Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rasha ta ce ta ƙwace babbar tashar nukiliyar Ukraine
Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman game da yaƙin Ukraine.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau
Mutum kusan dubu 900 suka tsere daga Ukraine
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan mutum dubu 900 ne suka fice daga Ukraine, tun bayan da Rasha ta ƙaddamar da mamayar kasar, ranar Alhamis da ta gabata.
Sama da rabin adadin sun shiga Poland, yayin da wasu dubu 100 ɗaya suka nufi yamma zuwa kasar Hungary.
Hukumar kula da ƴan gudun hijira ta majalisar na turakarin ma'aikata da kayan agaji domin tallafa wa 'yan gudun hijirar, da kuma makwabtan Ukraine wadanda suke bayar da mafaka ga mutanen.
Majalisar na rokon kusan dala miliyan dubu biyu domin gudanar da ayyukanta na jin-kai.
Hasashen da aka yi da farko cewa kusan 'yan Ukraine miliyan hudu za su tsere daga kasar, alkaluman ka iya zarta haka matuka gaya.
Rasha ta ce ta ƙwace babbar tashar nukiliyar Ukraine
Gwamnatin Rasha ta gaya wa hukumar da ke sa ido kan harkokin nukiliya ta duniya cewa, a yanzu haka yankin da babbar tashar nukiliya ta Ukraine take, kusa da birnin Zaporizhzhia na kudanci yana karkashin ikonta.
Hukumar nukiliyar, IAEA, ta ce Rashawan sun ba ta tabbacin cewa ma'aikatan Ukraine da ke aiki a tashar na ci gaba da gudanar da ayyukansu.
Sai dai hukumar nukiliyar Ukraine ta ce tana tattaunawa da dukkanin tashoshinta na nukiliyar, kuma aiki na ci gaba da gudana a dukkanninsu.
Amma Darakta Janar na hukumar nukiliyar ta duniya, Rafael Grossi, ya shaida wa taron manema labarai cewa halin da ake ciki na da tayar da hankali
Ya ce abu mafi muhimmanci a nan shi ne, idan ana rikici, lalle akwai fargabarkai hari, ko kuma ma a samu hadarin tashin makaman.
Tashar Zaporizhzhia tana dauke da shida daga cikin na'urorin nukiliya 15 na Ukraine.
Kafin yanzu dai hukumomin da ke kula da nukiliyar Ukraine sun bukaci taimakon hukumar nukiliya ta duniya, da ta taimaka ta tabbatar da tsaro a cibiyarta ta Chernobyl da ke arewacin Ukraine, wadda dakarun Rasha suka kwace.
Rasha na ci gaba da ruwan wuta a biranen Ukraine
Rasha na ci gaba da tsananta kai hare-hare kan tashar jirgin ruwa da ke Mariupol inda hukumomi suka ce akwai yiwuwar an halaka daruruwan mutane.
Mataimakin magajin garin ya shaida wa BBC cewa ruwan makaman da Rasha take ta yi, ya lalata kusan baki dayan wata gunduma, wadda take da mutane sama da dubu 100.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutum dubu dari takwas sun tsere daga Ukraine zuwa yanzu. Ministocin cikin gida na Turai na gab da fara tattaunawa kan wata shawara da hukumar Turai ta gabatar ta neman a bai wa mutanen da ke tserewa yaki a Ukraine kariya ta wuccin gadi.
Haka suma biranen Chernihiv da Kharkiv da ke arewacin kasar sun sha mummunan harin makaman atilari na Rasha.
Rasha dai ta tsananta hare-harenta a kan muhimman wurare a fadin kasar ta Ukraine, inda hukumomin bayar da agajin gaggawa suka yi kiyasin cewa sama da mutum 2000aka kashe tun da aka fara mamayar.
Can kuma a wani bangaren yayin da wata babbar kwamba ta dakarun Rasha ta durfafi, Kyiv, mazauna garin Ivankiv, da ke arewa da babban birnin sun ce sun kasa tserewa, bayan da sojin na Rasha suka kame iko da yankin a makon da ya wuce.
