Sojojin Najeriya sun ce sun kashe 'ƴan ta'adda' 100 a arewacin ƙasar

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Sani Aliyu and Umar Mikail

  1. Labaran duniya cikin minti daya da BBC Hausa

    Ku saurari labaran duniya cikin minti daya da BBC Hausa wanda Mustapha Kaita da Annur Muhammad suka karanta.

    Ku latsa hoton kasa don sauraro.

    Bayanan sautiMinti Daya da BBC Hausa Na Safe 10/03/2022
  2. Fadar White House: Rasha na iya kai harin guba kan Ukraine

    Russia has been shelling Ukrainian cities, including Irpin, near the capital Kyiv

    Asalin hoton, SOPA IMAGES/GETTY IMAGES

    Fadar Shugaban Amurka ta ce akwai yiwuwar Rasha na shirin ta kai hari na guba kan kasar Ukraine - kuma "ya kamata mu sa ido".

    Kakakin Fadar White House Jen Psaki ta ce ikirarin da Rasha ke yi cewa ta damu da wasu dakunan bincike na Amurka da ke cikin Ukraine abubuwa ne masu daure kai.

    Amurka ta kuma ce ta "damu matuka" cewa yakin na iya ci gaba da rincabewa, musamman a bangaren amfani da sinadarai na guba da bama-bamai masu guba.

    Wani jami'in gwamanti a Turai ya ce, "Muna da dalilai da suka sa muka damu".

    Gwamnatocin yaamcin Turai sun ce damuwarsu ta biyo bayan yadda Rasha ta rika amfani da sinadarai da bama-bamai masu guba yayin da ta mamaye wasu yankuna a baya.

    Ms Psaki ta kuma ce, "Tilas mu sa ido kan matakan da Rasha ke dauka domin tana iya amfani da wadannan makaman a Ukraine, makaman da aka haramta amfani da su."

  3. Muna muku lale marhabin masu bibiyar Sashen Hausa na BBC.

    BBC Bureau Lagos Nigeria

    A yau ma BBC za ta ci gaba da kawo muku yadda ta ke kasancewa a fagen dagar yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine tun daga ranar Alhamis, 24 ga watan Fabrairu zuwa yau.

    Suna na Sani Aliyu, kuma ni ne zan jagoranci gabatar muku da labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa kai-tsaye daga nan BBC Hausa.

    Za mu kuma kawo muku muhimman labarai daga wasu sassa na Najeriya da wasu kasashen Afirka da ma na duniya.