 60,000 ne kacal suka gudanar da ibadar a shekarar 2021, yayin da ba su wuce 1,000 ba a 2020 sakamakon annobar korona da ta ɗaiɗaita harkoki a duniya.

  4. Abu biyar da muka koya shekara biyu bayan ayyana korona a matsayin annoba

    Shekaru biyu ke nan tun bayan da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ayyana cutar korona a matsayin annoba a hukumance.

    Tun daga wannan rana ta 11 ga watan Maris din shekarar 2020 duniya ta sauya cikin sauri - daga yanayin yadda muke aiki zuwa hanyoyin kiwon lafiyar da muke da su.

    Ga abubuwa biyar da muka koya tun bayan barkewar annobar:

    • Abu biyar da muka koya shekara biyu bayan ayyana korona a matsayin annoba
  5. Indiya ta yi kuskuren harba makami mai linzami cikin Pakistan

    Indiya ta ce ta harba makami mai linzami cikin kuskure zuwa Pakistan ranar Laraba, inda ta ɗora alhakin abin kan "matsalar na'ura" yayin aikin duba makaman.

    Indiya ta ce ta yi nadama sannan ta nuna jin daɗinta da "ba a kashe kowa ba".

    Rundunar sojan Pakistan ta ce "wani abu mai ɗan karen gudu" ya faɗo a kusa da birnin Mian Channu kuma hanyar da ya bi ta tsorata jiragen fasinja.

    Dukkan ƙasashen na da makamin nukilya.

    Pakistan ta gargaɗi maƙociyar tata da ta kiyaye sake afkuwar hakan.

    An harba makamin ne daga tashar Sirsa da ke jihar Haryana, a cewar wata sanarwa daga ma'aikatar tsaro ta Indiya.

  6. Rasha za ta toshe dandalin Instagram

    Rasha ta tabbatar da cewa za ta toshe dandalin Instagram.

    Lamarin na zuwa bayan kamfanin da ya mallaki Instagram, Meta, ya sauya dokokinsa a wasu ƙasashe don ba su damar jawo wa Shugaban Rasha Vladmir Putin bala'i da sojojinsa, amma ban da 'yan ƙasar.

    Hukumar kula da kafofin yaɗa labarai ta ƙasar ta ce dandalin na sada zumunta yana yaɗa wasu bayanai da ke kiran a afka wa 'yan ƙasar ta Rasha.

    Sai dai ya zuwa yanzu babu tabbas ko za a toshe dandalin ne kwatakwata ko kuma taƙaita wa mutane shiga.

    Da ma tuni aka taƙaita wa mutane shiga Facebook, mallakar Meta, da kuma Twitter.

  7. Labarai da dumi-dumi, Rasha ta yi iƙirarin gano hujjar makamai masu guba a Ukraine

    Jekadan Rasha a Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ya yi iƙirarin cewa dakarunsu sun samu hujjojin da ke nuna sojojin Ukraine sun yi yunƙurin goge hujjar da ta tabbatar da cewa akwai makamai masu guba a Ukraine ɗin.

    Da yake magana a taron Zauren Tsaro na MDD da Rasha ta kira, Vasily Nebenzya ya yi iƙirarin cewa sojojin Rasha sun gano wani ƙunshi na makamai aƙalla 30 masu guba da ake bincike a kai da zimmar haɓaka makaman don yaɗa cutuka.

    Ya ce "akwai bincike masu haɗari sosai" da aka yi a wasu wurare tare da haɗin gwiwar Amurka.

    Nebenzya bai gabatar da wata hujja ba game da iƙirarin nasa, yayin da shugabar sashen hana mallakar makamai ta MDD, Izumi Nakamitsu, ta ce hukumarta ba ta da masaniya game da abin da yake magana a kai.

  8. Shugabannin Turai za su sasanta Rasha da Ukraine

    Shugabannin ƙungiyar Tarayyar Turai ta EU za su yi yunƙurin sasanta rikicin da ke faruwa a Ukraine, ciki har da tsagaita wuta, a cewar Firaministan Hungary Viktor Orban a yau Juma'a a Faransa.

