Mu kwana lafiya
Mun kawo ƙarshen rahotannin a wannan shafin.
Mu haɗu da ku gobe idan Allah ya kai mu. Umar Mikail ke muku fatan alheri.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.
Sani Aliyu and Umar Mikail
Mun kawo ƙarshen rahotannin a wannan shafin.
Mu haɗu da ku gobe idan Allah ya kai mu. Umar Mikail ke muku fatan alheri.
Ukraine da Rasha sun gaza cimma matsaya kan batun tsagaita wuta domin ba wa mutanen da suka makale a rikicin Ukraine damar ficewa a wata tattaunawa da jami’an kasashen suka yi tun bayan da Rasha ta fara mamaya.
Dukkan ɓangarorin sun nuna bayar da damar ci gaba da tattaunawa.
Amma ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov bai ce komai ba kan hakan sannan kuma ya yi watsi da Allah-wadai da kasashen duniya suka yi kan harin da aka kai kan wani asibiti a Mariupol.
Shi kuwa takwaransa na Ukraine, Dmytro Kuleba, ya bayyana tattaunawar a matsayin mai tsaurin gaske, sannan ya ce Mista Lavrov ya yi watsi da bukatarsa ta tsagaita wuta na tsawon sa’oi 12 don ba wa fararen hula damar ficewa daga inda suka makale.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Rasha ta sanar da jerin kayayyaki fiye da 200 da ta hana shiga da su ƙasar daga ƙasashen waje.
Kayayyakin sun ƙunshi na sadarwa da harkokin lafiya, da ababen hawa, da injinan noma, da na lantarki, da ƙarafen layin dogo, da injinan sarrafa duwatsu, da majigi da sauransu.
Wata sanarwa daga fadar gwamnatin ta ce da ma an dakatar da shigar da kayan na ɗan wani lokaci amma yanzu haramcin zai ci gaba har zuwa ƙarshen 2022.
"Wannan matakin ya zama dole don tabbatar da samun natsuwa a kasuwannin Rasha," a cewar sanarwar.
Matakin na zuwa ne yayin da ƙasashe da kamfanonin duniya ke ci gaba da ƙaurace wa harkoki da Rasha da zimmar matsa mata ta janye dakarunta da ke luguden wuta a Ukraine tun daga ranar 24 ga watan Fabarairu.

Asalin hoton, NCBN
Hukumar hana fasa ƙwauri a Najeriya ta kwastam ta ce ta kama buhunhunan naman jaki 1,390 da ake shirin yin safararsu a Jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Kwantirolan da ke kula da shiyyar Kebbi, Joseph Attah, ya ce darajar kuɗin naman da suka kama ta kai naira miliyan 42.
"Ɗaya daga cikin waɗanda suka zo da naman ya faɗa mani cewa sai da suka yanka jaki kusan 1,000 kafin su samu wannan yawan naman," in ji Mista Attah.
Ya ƙara da cewa safarar dabbobin da aka ayyana a matsayin waɗanda ba na ci ba ya saɓa wa sashe na 63 (b) na kundin dokar hukumar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Ƙungiyoyin agaji sun yi gargaɗin cewa adadin mutane da suka rasa muhallansu a Burkina Faso na ƙaruwa saboda hare-haren masu ikirarin jihadi.
Sun ce a watan Janairun da ya wuce kaɗai, mutum 160,000 sun tsere daga muhallansu abin da ya kai adadin zuwa mutum miliyan ɗaya da dubu 700 da aka tursasa wa barin muhallansu.
Hukumomin agaji ciki har da kungiyar da ke kula da 'yan gudun hijra ta Norwegian Council da kuma Oxfam, sun ce wannan tashin hankalin ya fi illa ga yara wadanda ake tilasta wa daina zuwa makaranta.
Kungiyoyin agajin sun kuma yi gargadin cewa rikicin Ukraine a yanzu ya janyo kungiyoyin sun rage kudaden da suke kashewa wajen taimaka wa mutanen da rikici ya rutsa da su a yankunan Afirka.

Asalin hoton, Nigerian Army
Rundunar sojan Najeriya ta ce dakarunta da ke aiki a rundunoni daban-daban sun yi nasarar kashe waɗanda ta kira 'yan ta'adda fiye da 100 a arewacin ƙasar.
Rundunar ta bayyana haka ne ta bakin kakakinta Benard Onyeuko a yau Alhamis yayin wani taron manema labarai, yana mai cewa sun cimma nasarar ce cikin mako biyu da suka gabata.
Cikin ayyukan da ta ce rundunarta ta Operation Hadarin Daji na gudanarwa a jihohin arewa maso yamma, sojoji sun yi nasarar kashe 'yan fashin daji 90 tare da ƙwato shanu 574 da babur 22 da kuma bindigogi ƙirar AK-47 uku a Jihar Zamfara.
Su ma dakarun Operation Hadin Kai a yankin arewa maso gabas sun harbe wasu 'yan ƙungiyar Boko Haram ko kuma ISWAP 10 a Jihar Borno. Sojojin sun ƙwace kekuna 10 da wasu bindigogi daga hannun masu iƙirarin jihadin.
Sai kuma rundunar Whirle Stroke da ta kashe wani "ƙasurgumin" ɗan fashi mai suna Janta a Ƙaramar Hukumar Katsina Ala ta JIhar Benue.

Asalin hoton, Reuters
Kamfanin hada magunguna na Pfizer zai aike da maganin cutar korona ga hukumar da ke yaki da cutuka masu yaduwa ta Afirka.
Za a soma amfani da maganin - mai suna Paxlovid - idan aka ga alamun cutar a jikin mutanen da ke fuskantar hatsarin kamuwa da cutar.
A halin da ake ciki, bayanan yarjejeniyar da aka kulla tsakanin hukumar da ke yaki da cutuka masu yaduwa ta Afirka da Pfizer suna ofishin lauyoyin hukumar - bayan haka ne za a fitar da sanarwa a hukumance, a cewar daraktan hukumar a Afirka, John Nkengasong.
Ya yi kira ga ministocin lafiya na nahiyar su dauki kwararan matakai na riga-kafi da gwaje-gwaje da Pfizer zai bayar.

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyoyin agaji suna nuna damuwa cewa yakin da ake yi a Ukraine yana sa ana rage tallafi ga wasu ayyukan da ke bukatar agaji - ciki har da yaki a Yammacin Afirka da kuma fari a gabashin nahiyar.
A Burkina Faso, inda rikicin masu ikirarin jihadi yake watsuwa, kungiyoyin agajin ciki har da kungiyar da ke kula da 'yan gudun hijira ta Norwegian Council da kuma Oxfam sun ce masu bayar da agaji sun rage bayar da shi da kusan kashi 70 domin bayar da tallafi kan yakin da ake yi a Ukraine.
Sun ce hakan zai yi mummunar illa kan fiye da mutum miliyan daya da dubu 700 wadanda suka tsere daga gidajensu saboda rikicin masu ikirarin jihadi.
A Somalia, Majalaisar Dinkin Duniya tana gargadin cewa yakin Ukraine ya sa za a samu karin matsalolin fari kan kashi daya cikin uku na 'yan kasar.
Matsalar talauci ta yi kamari saboda annobar korona, yayin da sauyin yanayi yake ci gaba da tasirin da ya hada da tashin farashin kayan abinci.

Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatar harkokin tsaron Birtaniya ta ce sojojin Rasha sun tabbatar da cewa sun yi amfani da wasu makaman roka da ake kira Vacumm bom wadanda ke zuke iska a Ukraine.
Makaman kan kama da wuta bayan sun zuke iskar wajen da suka fado abin da ke sa su zamo masu matukar hadari.
Ba a haramta amfani da su ba, to amma akwai sharudda kan yadda ake amfani da su.
A baya, Rasha da Amurka sun yi amfani da irinsu a Afghanistan da kuma Vietnam.
Ma'aikatar harkokin tsaron da ke London, ta ce ta yi amanna Rasha ta tura sojojin haya zuwa Ukraine wadanda a baya aka zarge su da aikata cin zarafin bil adama a Syria da Libya da Kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Kungiyoyin agaji sun yi gargadin cewa adadin mutane da suka rasa muhallansu a Burkina Faso na kara karuwa saboda hare-haren masu ikirarin jihadi.
Sun ce a watan Janairun daya wuce kadai, mutum dubu 160 kadai sun gudu sun rasa muhallansu abin da ya kai ga adadin mutum miliyan daya da dubu dari bakwai da aka tursasawa barin muhallansu.
Hukumomin agajin ciki har da kungiyar da ke kula d a'yan gudun hijra ta Norwegian Council da kuma Oxfam, sun ce wannan tashin hankalin ya fi illa ga yara wadanda ake tursasawa rashin zuwa makaranta.
Kungiyoyin agajin sun kuma yi gargadin cewa rikicin Ukraine a yanzu sun janyo kungiyoyin su rage kudaden da suke kashewa wajen taimakwa mutanen da rikici ya rusta da su a yankunan Afirka.
Wata mata da ake tuhumarta da kashe wani dan kasuwa ta lashe gasar mace mafi kyau ta "Miss Cell 2022", a gidan gyara hali na Kirikiri da ke birnin Legas.
Matar mai suna Chidinma Ojukwu, wacce labarinta ya karade gidajen jaridar Najeriya ba ta amsa laifin kisan kan da ake tuhumarta da aikatawa ba.
An dai kashe mutumin ne mai suna Usifo Ataga a watan Yunin bara - wanda shi ne mamallaki tashar talabijin ta Super TV yayin da yake raye - bayan an daba ma sa wuka.
An ga hotunan Mis Ojukwu sanye da kayan da ake saka wa sarauniyar kyawun yayin da aka gudanar da bikin a cikin gidan gyara halin na Kirikiri, wanda shugaban hukumar gidajen gyara halin na Najeriya ya ce yana cikin abubuwan da suka shirya domin bikin Ranar Mata ta duniya ta bana.
Jaridar Punch ta turancin Ingilishi a Najeriya ta wallafa hotunan bikin:

Asalin hoton, @MobilePunch

Asalin hoton, @MobilePunch

Asalin hoton, @MobilePunch

Asalin hoton, @MobilePunch

Asalin hoton, MARIUPOL CITY COUNCIL
Ga wadanda yanzu suka fara bibiyar BBC Hausa, ga abubuan da ke faruwa na baya-bayan nan a Ukraine:

Asalin hoton, EPA
Ministan harlkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya yi bayani kan tattalin arzikin Rasha: "Za mu jure ma takunkuman - mun jure ma irin wadannan matsalolin ciki tarihinmu."
Ya kuma ce "Tunani da nazarin Rasha zai inganta bayan wannan rikicin."
"Ina tabbatar muku cewa za mu jure ma komai kuma za mu dauki dukkan matakan kauce ma dogara ga kasashen yammacin Turai, a dukkan fannonin rayuwarmu."
Lavrov ya kuma ce rasha ta "janyo hankalin duniya" cewa Ukraine na juya ma Rasha baya na tsawon shekaru, kuma ya ce: "Ana mayar da Ukraine karen farautar kasashen yammacin Turai."

Ministan harkokin wajen Ukraine Dmitry Kuleba ya gana da manema labarai bayan ganawar kai tsaye da ministocin Rasha da na Ukraine suka yi a Turkiyya dazu.
Kuleba ya ce kasashen biyu sun amince su ci gaa da kokarin kawo karshen matsloln da al'ummar kasar Ukraine ke fuskanta a yankunan da ake yaki.
Ya kuma ce a shirye yake ya sake ganawa da takwaran nasa na Rasha, "domin tattaunawar neman mafita".
Ya kara da cewa: "A shirye na ke in ci gaba da wannan tattaunawar da zummar kawo karshen yakin da ake yi a Ukraine."

Bayan tatatunawar da ministocin harkokin wajen Rasha da Ukraine suka yi kai tsaye a Turkiyya, minista Sergei Lavrov na Rasha ya amsa tambayoyi.
Da aka tamabaye shi yadda yakin da kasarsa ke yi a Ukraine, ya ce harin aiki ne na musamman kuma yana gudana yadda aka tsara shi tun farko.
Lavrov ya tuhumi kasashen yammacin Turai da daukan matakai "masu hadari" ta hanyar ba Ukraine makamai, yana cewa wannan matakin ya keta "dukkan abubuwan da suka amince da su."
Da aka tambaye shi ko Rasha na da niyyar kai wa wasu kasashen hari, sai ya ce ba ta da wannan shirin kuma ya nanata matsayar Rashar cewa ba hari ta kai wa Ukraine ba.

Asalin hoton, Getty Images
Ministocin harkokin wajen Rasha da Ukraine na tattaunawa a karon farko tun bayan da Rasha ta fara mamayar kasar Ukraine kamar yadda kamfani dillancin labarai na Reuters ya ruaito.
Ministocin harkokin waje Mevlut Cavusoglu na Turkiyya da Sergey Lavrov na Rasha da kuma Dmytro Kuleba na Ukraine na halartar tattaunawa a Antalya na Turkiyya.

Asalin hoton, PA Media
Gwamnatin Birtaniya ta dauki matakin ladabtarwa kan mamallakin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Roman Abramovich a karkashin martaninta kan mamayar da Rasha ke yi wa kasar Ukraine.
Yana cikin manyan attajirai bakwai da Birtaniyar za ta kakaba wa sabbin matakan ladabtarwa, ciki har da kwace kadarorinsa da hana shi tafiye-tafiye.
Cikin attajiran da wannan matakin zai shafa akwai Igor Sechin da Oleg Deripaska, wadanda ake kallo a matsayin makusantan Shugaban Rasha Vladimir Putin.
Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya ce "babu maboya" ga wadanda ke ba wannan mamayar goyon baya.
Gwamnatinsa ta sha matsin lamba domi ta dauki mataki kan Mista Abramovich, wanda ya ce ya yanke shawarar sayar da kungiyarsa ta Chelsea a farkon wannan watan.
Ana hasashen Abramovich mai shekara 55 na hannun daman Vladimir Putin ne, hasashen da ya musanta, inda ake kuma ganin Abramovich na da arzikin da ya kai fam biliyan 9.4.