Farashin ɗanyen mai ya ƙara tashi a duniya bayan ƙauracewa man Rasha
Farashin ɗanyen mai ya ƙara tsada a ranar Laraba, yayin da ƴan kasuwa suka rungumi man da ba na Rasha ba, wanda zai haifar da tsadar man a Birtaniya.
Ɗanyen mai samfurin Brent - ma'aunin farashin mai a duniya - ya haura dala 113 a kowace ganga, cirawa mafi girma tun watan Yunin 2014.
Ƴan kasuwa na shan wahalar sayar da man Rasha, duk da sun sassauta farashi, saboda wahalar ɗauko man da kuma biyan kuɗi sakamakon rikicin Ukraine.
Farashin Gas ma ya lunka.
Kusan kashi 70 na ɗanyen man Rasha babu wanda zai saya, kamar yadda wani kamfanin makamashi na Energy Aspect na Birtaniya ya bayyana.
Ƴan kasuwa dai na tsoron kada su fuskanci fushin hukumomi sakamakon takunkumin da ƙasashen yammaci suka kakabawa Rasha.
Labarai da dumi-dumi, Abramovich zai sayar da Chelsea
A cikin wata sanarwa da Chelsea ta fitar ta ce Roman Abramovich ya tabbatar da zai sayar da ƙungiyar.
Wannan ya tabbatar da jita-jitar da ake yi kan Chelsea.
Tuni aka ruwaito cewa attajirin na Rasha zai gaggauta sayar da Chelsea bayan batun barazanar takunkumi da aka tayar a majalisa.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi Allah wadai da mamayar Rasha a Ukraine
Ƙasashe mambobin Majalisar Ɗinkin Ɗuniya sun kada kuri'a da gagarumin rinjaye ta nuna kyama ga mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, inda suka nemi janyewarta nan take.
Ayayin taron na gaggawa wanda ba kasafai ake irinsa ba, Rasha ta kare matakinta na mamayar makwabciyarta, tana musanta cewa ta aikata laifin yaki, tare da zargin ƙasashen yamma da matsa wa da kuma barazana ga kasashe kan su jefa kuri'ar amincewa da matakin , ba tare da ta bayar da wata sheda ba.
Ƙasashe 141 suka amince da kuɗirin daga cikin mambobin majalisar 193 a babban taron na Majalisar Ɗinkin Duniya
Ƙasashje 35 suka kaurace wa kuri'ar, ciki har da Rasha da Indiya.
Rahoton ya kuma yi Allah-wadarai kan yadda Shugaba Putin na Rasha ya sanya dakarun nukiliya na kasarsa cikin shiri.
Wannan ne taron gaggawa na farko tun 1997.
Waɗanne ƙasashe ne suka kaɗa ƙuri'ar ƙin amincewa?
Ƙasashe biyar ne suka kaɗa ƙuri'ar ƙin amincewa da kudirin yin Allah wadai da Rasha.
Bai zo da mamaki ba da Belarus babbar aminiyar Rasha ta bayyana adawa da kuɗirin. Wasu dakarun Rasha ta Belarus suka kutsa Ukraine.
Syria ma babbar aminiyar Rasha ta ƙi amincewa da ƙudirin.
Haka ma Eritrea daga Afirka da Koriya Ta Arewa daga yankin Asiya da suka ƙi amincewa da ƙudirin.
China ta ƙauracewa zaman kaɗa ƙuri'ar
Rasha ta ce sojojinta 498 aka kashe a Ukraine
Ma'aikatar tsaron Rasha ta bayyana alƙalumman farko na yawan sojojin da aka kashe a yaƙin Ukraine.
Ta ce sojojin Rasha 498 kawai aka kashe, yayin da 1,597 suka samu rauni, kamar yadda kafofin yaɗa labaran Rasha suka bayyana.
Adadin ya ci karo da alƙalumman da Ukraine ta bayar inda ta ce ta kashe sojojin Rasha 5,840.
Rasha kuma ta yi ikirarin kashe sojojin Ukraine sama da 2,870 kuma kusan 3,700 suka jikkata. Zuwa yanzu Ukraine ba ta bayyana wasu alƙalumma ba.
