Buhari ne ya ce a cire Mai Mala Buni – El-Rufai

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Sani Aliyu

  1. A nan za mu dakatar da kawo labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a duniya

    Sai gobe

  2. Gwamnan Ebonyi ya ɗaukaka kara kan tsige shi

    Gwamnan jihar Ebonyi Dave Umahi da ke kudu maso gabashin Najeriya ya daukaka kara game da hukuncin wata babbar kotun tarayya wadda ta bayar da umurnin sauke shi daga mulki bisa sauya sheka da ya yi daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

    Takardar da suka gabatar ta daukaka karar, ta ce kotun ta yi kuskure a hukuncin da ta yanke, saboda haka ne ya ce yana da ja da daukacin shari'ar.

    Takardar ta ce kotun ta gaza bisa dogaron da ta yi da sashen na 68, da na 109 na kundin tsarin Mulki wanda dole gwamnan ya bar mukaminsa kasancewar ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP wadda aka zabe shi a karkashinta, zuwa jam'iyyar APC mai mulkin kasar, wanda hakan a cewar takardar tamkar watsi ne da wani hukunci da kotun kolin kasar ta taba yankewa, tsakanin ministan shari'a na Najeriya da tsohon mataimakain shugaban kasa Atiku Abubakar, inda ta ce babu wani tanadin kundin tsarin mulki da ya haramta wa shugaban kasa, ko mataimakinsa, ko kuma gwamnan, ko mataimakinsa daga sauya sheka daga wata jam'iyya zuwa wata.

  3. Buhari ne ya ce a cire Mai Mala Buni – El-Rufai

    nasirelrufai

    Asalin hoton, @nasirelrufai

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya goyi bayan cire gwamnan Yobe Mai Mala Buni a matsayin shugaban riko na APC kamar yadda gwamnan Kaduna Malam Nasir El Rufai ya bayyana.

    A hirar da kafar talabijin ta Channels ta yi da shi ranar Talata, El Rufai ya ce gwamnan Neja Sani Bello ya samu goyon bayan Buhari da kuma gwamnonin APC 19.

    Sannan ya ce Buhari ne ya ce a cire gwamnan Yobe Mai Mala Buni.

    “Buhari ne ya bayar da umarnin a cire shi kuma aka aiwatar, yanzu gwamna Bello ne ya gaje shi,” kamar yadda El Rufai ya bayyana.

    Ya ce Mai Mala Buni wanda ba ya ƙasar zai dawo ne a matsayin gwamnan Yobe amma ba matsayin shugaban jam’iyyar APC ba.

  4. Majalisar Guatemala ta haramta auren jinsi

    Majalisar Guatemala ta kada kuri'ar amincewa da haramta auren jinsi guda a kasar.

    Dokar kuma za ta haramta koyar da duk wani darasi da ya shafi bambancin jinsi da kuma batun ɗauri ga matan da suka nemi zubar da ciki.

    An haramta zubar da ciki a Guatemala, sai idan ya kasance rayuwar mace na cikin hatsari.

    Kafin ta zama doka, sai shugaban ƙasa Alejandro Giammatte ya amince da dokar.

    Kudurin dokar ta "rayuwa da kariyar iyali" ya samu gagarumin rinjaye a majalisar, inda ƴan majalisa 160 suka kaɗa ƙuri'ar amincewa yayin da takwas kawai suka kaɗa ƙuri'ar ƙin amincewa.

    Babu tabbas ko shugaban ƙasar zai amince da dokar, amma yawancin mambobin jam'iyyarsa suna goyon bayan dokar.

    s

    Asalin hoton, Getty Images

  5. 'Nan ba da jimawa ba Rasha za ta kasa biyan basussukan da ake bin ta'

    kudin rasha

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani kamfanin da ke sa ido kan basussukan da ake ba kasashe ta ce nan ba da jimawa ba Rasha za ta kasa biyan basussukan da ake bin ta.

    Kamfanin Fitch Ratings ya ce a gainsa Rasha za ta gaza biyan basussuka "nan ba da jimawa ba".

    Ana kiran tsarin da kamfanin ke amfani da shi 'credit rating', kuma a wannan karon masu zuba jari na dari-dari sayen takardun lamunin da kasar ke fitarwa.

