Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Rasha ta ce ta ƙwace babbar tashar nukiliyar Ukraine

Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman game da yaƙin Ukraine.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau

  1. Matan da ake zargin mazajensu da taimaka wa Boko Haram na zanga-zanga a Kano

    Hukumomi a ƙasar na zargin mazajen nasu ne da taimaka wa ƙungiyar masu iƙirarin jihadi ta Boko Haram ta hanyar yi musu canjin kuɗin ƙasar waje.

    Mafi yawan mazajen da ake tsare da su fiye da shekara ɗaya 'yan kasuwar canji ne da aka fi sani da wapa, kuma tun da aka kama su ba a bari iyalansu sun gan su ba in ban da kwanan nan, a cewar matan.

    Matan ƙarƙashin jagorancin Aisha Jibril sun ce "buƙatarmu ita ce a gurfanar da su a gaban kotu, masu laifi a hukunta su, waɗanda ba su da laifi a sako mana mazajenmu".

    Wasu daga cikin matan sun fito ne tare da 'ya'yansu ƙanana maza da mata.

    A 2021 ne wata kotu a Dubai da ke ƙasar Daular Larabawa (UAE) ta yanke wa wasu 'yan Najeriya hukunci, ciki har da ɗaurin rai-da-rai, saboda kama su da laifin yi wa Boko Haram canjin kuɗaɗe.

    Sakamakon haka ne jami'an tsaro a Najeriya suka fara kamen wasu 'yan canjin da ake zargi da tallafa wa ƙungiyar wajen yi musu safarar kuɗaɗe.

  2. Za a fara kwaso 'yan Najeriya daga Ukraine a yau Laraba

    Gwamnatin Najeriya za ta fara ɗebo 'yan ƙasarta a yau Laraba da suka tsallaka zuwa ƙasashe maƙota daga Ukraine sakamakon yaƙin da ake yi.

    Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta fitar ta ce ana sa ran rukuni na farko na mutanen za su isa Najeriya gobe Alhamis.

    Ta ƙara da cewa zuwa yanzu hukumomi na da adadin 'yan Najeriya da suka samu shiga Romania da Hungary da Poland da Slovakia. Su ne:

    • Hungary - 650
    • Poland - 350
    • Romania - 940
    • Slovakia - 150

    Sai dai tun wasu 'yan Najeriyar da ma baƙaken fata suka koka kan wariyar launin fata da aka dinga nuna musu yayin da suke ƙoƙarin ficewa daga ƙasar.

    • Daliban Najeriya da suka yi tafiyar awa 72 don ficewa daga Ukraine
  3. Mazauna Ukraine sun wayi garin Laraba da luguden wuta a rana ta shida

    Mazauna Ukraine sun wayi garin Laraba da ƙarar sautin ankararwa saboda hare-haren da sojojin Rasha ke kai wa a faɗin ƙasar.

    Ga abubuwan da muka sani zuwa yanzu:

    • Aƙalla mutum 21 aka kashe tare da raunata 112 yayin wani luguden wuta a gari na biyu mafi girma a Ukraine, Kharkiv, a cewar magajin garin
    • An samu rahotannin kai wasu sabbin hare-haren a birnin, wanda ya hari wani ginin ofishin 'yan sanda na yanki da kuma wani ɓangare na Jami'ar Karazin
    • Kazalika, sojojin lema na Rasha sun sauka a birnin na Kharkiv da zimmar ƙwace yankin da ke gabashin ƙasar, a cewar sojojin Ukraine
    • Dakarun Rasha na ci gaba da ƙwace garuruwa a kudanci, inda ma'aikatar tsaron ƙasar ta ce dakarunta sun ƙwace garin Kherson da ke kudanci
    • An katse harkokin yaɗa labarai a Ukraine sakamakon harin da aka kai kan tashar yaɗa labarai ta gidajen talabijin, inda aka kashe mutum biyar da kuma raunata wasu biyar
    • Sojoji sun umarci mazauna garin Sumy da ke arewaci su nemi gidan ɓuya saboda barazanar harbo makamin atilare, a cewar gwamnan yankin
    • A Amurka kuma, Shugaba Joe Biden ya yi taron manema labarai yana mai bayyana haramta wa jiragen Rasha bi ta sararin samaniyar ƙasarsa
  4. Rasha ta ce dakarunta sun ƙwace garin Kherson

    Ma'aikatar tsaro ta Rasha ta ce dakarunta sun ƙwace iko da garin Kherson da ke kudancin Ukraine.

    Idan ta tabbata, zai zama gari mafi girma da Rasha ta karɓe iko da shi tun bayan fara kai hare-hare ranar Alhamis da ta wuce.

    Tun cikin dare rahotanni suka ruwaito cewa an ga dakarun Rasha a titunan birnin, inda magajin garin ke cewa an ƙwace filin jirgin ƙasa da kuma tashar jiragen ruwa.

  5. Labarai da dumi-dumi, An harba makamai kan ofishin 'yan sanda a Kharkiv

    Kamfanin labarai na UNIAN na ba da rahoton cewa wani makamin roka da aka harba a birnin Kharkiv ya faɗa kan wani gini na 'yan sanda.

    Wani bidiyo da aka wallafa a dandalin Telegram na wani jami'in gwamnatin Ukraine ya nuna ginin na ci da wuta.

    Anton Geraschenko, wanda mai bai wa ministan harkokin cikin gida shawara ne, ya ce wani gini mallakar Jami'ar Karazin shi ma ya kama da wuta sakamakon harin.

    Ya zuwa BBC ba ta iya tabbatar da ingancin bidiyon ba.

  6. Maraba

    Sannunmu da sake haɗuwa a shafin rahotanni kai-tsaye.

    Za mu ci gaba da kawo muku yadda take kasancewa a rana ta shida da fara kai hare-haren Rasha a maƙociyarta Ukraine da sauran sassan duniya.

    Umar Mikail ne ke fatan kun wayi hantsin Laraba lafiya.