NATO ta yi shuri da roƙon Ukraine

Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman game da yaƙin Ukraine.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Imam Saleh

  1. Labarai da dumi-dumi, Rasha ta ƙwace iko da cibiyar nukiliyar Ukraine

    Dakarun Rasha sun ƙwace cibiyar makamashin nukiliya ta Zaporizhzhia, a cewar hukumomin Ukraine.

    "Ma'aikata na ci gaba da duba halin da ɓangarorin wutar lantarki ke ciki," kamar yadda wani jami'in yankin ya bayyana a shafinsa na zumunta cikin rahoton Reuters.

    Tun farko gobara ta tashi a cibiyar, wadda ita ce mafi girma a nahiyar Turai, bayan Rasha ta kai hari a kan ta.

  2. Maraba

    Barkanmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye don kawo rahotannin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman hare-haren Rasha a Ukraine.

    Umar Mikail ne zai kasance da ku a wannan hantsi na Juma'a.