    Kamfanin labarai na Rasha Tass ya ruwaito shi yana cewa "kar a tsammaci za a daina fafatawa a Ukraine". Ya ƙara da cewa "mun yanke shawarar cewa Turawa za su shiga tattaunawar tsagaita wuta".

    Kalaman na Mista Orban na zuwa ne jim kaɗan bayan kammala taron EU na farko tun bayan fara kai hare-haren a Ukraine, wanda suka yi a Versailles.

    "Muna godiya ga duka shugaban Faransa da na Jamus bisa yunƙurinsu na dawo da zaman lafiya a Ukraine," in ji shi.

    A 'yan kwanakin da suka wuce Shugaban Rasha Vladmir Putin ya tattauna ta waya da shugaban Faransa Emmanuel Macron da na Jamus Olaf Scholz.

    Shugabannin na EU sun tattauna kan halin da ake ciki a Ukraine.

  9. 'Yan tawayen a Ukraine sun kama garin Volnovakha, in ji Rasha

    Ma’aikatar harkokin wajen Rasah ta ce dakarun ‘yan aware na lardin Donesk da ya ayyana 'yancin kansa sun kama garin Volnovakha da ke tsakanin Donesk din da kuma birnin Mariupol da aka yiwa kawanya.

    Wata 'yar jarida a birnin ta bayyana cewa @an kai hare-hare har ta sama har uku da fashewar abubuwa miniti 13 daga inda nake tsaye kuma jami'an kashe gobara na ta kokari wajen kashe wutar wajen".

    Mutum ɗaya ya mutu nan take, akwai kuma hari ta sama da ya fada a wata makarantar yara.

    Mai Magana da yawun rundunar, Igor Konashenkov, ya bayyana a kafar talbijin din kasar cewa dakarun ‘yan awaren sun yi wa Mariupol kofar rago.

  10. Ukraine na ikirarin ta kashe wani babban hafsan sojojin Rasha

    Rundunar sojin Ukraine ta ce dakarun Ukraine sun kashe wani babban janar na Rasha.

    Manjo Janar Kolesnikov shi ne kwamandan gunduma ta 29 ta rundunar sojin Rasha da ke gabashin kasar, kamar yadda Anton Gerashchenko, mai ba shugaba kasar Ukraine shawara ya sanar.

    Sai dai babu cikakken bayani kan yadda ya mutu kuma Rasha ba ta ce komai ba.

    Akalla manyan hafsoshi biyu rahotanni ke cewa an kashe tun bayan da yakin ya barke mako biyu da ya gabata.

  11. Rasha na duba yiwuwar dakatar da Facebook da Instagram a cikin kasar

    Ofishin babban mai shigar da kara na Rasha ya nemi a ba shi izinin ayyana Meta, kamfanin da ya mallaki Facebook da Instagram - a matsayin "kungiya mai tsattsauran ra'ayi" kuma ya hana shi yin aiki a Rasha, kamar yadda kafofin yada labaran Rasha suka ruwaito.

    Ofishin ya kuma bayar da shawarar a rage karsashin Instagram a cikin kasar.

    Wannan matakin ya biyo bayan sanarwar da kamfanin na Meta ya fitar ne cewa zai kyale masu amfani da shafinsa a wasu kasashe su yi kraye-kirayen a kashe shugaban Rasha da dakarunta.

    Ofishin mai shigar da karan ya ce yana tuhumar Meta da "cusa kiyayya a zukatan mutane da kuma yin kira ga wasu su dauki matakai da za su iya illata jama'a".

    Tun makon jiya Rasha ta fara hana al'ummar kasar shiga shafukan sada zumunta na Facebook da Twitter a cikin kasar.

  12. Korona: Kenya ta daina tilasta wa 'yan kasarta sanya takunkumi da killace kansu

    Ma'aikatar lafiya ta Kenya ta sanar cewa ba za ta sake bukatar 'yan kasar su rika sanya takunkumi a wuraren da jama'a ke taruwa ba.