Asalin hoton, Natalia Miroshnikova
Tun bayan da rasha ta mamaye kasarsu, wsu 'yan Ukraine su 17,000 da suka tafi Masar domin yawon bude idanu sun makale a yankin shakatawa na Sharm el-Sheikh da ke gabar tekun Bahar a Ahmar.
Sun kasance cikin wannan halin inda sai dai su kali tashin hankain da ke aukuwa a talabijin.
Natalia Miroshnikova, wadda wannan ne karon ta na farko na tafiya kasashen waje ta ce:
"Rudani da hawaye da kuma gigita muke ciki!.
Wannan tafiyar ta yi ta ne tare da mijinta da kuma dan su - amma da suka so barin garin da safiyar ranar 24 ga watan Fabrairu, sai ba su ga jirgin da suka yi shata ba.
Sai daga baya ta gane cewaa yaki ya barke tsakanin Raha da kasarta cikin wani sako da makarantar da nasu ta aiko.
Wata mai yawon shakatawar, Julia, wadda ke da 'ya'ya takwaye da ke Hurghada ta ce tilas babu shiri ta sanar da 'ya'yan nata halin da ake ciki.
"Na sha kuka babu kakkautawa a kwanakin farko kuma na kasa boye halin da nake ciki," inji ta. "Mijina na Kyiv kuma halin da birnin ke ciki ya tayar min da hankali."
'Yan Ukraine din da ke Masar na da zabi - ko dai su ci gaba da zama a otel-otel din da suke a yanzu a farashi mai rahusa, ko kuma su koma wasu masaukan masu arha da gwamnatin Masar za ta biya dominsu.
A shekarun baya Rashawa ne kan gaba a yawan masu zuwa yawan bude ido a Masar, inda 'yan Ukraine ke na biyunsu.
Gwamnatin Masar ta umarci otel-otel din kasar su tabbatar ba su sauke 'yan kasashen biyu a masaukansu ba.

Asalin hoton, cbp
Jami'an da ke tsaron kan iyakokin Amurka sun gano gwamman kadangaru da macizai boye cikin rigunan wani mutum yayin da yake kokarin shiga kasar daga Mexico a watan jiya.
An gano wannan abin al'ajabin ne a kan iyakar San Ysidro da ke kusa da San Diego da misalin karfe 3 agogon yankin a ranar 25 ga watan Fabrairu.
An dakatar da mutumin ne lokacin da ya tunkari kan iyakar cikin wata mota kirar a-kori-kura.
Jami'an sun gano kadangaru 43 da macizai tara cikin rigar mutumin da cikin aljihun wandonsa, kamar yadda jami'an tsaron kan iyakar suka ce.
Mutumin Ba'Amurke ne mai shekara 30 da haihuwa, kuma na take aka kama shi da tuhumar yana saka rayuwar dabbobin dawa cikin hatsari. da kuma yin fasa kwaurinsu zuwa Amurka
Bayan da aka kama mutumin, jami'an sun kwace dabbobin kma sun mika su ga wata cibiyar da ke kulawa da su.

Asalin hoton, AFP
Wani dan Saudiyya da Amurka ke tuhuma da zama mutum na 20 ciin wadanda suka kai harin 11 ga watan Satumbar 2001 ya shaki iskar 'yanci bayan da aka sake shi daga gidan yarin Guantanamo Bay, inji ma'aikatar tsaro ta kasar.
Amurka ta saki Mohammed al-Qahtani, mai shekara 46 kuma ta tasa keyarsa zuwa Saudiyya bayan da wani kwamiti ya sake duba batunsa, kuma ya ce babu alamar zai sake zama mai hatsari ga Amurka.
Kwamitin ya jingina sakamakon nasa ne kan abin da ya kira "tabarbarewar lafiyar kwakwalwarsa".
Bayan da aka kama shi a a 2001 Amurka ta azabtar da shi har ta kai ga ba za a iya gurfanar da shi a gaban shari'a ba.
Jmai'an gwamnatin Amurka sun ce dama an shirya cewa Qahtani zai shiga jirgin United Airlines mai lamaba 93 ne, wanda shi ne ya fado a jihar Pennsylvania bayan da wasu wadanda ake tuhuamr 'yan al Qaeda ne su hudu suka kwace shi daga matukansa a ranar 11 ga watan Satumbar 2001.
Sai dai Amurka ta hana shi bizar shigga kasar a watan Agustan wannan shekarar.