    Cikin wannan makon Rasha da kanta ta ce takunkumin da aka saka ma ta na iya shafar lokacin da za ta biya basussukan da ake bin ta.

    Wannan ne karo na biyu da Fitch ya fitar da rahoto kan gazawar Rasha ta biyan basussuka, wanda masana ke kallo a matsayin koma baya.

  6. An gano jemagen da ke barazanar karewa a Afirka

    An gano wani jemage da ke fuskantar barazanar karewa a doron kasa a dajin Nyungwe na Rwanda da aka dade ba a gani ba tsawon shekara 40.

    Kungiyar kare jemagu ta duniya ta fara gano jemagen ne a wani kogo a 2019, amma sai bayan shekara uku aka gano cewa nau'in jemage ne mai hatsari.

    Jemagen na cikin nau'in waɗanda aka bayyana da ke fuskantar barazanar karewa a duniya a bara.

    An dasa wasu na'urori a dajin Nyungwe domin sauraren rayuwar jemagun. Dajin Rwanda wuri ne mai yawan goggon biri da ke fuskantar barazanar karewa

    Jemage

    Asalin hoton, AFP

  7. Wani ya harbe ƴarsa jaririya don ba ya son fara haihuwar mace

    Ƴan sanda a Pakistan na neman wani mutum ruwa a jallo da ake zargi ya kashe 'yarsa 'yar kimanin kwanaki bakwai da haihuwa.

    Ana zargin mutumin da harbe jaririyar ne saboda ba ya son ya fara haihuwar 'ya mace sai dai namiji.

    Lamarin ya faru ne a birnin Mianwali da ke tsakiyar Pakistan.

    Bincike ya nuna cewa jaririyar ta mutu ne nan-take bayan harbinta sau biyar da bindiga.

    Kisan ya fusata jama'a tun bayan da aka sanya hoton gawar jaririyar a shafukan sada zumunta.

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin dan adam a kasar sun ce kisan yarinyar da suka sanyawa suna Jannat na daga cikin kisan da aka yi wa ƙanana yara abin da kuma ba za su amince da shi ba har sai an bi mata haƙƙinta.

  8. Uwargida Olena Zelenska ta yi tir da 'kisan kiyashin' da Rasha ke yi

    matar zelensky

    Asalin hoton, Getty Images

    Uwargidan shugaban kasar Ukraine Olena Zelenska ta fitar da wata sanarwa cike da tausayi kan mamayar da Rasha ke yi wa kasarta, tana sukar abin da ta kira "kisan kiyashin" da ake wa fararen hular kasar.

    Ta mayar da hankalinta kan ne kan mace-macen kananan yara har ta ambato sunayen was yara uku da suka halaka yayin yakin da ake gwabzawa.

    Ta ce Ukraine kasa ce mai nema zaman lumana amam za ta kare 'yancinta da kan iyakokinta.

    Sai dai babu wanda ya san inda Misis Zelenska mai shekara 44 ta ke a halin yanzu, kuma maigidanta Shugaba Zelensky ya ce dakarun Rasha na neman inda iyalansa suke.

    Cikin wata wasika da aka wallafa a shafin intanet na shugaban Ukraine da yammacin Talata domin zagayowar Ranar Mata ta Duniya, Misis Zelenska ta ce ta sha karbar wasiku da bukatu na tattaunawa da 'yan jarida kuma wannan wasikar ta kasance amsarta garesu.

    Ta kuma bayyana mamayar da ake ma kasar Ukraine a matsayin wanda "abin al'ajabi ne. Rayuwa a kasarmu ta kwanciyar hankali ce; inda biranenmu da garuruwanmu da kauyukanmu ke cike da rayuwa."

  9. Mutumin da aka yi wa dashen zuciyar alade ya mutu

    Mutumin da aka yi wa datsen zuciyar alade

    Asalin hoton, UNIVERSITY OF MARYLAND SCHOOL OF MEDICINE

    Mutum na farko da aka yi wa dashen zuciyar alade a duniya ya mutu.

    David Bennett, wanda ke fama da ciwon zuciya da ya kai makura ya rayu na tsawon wata biyu bayan dashen zuciyar alade da aka yi masa a Amurka.