    Sai dai za a ci gaba da kira ga mutane su rika bayar da tazara da tsafatace hannayensu domin rage yaduwar cutar korona.

    Gwamnatin kasar ta kuma daina tilasta ma mutane killace kansu ko da kuwa suna dauke da kwayar cutar.

    Minista lafiya na kasar Mutahi Kagwe ya ce tarurruka a wuraren ibada kamar coci-coci da masallatai na iya ci gaba kamar yadda aka saba gabanin bayyanar cutar ta korona.

    Mutum fiye da miliyan bakwai ne aa yi wa alluran riga-kafin cutar korona a kasar, adanda yawansu bai wuce kashi 28.5 na al'ummar kasar balagaggu ba.

    A shekaar 2020 ne Kenya ta fara tilasta ma 'yan kasar sanya takunkumi, a lokaci annobar korona na kara yaduwa.

  13. Putin: An samu ci gaba a 'tattaunawarmu da Ukraine'

    Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce an sami wasu abubuwan ci gaba bayan tattaunawar da jami'an Rasha ke yi da na Ukraine.

    "Akwai wasu abbuwan karfafa gwuiwa da suka faru, kamar yadda jami'ai daga bangarenmu suka sanar da ni", inji Shugaba Putin yayin da yake ganawa da Shugaba Alexander Lukashenko na Belarus yayin wata ganawa da suka yi a birnin Moscow.

    Kawo yanzu bangaroroin biyu sun gana sau uku a kan iyakar Ukraine da Belarus kuma ranar Alhamis ministocin harkokin wajen kasashen biyu sun gana kai tsaye a Tukiyya.

    Sai dai har yanzu babu wani kwakkwaran ci gaba da aka samu.

    Mista Putin ya tabo batun takunkuman da kasashen yammacin Turai suka kakaba ma Rasha, yana cewa al'amarin na iya zama alheri ga kasarsa:

    "Wannan lokaci ne da ya ba mu damar karfafa tattalin arzikinmu da 'yancinmu a fannin fasaha."

  14. Tun bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, kamfanonin kasashen yamma da dama kamar Apple da Disney da kuma Netflix sun daina kasuwanci a Rasha.

    Wasu kamar babban kamfanin man fetur na Shell sun sanar da za su fice da ga kasar a hankali a hankali, yana ba da misali da ƙalubalen da ayyukansa ke fuskanta a Rasha ta fuskar tattalin arziki.

    Kuma waɗanda suka iirn su McDonald's da Coca-Cola suna fuskantar kiraye-kirayen ficewa daga Rashar a matsayin martani ga mamayar da Shugaba Putin ya yi wa makwabciyarsa Ukraine.

    To su waye suka tafi kuma su waye suka tsaya?

  15. Hotuna: Najeriya ta kwaso wasu karin 'yan kasarta da yakin Ukraine ya shafa

    Karin 'yan Najeriya su 122 da suka tsere daga yakin da ake gwabzawa a kasar Ukraine sun isa Abuja da sanyin safiyar yau Juma'a.

    Kawo yanzu, Najeriya ta kwaso 'yan kasarta 1,076 ciki har da dalibai daga kasar ta Ukraine.

    Gwamnatin Najeriya ta kuma ware wasu kudade domin tallafa wa 'yan kasar su kimanin 5,000 da rikicin na Ukraine ya shafa.

    Ga wasu hotunan 'yan Najeriyan yayin da suke sauka a babban filin jirgin saman Abuja:

  16. Putin zai tura mayaka 16,000 daga Gabas ta Tsakiya zuwa Ukraine

    Muna samun rahotanni cewa Shugaban Rasha Vladimir Putin ya amince da wani shiri na tura mayaka 'yan sa kai zuwa Ukraine.