BBC ba za ta iya tantance iƙirarin Rasha ba ko na Ukraine, amma ma'aikatar tsaron Birtaniya ta bayyana cewa sojojin Rasha sun ji jiki.
Tun da farko hukumar agajin gaggawa ta Ukraine ta ce sama da fararen hula 2,000 da jami'ain agaji 10 aka kashe zuwa yanzu.
Fashewa ta kashe magajin gari a Kamaru
Aƙalla mutum biyar da suka haɗa da wani babban jami’i da magajin gari suka mutu sakamakon fashewa
Lamarin ya faru ne a yankin da ke magana da harshen ingilishi.
Ƴan a ware ne suka kai wa ayarin mutanen hari a kan hanyarsu tsakanin Ekondo-Titi da Bekora, kamar yadda wani babban jami’in ƴan sanda ya shaida wa kamfanin dillacin labaran Faransa.
Tun a 2017 wasu mutanen suka ɗauki makamai suna neman ƴancin kai daga ƙasar Kamaru da mafi yawanci ke magana da harshen Faransanci.
Ƴan Najeriya na ce-ce-ku-ce kan bikin murnar zagayowar ranar haihuwar Aisha Buhari a Dubai
Wasu ƴan Najeriya a shafukan sada zumunta sun nuna ɓacin ransu bayan ganin wani bidiyo da ya nuna yadda wasu matan gwamnonin jihohin ƙasar na taya uwar gidan shugaba Buhari murnar zagayowar ranar haihuwarta a ƙasar Dubai.
A ranar 17 ga watan Fabrairu ne Aisha Buhari ta yi bikin cika shekaru 51 a duniya, amma sai yanzu bidiyon ya fito. Babu tabbaci kan lokacin da aka ɗauki bidiyon.
Bidiyon ya nuna wasu gungun mata da kafafen yaɗa labaran Najeria suka ce matan ƴan siyasar ƙasar ne ɗauke da wani ƙaton akwati da furanni, suna rera waƙar murnar zagayowar ranar haihuwa ga Aisha Buhari. Akwai kuma mai daukar hoto a baya.
Wasu sun bayyana mamakin yadda waɗanda suka halarci bikin suka kashe kuɗin jirgi zuwa Dubai.
“Nawa ne daga cikinsu za su yi amfani da kuɗin aljihunsu,” kamar yadda wani mai amfani da Twitter ya bayyana.
Wasu kuma na ganin matan ƴan siyasar sun kama hanya sun tafi biki a daidai lokacin da ƙasa ke fuskantar tarin matsaloli.
"Wannan rashin hankali ne sosai kuma abin baƙin ciki ne", kamar yaddawani ya rubuta.
Bidiyon bai nuna ko shugaba Buhari yana wajen bikin ba.
A ranar 21 ga Fabrairu Aisha Buhari ta wallafa hotonta da tare da wasu matan gwamnoni a wata cibiyar ilimi ta zamani a Dubai inda ta ce tana ƙoƙarin haɗin guiwa da shirinta na inganta ilimi ta hanyar intanet da fasahar ƙere ƙere.
Yaƙin Ukraine ya sa farashin man fetur da na gas na ƙara tashi a duniya
Yayin da ake ci gaba da gwabza yaki a Ukraine, farashin mai da iskar gas na ci gaba da tashin gwauron zabi. Maganan nan da muke da ku, farashin mai ya haura dala 110 a kan kowace ganga daya, kuma farashin sarin gas ya kai kusan inda bai taɓa kaiwa ba.
Wakilin BBC ya ce duk da cewa takunkumin da kasashen yamma suka sanya wa Rasha bai shafi bangaren makamashi ba, akwai fargaba a kasuwar cewa nan gaba, ko kuma ita kanta Rasha ka iya rama wa kura aniyarta ta rike makamashinta ta daina sayarwa.
Farashin man dai na ta tashi ne duk da alkawarin da kasashe sama da 30 da suka yi ciki har da Amurka, cewa za su fitar da ganga miliyan 60 ta danyen man daga rumbunansu na ajiyar ko-ta-kwana.