    Amma rashin lafiyar ta fara tsananta a kwanakin da suka gabata, kamar yadda likitansa Baltimore ya bayyana.

    Ya ce majinyajin mai shekara 57 ya mutu ne a ranar Litinin 8 ga watan Maris.

  10. Labarai da dumi-dumi, APC ta bai wa yankin Arewa ta Tsakiyar Najeriya muƙamin shugaban jam'iyya

    Kwamatin shugancin jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya na ƙasa ya bayyana muƙamai da ya ware wa kowane ɓangaren siyasar ƙasar kafin babban taronta na ƙasa ranar 26 ga watan Maris.

    Cikin wata sanarwa, APC ta bai wa ɓangaren arewa ta tsakiya muƙamin shugaban jam'iyya, yayin da kudu maso yamma zai samar da sakatare.

    An bai wa yankin kudu maso gabas muƙamin mataimakin shugaban jam'iyya.

    Ta ce an cimma matakin rarraba muƙaman ne a zaman da kwamatin ya yi ranar Talata.

    Sanarwar ta biyo bayan sabuwar dambarwar da ɓarke ne na shugabancin jam'iyyar a shekaranjiya bayan da gwamnan Neja ya karbi ragamar daga hannun gwamnan Yobe.

  11. Labarai da dumi-dumi, Ƴan bindiga sun kashe jami'an tsaro 19 a Kebbi yayin ziyarar mataimakin gwamna

    Rahotanni daga jihar Kebbi a arewa maso yammacin Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun kashe jami’an tsaro a kalla 19 a wani hari da suka kai a ƙauyen Kanya da ke cikin karamar hukumar Danko-Wassagu.

    Maharan sun je ne a kan babura a lokacin da mataimakin gwamnan Kebbi ke ziyara a ƙauyen a ranar Talata.

    Mataimakin gwamnan Samaila Yombe Dabai, ya shaida wa BBC cewa dakarun tsaron sun fafata ne da maharan, amma bai faɗi yawan jami'an da aka kashe ba.

    Mutanen da suka mutun sun haɗa da sojoji 13 da ƴan sanda biyar da wani ɗan sa kai.

    Maharan sun kuma sace kayan abinci da dabbobi.

    Harin ya faru ne kwana ɗaya bayan da ƴan bindiga suka kashe ƴan sa kai 63 a yankin.

  12. Ukraine ta ce babu wutar lantarki a tashar nukiliyar Chernobyl

    Tsohuwar tashar samar da makamashin nukiliya ta Chenobyl

    Asalin hoton, Getty Images

    Ukraine ta ce babu wutar lantarki a tsohuwar tashar samar da makamashin nukiliyarta ta Chenobyl tun bayan da dakarun Rasha suka kwace wajen kusan makonni biyu da suka wuce.

    Ministan harkokin wajen Ukraine, Dmytro Kuleba, ya ce dole Rasha ta tsagaita wuta domin bayar da damar yin gyara a wajen wanda ya fuskanci wani mumunan hadarin da ba a taba cin karo da shi ba a tarihin duniya cikin shekarar 1986.

    Hukumar da ke kula da makamshi ta MDD ta ce dole a samu mafita ciki har da samar da abubuwan da zasu rinka sanyaya manyan injinan wajen.

  13. Shugaban Turkiyya Erdogan na fatan sasanta Rasha da Ukraine

    President Erdogan has offered to mediate in the crisis for several weeks

    Asalin hoton, Getty Images

    A karon farko tun bayan mamayar da Rasha ta ke yi wa Ukraine ta fara, ministocin harkokin wajen kasashen biyu sun amince su gana a Turkiyya gobe Alhamis.

    Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya ce yaa fatan tataunawar da za a yi a wani wurin hutu da ke kudancin kasarsa mai suna Antalya zai "bude kofofin da za su samar da yanayin tsagaita wuta na dindindin."

    Turkiyya na cikin kasashen kungiyar tsaro ta Nato amma ta yi kokarin fitar da wata matsaya da ta yi hannun riga da ta sauran kasashen yammacin Turai kan mamayar ta Rasha.