    Putin na magana ne yayin wani taro na kwamitin tsaro na kasar, inda yake cewa za a yi maraba da dukkan mayaka 'yan sa kai da ke sha'awar taimaka ma sojojin da Rasha ke mara ma baya.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters na cewa ministan tsaro na Rasha Sergei Shoigu ya ce akwai mayaka 'yan sa kai 16,000 daga Gabas ta tsakiya da ke son shiga yakin domi taimaka ma dakarun da Rashar ke mara ma baya a Ukraine.

  17. Yakin Ukraine: Facebook zai kyale masu amfani da shafin su yi kiran 'a kashe Putin'

    Kamfanin Meta wanda ya mallaki dandalin sada zumunta na Facebook da Instagram zai kyale wasu masu amfani da kafofin sadarwan a wasu kasashe su yi kiraye-kirayen daukar matakan raunata Shugaban Rasha Vladimir Putin.

    Meta ya ce ya shirya kyale wasu kalaman batanci da na tayar da hankali kamar "a kashe Rashawa masu mamaya", wadanda a zahiri sun taka tsarin aikinsu.

    Sai dai kamfanin ya ce ba zai bari a rika kiraye-kirayen illata fararen hula 'yan Rasha ba.

    A martanin da ta mayar, Rasha ta bukaci Amurka ta taka ma kamfanin birki kan abin da ta kira "matakan cin zarafi" da ya ke son dauka kan Rashar.

    Wannan matakin ya biyo bayan wasikun imel da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce ya gani da ke bayyana wannan aniyar ta kamfanin Meta.

    A karkashin sabon tsarin, masu amfani da shafukan Facebook da Instagram a rasha da Ukraine da Poland na iya yin kiran a kashe Shugabn Rasha Vladimir Putin da Shugaba Lukashenko na Belarus.

  18. Rasha na son kwace kadarorin kamfanonin Turai da suka fice saboda yakin Ukraine - Amurka

    Fadar Shugaban Amurka ta yi tsokaci kan rahoton da ya bayana cikin sa'a 24 da suka gabata cewa Rasha na iya kwace dukkan kadarorin kamfanonin kasashen yammacin Turai dasuka fice daga kasar kan yakin Ukraine.

    kakakin fadar White House Jen Psaki ta gargadi Rasha a cikin wani jerin sakonnin Twitter cewa "wannan matakin da ba na doka ne ba" na iya yi ma Rasha illa nan gaba.

    Ana samun karin kamfanonin da ke ficewa daga Rasha, ciki har da McDonalds, Western Union, Goldman Sachs, JPMorgan Chase da Warner Music.

    Dukkan wadannan kamfanonin na da shaguna da gine-gine da masana'antu da suka mallaka acikin Rasha - kuma Rasha na iya kwace su baki daya idan rahoton ya zama gaskiya.

  19. Koriya ta ce tana gwajin makamai ne don sa ido kan ayyukan sojin Amurka a yankin

    Jami'ai a Amurka da Koriya Ta Kudu sun yi gargaɗin cewa Koriya Ta Arewa na ta gwajin makamai masu dogon zango da ke da ƙarfin gaske abin da gwamnatin Biden ta kira babban lamari.

    Sai dai Koriya Ta Arewa ta ce gwaje-gwaje biyu na baya-bayan nan da ta yi duka ta yi su ne domin samar da wani sabon tauraron ɗan adam mai leƙen asiri.

    Ta ce tauraron zai rinƙa sa ido kan ayyukan da sojojin Amurka ke yi a yankin.

    Amurka da Japan duka sun ce za su soma tunanin maka wa Koriya Ta Arewa sabbin takunkumai.

  20. Hotunan yadda aka tashi a birnin Kyiv na Ukraine a safiyar yau

    Babban birnin kasar Ukraine da yankunan da ke wajensa na ci gaba da shan luguden wuta daga hare-haren da Rasha ke kai wa birnin.

    Mazauna birnin masu yawa sun tsere zuwa yammaci domin kaucewa hare-haren.

    ga wasu hotunan halin da ake ciki a makon nan a birnin Kyiv: