Buhari ne ya ce a cire Mai Mala Buni – El-Rufai

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Sani Aliyu

  1. Mutum 22 sun mutu bayan harin da Rasha ta kai ta sama a birnin Sumy na Ukraine

    Sumy Region of Ukraine

    Asalin hoton, Sumy Regional State Administration

    Mun sami karin bayani kan wani hari da Rasha ta kai da yayi sanadin mutuwar mutum 22 - cikinsu har da kananan yara uku - a birnin Sumy na kasar Ukraine.

    Gwamnan yankin Sumy Dmytro Zhyvytskyi ya ce cikin dare Rasha ta harba bama-bamai ne ayankin da fararen hula ke zama wanda ke arewa maso gabashin birnin, inda ya ce kisan kiyashi ne Rashar ta yi.

    Ya shaida wa BBC Ukrainian cewa: "Bama-bamai uku cikin dare daya... Abin babu kyawun gani."

    harin ya halaka mutum uku da ke zaune tare cikin gida daya. Ya kuma lalata gidaje uku baki dayansu, inda wasu gidaje 20 kuma aka lalata su sosai.

    Kamar yadda muka fadi a baya, mutum 5,000 sun sami ficewa daga birnin na Sumy, bayan da Rasha ta amince ta dakatar da bude wuta kan birnin domin a bude wa fararen hula hanyoyin jin kai na barin birnin.

  2. Kamfanonin jiragen sama sun dakatar da ayyukansu kan tsadar da man jirgin sama ke kara yi

    Jirgin sama

    Da alama babu sauki nan kusa kan batun tsadar man fetur a Najeriya, matsalar da ta tilasta wa kamfanonin sufurin jirgin sama kara farashin tikitinsu a kwanakin baya.

    Kamfanonin sun ce a jiya sun yi mamaki bayan da aka sanar da su cewa an kara farashin man jirgin saman, inda ake sayar da shi kan naira 607 kan kowace lita a Kano a jiya.

    Wannan ya kasance karin fiye da naira 100 cikin kwana guda.

    Jaridar Daily Trust ta ce wasu masu kamfanoni sufurin jiragen saman sun sami sanarwar ce daga masu dillancin man a jiya, wadda ke sanar da su cewa farashin man na JetA1 ya karu zuwa naira 597 a Legas, kuma ya koma naira 599 a Abuja da Port Harcourt, sannan ya koma naira 607 a Kano.

    A ranar Litinin an rika sayar da man kan naira 470 ne a Legas, inda a Kano kuwa naira 495 aka sayar da shi.

    Wannan matakin ya janyo soke sauka da tashin jiragen sama a manya da kananan filayen jirgin sama na Najeriya.

    Yawancin kamfanonin sufurin jirgin saman sun fitar da sanarwar da ke bayana halin da suka shiga kuma sun ba abokan huldarsu hakuri.

    Kakakin kamfanin Azman Airline ya koka kan halin da suka sami kansu a ciki kuma ya ce babu yadda za su iya mayar da uwar kudin da suke zubawa balle ma su sami riba.

  3. Abin da ya faru a Ukraine a wayewar garin yau Laraba

    Russian Mig-29 aircraft

    Asalin hoton, reut

    Idan yanzu ku ka fara bibiyar BBC Hausa, ga wasu cikin abubuwan da suka faru cikin kwanai 14 na mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine:

    • Ministan harkokin wajen Erasha Sergei Lavrov da takwaransa na Ukraine Dmytro Kuleba suna daf da tattaunawa da juna ranar Alha,is a Turkiyya - ganawarsu ta farko tun bayan da Rasha ta fara mamayar Ukraine
    • Kimanin mutum 5,000 aka kwashe daga birnin Sumy na arewa maso yammacin Ukraine bayan da Rasha ta amince ta tsagaita jefa bama-baman da ta ke yi
    • Gwamnan birnin ya ce za a cigaba da kyale mutanen birnin su fice zuwa yau Laraba
    • Rasha za ta kuma bude wasu hanyoyin na jin kai a biranen Kyiv, Chernihev, Sumy, Kharkiv, da Mariupol daga misalin karfe 7:00 na safiyar yau agogon GMT
    • Amurka ta ki amincewa da tayin da kasar Poland ta yi ma ta cewa za ta tura dukkan jiragen yakinta samfurin Mig-29 zuwa Ukraine domin su yaki Rasha
    • Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar cewa kasarsa za ta daina sayen dukkan albarkatun mai daga Rasha, ciki har da makamashin kwal domin yi wa tattalin arzikin "Rasha mummunar illa"
    • Kamfanonin Amurka McDonald's, Starbucks da Coca-Cola sun sanar da cewa za su dakatar da kasuwanci a Rasha
  4. Barkanmu da safiyar Laraba

    Sani Aliyu, BBC Hausa Service

    Asalin hoton, Sani Aliyu / BBC HAUSA

    Kamar kullum, a yau ma BBC za ta ci gaba da kawo muku yadda take kasancewa a fagen dagar yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine tun daga ranar Alhamis, 24 ga watan Fabrairu zuwa yau.

    Za mu kuma kawo muku muhimman labarai daga wasu sassa na Najeriya da wasu kasashen Afirka da na duniya.

    Suna na Sani Aliyu, kuma ni ne zan jagoranci gabatar muku da labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa kai-tsaye daga na n BBC Hausa.