    Duk da yace Turkiyya ba ta goyon bayan mamayar da Rasha ke yi, amma ya ce takunkuman da ake saka ma ta sun zama tamkar na "cin fuska da na ramuwar gayya kan al'ummar Rasha."

  14. Ana neman wani matashi dan Indiya da ya tafi Ukraine domin yakar Rasha

    Sainikesh, 21, went to study aerospace engineering in Kharkiv

    Asalin hoton, Sainikesh

    An dade da jin labaran dubban dalibai 'yan kasar Indiya da suka makale a Ukraine kuma suna neman hanyoyin ficewa zuwa gida - amma ba a san labarin wani dalibin da ke kan hanyar zuwa Ukraine daga Indiya ba.

    Sainikesh matashi ne mai shekara 21 ya tafi Jami'ar Kharkiv ne domin karatun injiniya a shekarar 2018 daga jihar Tamil Nadu na kudancin Indiya.

    Bayan da yakin ya barke a Uraine, sai iyayensa suka bukaci ya koma gida amma sai ya ki. A maimakon haka sai ya shiga rundunar sojojin Ukraine.

    Sai dai iyayen Sainikesh - wadanda suka ji labarin daga jami'an diflomasiyyar Indiya - ba su so su ce wani abu ga manema labarai ba.

    Wani cikin 'yan uwansa sun shaida wa Sashen BBC Tamil cewa Sainikesh ya dade yana son shiga aikin soja amma ba a dauke shi ba saboda gajere ne shi.

  15. 'Yan sanda a Pakistan na neman mutumin da ya harbe jaririyarsa sau biyar da bindiga

    'Yan sandan Pakistan

    Asalin hoton, Reuters

    'Yan sanda a tsakiyar birnin Mianwali a Pakistan na neman wani mutum ruwa a jallo wanda suke zargi da kashe 'yarsa 'yar kimanin kwanaki bakwai da haihuwa.

    Ana zargin mutumin da harbe ta ne saboda baya son ya fara haihuwar 'ya mace a haihuwar farko sai da namiji.

    Bincike ya nuna cewa jaririyar ta mutu ne nan take bayan harbinta sau biyar da bindiga.

    Kisan ya janyo jama'a sun rinka alawadai tun bayan da aka sanya hoton gawar jaririyar a shafukan sada zumunta.

    Kungiyoyin kare hakkin dan adam a kasar sun ce kisan yarinyar da suka sanyawa suna Jannat na daga cikin kisan da aka yiwa kanana yara abin da kuma ba za su amince da shi ba har sai na bi mata hakkinta.

  16. Yakin Ukraine: Ana fargaban wani sojan Birtaniya ya tafi Ukraine babu izini

    A Ukrainian serviceman stands near captured Russian tanks in the north of the Kharkiv region

    Asalin hoton, Reuters

    Wani sojan Birtaniya ya yi batan dabo, kuma ana fargaban yana son tafiya Ukraine ne.

    Wata majiya a rundunar sojin Birtaniya ta shaida wa BBC cewa ba a ba sojan izinin yin tafiyar ba.

    Matakin ya biyo bayan wani rahoto a jaridar Sun na wani sojan rundunar Coldstream Guards da ya bar barikinsa na Fadar Windsor kuma ya sayi tikitin zuwa Poland a karshen makon jiya.

    Sai dai ma'aikatar tsaron Birtaniya ba ta tabbatar da sahihancin rahoton ba.

    Wani kakakin ma'aikatar ya ce ta hana dukkan sojojin kasar tafiya zuwa Ukraine har zuwa wani lokacin da ba ta sanar ba.

    Amma akwai wasu sojojin da ake fargabar cewa za su iya shiga yakin na Ukraine ba tare da sanin hukumomin Birtaniya ba.

    Birtaniya ta sha nanata cewa ba za ta tura sojojin kasar zuwa Ukraine domin su taimaka wa Ukraine a mamayar da Rasha ke yi wa kasar.

  17. Nadin sabon sarki: Jami'an tsaron Chadi sun kashe masu zanga-zanga 13 a birnin Abéché na gabashin kasar

    Shugaban Chadi Mahamat Deby

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kungiyar da ke fafutukar kare hakkin dan Adam ta ce jami'an tsaron Chadi sun kashe akalla mutum 13 kuma su raunata fiye da mutum 80 yayin da suke kokarin murkushe wasu dubban 'yan kasar da suke zanga-zanga a gabashin kasar.

    Zanga-zangar da aka yi a birnin Abéché ya taso ne saboda adawar da mutanen yankin ke yi da shirin nada musu wani sabon sarki.

    Kungiyar kare hakkin dan Adam ta ce wasu sojojin sun rika harbi kan mai uwa da wabi.

    Ta kuma ce sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da manyan bindigogi.

    Wani ministan gwamnati ya ce sun yi nadamar kisan kan da aka yi amma ya musanta cewa jami'an tsaron kasar sun yi amfani da harsasai na gaske ne kan masu zanga-zangar.

  18. Ukraine ta ce mazauna birnin Mariupol na fuskantar matsananciyar yunwa

    Jiragen yaki na shawage

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani dan majalisar kasar Ukraine ya shaida wa BBC cewa jami'an birnin Mariupol da ke kudu maso yammacin kasar sun ce abincin kwana uku kawai ya rage a birnin kafin yunwa ta fara addabar al'ummar birnin.

    Dmytro Gurin, wanda iyayensa mazauna Mariupol ne ya ce ofishin magajin garin birnin ya sanar da shi cewa akwai gawarwaki a titunan birnin kuma sai da hukumomin birnin suka haka wani babban ramin da suka binne mamamta 33 saboda babu hanyar zuwa makabartar birnin yayin da ake yaki.

    Gurin ya yi kira ga kasashen yammacin Turai da su gane cewa "Yakin duniya na uku tuni aka fara shi".

    Ya kuma ce, "Tambayar da ta rage ita ce sanin yawan 'yan Ukraine da za su mutu da kuma wadanda za su mutu cikin mako daya."

  19. McDonalds ya sanar da rufe duka wuraren kasuwancinsa a Rasha

    Macdonalds in Russia

    Asalin hoton, Getty Images

    Kantin sayar da kayan maƙulashe na McDonalds ya sanar da rufe duka wuraren kasuwancinsa a Rasha na wucin gadi.

    Babban kantin ya ce ba zai ci gaba da zura ido yana ganin bil adama na wahala a Ukraine ba kuma ya yi shiru.

    McDonalds yana da sama da kantina ɗari takwas da hamsin a fadin Rasha kuma sama da Rashawa dubu 60 ke aiki a kantinansa da ke ƙasar.

    Shi ma kamfanin lemo na Coca-Cola ya sanar da cewa zai dakatar da kasuwancinsa a Rasha.

  20. IAEA: Rasha ta hana 'ma'aikatan tashar nukiliya ta Chernobyl hutu'

    Russian soldiers entered the site on 24 February

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Tashar nukiliyar Chernobyl na hannun sojojin Rasha tun 24 ga Fabrairun 2022

    Shugaban hukumar da ke kula da yaduwar makamashin nukiliya ta duniya, IAEA ta yi kira ga sojojin Rasha da ke iko da tashar nukiliya ta Chernobyl da ke arewacin Ukraine, da suk kyale wasu ma'aikatan tashar su huta.

    Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, Rafael Grossi ya ce jami'an gwamnatin Ukraine sun sanar da shi cewa har yanzu ma'aikatan tashar 210 ne ke aiki n atsawon mako biyu babu hutawa.

    Grossi ya ce ya damu matuka ga halin da suke ciki da kuma cewa suna iya fadawa cikin halin matsanancin damuwa.

    Ya kuma ce ya dace ma'aikatan su rika hutawa kuma a rika sauya su da wasu ma'aikatan, inda ya ce hutu na da muhimmanci ga kasancewar komai na aiki lafiya.

    Sojojin Rasha sun kutsa cikin tashar nukiliyar - wadda ita ce tashar da aka yi hatsarin nukiliya mafi muni a duniya - hatsarin da ya auku a ranar 24 ga watan Fabrairun 1986.

    Grossi ya kuma ce hukumar ta daina samun bayanan halin da na'urorin tashar ke ciki, bayanan da a baya suke iya samu ta intanet.