Zelensky ya caccaki Nato kan hana shawagin jirage

Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman game da yaƙin Ukraine.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau

  1. Labarai da dumi-dumi, Ba mu da zaɓi illa mu tsere - Magajin garin Mariupol

    Magajin garin Mariupol, Vadym Boichenko, ya fitar da sanarwa bayan bayyana tsagaita wuta tsakanin Rasha da Ukrain a kan brinin nasa.

    "Mariupol ba tituna ba ne kawai da gidaje," a cewarsa. "Mutanensa ne."

    Ya ƙara da cewa: "Sakamakon ruwan wuta ba ƙaƙƙautawa daga 'yan kama-wuri-zauna, babu wani zaɓi illa mu bai wa mazauna garin...damar tserewa daga Mariupol."

    Tsagaita wutar da Rasha ta yi na ɗan lokaci ne a safiyar Asabar ɗin nan don bai wa fararen hula damar guduwa.

  2. Rasha ta rage kai hare-hare amma tana ci gaba da ratsawa - Birtaniya

    Ukraine

    Asalin hoton, Reuters

    Rasha ba ta kai hare-hare masu yawa ba ta sama da kuma makaman atilare cikin awa 24 da suka gabata kamar a kwanakin baya, a cewar Ma'aikatar Tsaro ta Birtaniya cikin bayanan da take bayarwa.

    Sai dai ta yi gargaɗin cewa dakarun na Rasha na ci gaba da ratsawa cikin birnin Mykolayiv.

    A gefe guda kuma, ta ce "akwai yiwuwar" wasu dakarun za su sauya hanya don kama garin Odesa mai tashar jirgin ruwa.

    A cewar bayanan, har yanzu Ukraine na riƙe da Kharkiv, da Chernihiv, da Mariupol, yayin da ake ci gaba da faɗa a titunan garin Sumy.

    Akwai yiwuwar cewa Rasha ta zagaye dukkan biranen huɗu.

  3. Ukraine za ta yi nasara a yaƙin nan - Amurka

    Mista Blinken

    Asalin hoton, Reuters

    Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya shaida wa BBC cewa yana da yaƙinin Ukraine za ta yi nasara a yakin da suke yi da Rasha.

    Mista Blinken ya ce ba zai fadi yadda hakan ko tsahon lokacin da za a ɗauka ana yakin tsakanin kasashen biyu ba, sai dai ya yi watsi da batun Rasha ka iya cimma burinta a kan mutum miliyan 45 da ke yakin kwatar 'yancinsu.

    Blinken ya bayyana haka ne a Brussels a kan hanyarsa ta zuwa kasar Poland.

    Wakiliyar BBC ta ce ana sa ran da zarar sakataren harkokin wajen ya isa Poland zai kai wa 'yan gudun hijirar Ukraine ziyara da kara jaddada goyon baya ga kasar.

    Sai dai firaministan Poland ya ce yana fargabar kar Rasha ta kai hari wajen.

  4. Rasha ta ayyana tsagaita wuta a birni biyu

    Ukraine

    Asalin hoton, Reuters

    Kwana na 10 kenan da fara luguden wutar da Rasha ke yi a Ukraine. Ga abin da muka sani zuwa yanzu:

    • Ma'aikatar Tsaro ta Rasha ta ayyana tsagaita wuta ta ɗan lokaci don kai agajin gaggawa daga 10:00 agogon Moscow (8:00 agogon Najeriya da Nijar) a yau Asabar a gari biyu da ke kudancin ƙasar, Mariupol da Volnovakha
    • Rasha ta ce ta cimma matsaya game da hanyoyin da za a iya shiga garin tare da ɓangaren Ukraine, sai dai har yanzu Ukraine ba ta tabbatar da hakan ba tukunna
    • Mariupol babban gari ne mai tashar jirgin ruwa kuma an shafe kwanaki Rasha na zagaye da shi. Kazalika, ana ci gaba da fafata yaƙi a Volnovakha
    • Tun farko, magajin garin Mariupol ya buƙaci a ƙyale fararen hula su fice daga birnin saboda abin da ya kira "ƙawanya" daga dakarun Rasha
    • A gefe guda kuma, ana ci gaba da fafatawa a wasu wurare. An jiyo fashe-fashe a birnin Kharkiv da ke arewa maso gabashin Ukraine
  5. Barkanmu da asuba

    Mun sake haɗuwa da ku a sabon shafin labarai kai-tsaye, wanda ke kawo rahotannin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya tare da ni Umar Mikail.

    Za mu fi mayar da hankali kan hare-haren da Rasha ke kaiwa a Ukraine, inda aka shiga kwana na 10.