Ana sa ran yanzu haku wakilan kungiyar kasashe masu arzikin mai, OPEC da sauran kasashe masu samar da mai a duniya suna ganawa a birnin Vienna domin duba yuwuwar kara man da suke fitarwa don dakile tashin farashin.
Yawancin kasuwannin hannun jari na Asia sun fadi a yau Laraba, a sakamakon faduwa kasa sosai da aka samu a kasuwar hannun jari ta Amurka.
Yayin da duk ake wannan ita kuwa China ta ce za ta ci gaba da huldar kasuwancin da take yi da Rasha, kamar yadda suka saba, ba za ta bi sahun kasashen da ke sanya wa Rashar takunkumi ba.
Abin da ya faru a kwana na bakwai na yaƙin Ukraine
Yayin da aka shiga kwana na bakwai a yakin da ake fafatawa a Ukraine, dakarun Rasha sun tsananta hare-haren da suke kaiwa a kan muhimman wurare a bangaren gabashi da da kudanci da kuma arewacin kasar.
Hukumomin bayar da agajin gaggawa na Ukraine sun yi kiyasin cewa zuwa yanzu an kashe sama da mutum dubu biyu a yakin tun bayan da Rasha ta fara mamayar Ukraine din.
Kharkiv - birni na biyu mafi girma a Ukraine ya gamu da luguden wuta na makaman roka da hare-haren jiragen yaki na sama, abin da ya lalata gine-gine da suka hada da na majalisar hukumar birnin.
Akwai rahotannin fito-na-fito a titi da sojojin lema na Rasha. Can a bangaren kudancin Ukraine din, an ce dakarun Rasha na kokarin kama iko da dukkanin tasoshin jirgin ruwa da ke gabar tekun Bahar Aswad, ko bakin teku.
Magajin garin Mariupol ya ce mutane da dama sun samu raunuka saboda tsananin ruwan makamai masu linzami da ake harba masa, abin da ya da wuya a iya kwashe wadanda suka jikkata.
Akwai kuma rahotanni masu karo da juna kan cewa sojojin Rasha sun kwace garin Kherson mai tashar jirgin ruwa.
Shugabannin Taiwan za su tallafa wa 'yan Ukraine da albashinsu
Shugabannin siyasa na Taiwan haɗi da Shugabar kasar, Tsai Ing-wen, za su bayar da albashinsu na wata daya domin tallafa wa mutanen da suke tserewa daga yakin Ukraine.
Mataimakin shugabar kasar da firimiya da kuma shugabannin 'yan hamayya na daga cikin wadanda suka yi alkawarin ba da albashinsu.
Shugaba Tsai ta ce tana fatan dukkanin alummar Taiwan da ma'aikatan gwamnati za su taimaka wa al'ummar ta Ukraine.
Ta ce: ''Ma'aikatar Harkokin Waje za ta sanar da kafa asusun banki na musamman domin tattara tallafin na Ukraine, wanda hukumar ba da tallafin gaggawa ta samar. Hatta daidaikun jama'ar kasar ta Taiwan an bukace su da su ba da tallafin."
Bayan tallafin kudi da za ta bayar, gwamnatin Japan tana kuma shirin aikawa da taimakon kayayyakin kula da lafiya domin 'yan gudun hijirar na Ukraine.
Taiwan na nuna goyon bayanta ga Ukraine saboda ita ma tana fuskantar irin wannan barazana ta mamaya daga China, wadda ke ikirarin tsibirin nata ne.
Najeriya za ta kashe naira biliyan uku wajen kwaso 'yan ƙasar daga Ukraine
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da kashe dala miliyan takwas da rabi - fiye da naira biliyan uku - wajen aikin kwashe 'yan ƙasar daga ƙasashe huɗu maƙotan Ukraine sakamakon yaƙin da ake yi a can.
Ma'aikatar harkokin waje da haɗin gwiwar ta agaji ne za su gudanar da aikin kwashe 'yan ƙasar kusan 5,000 daga ƙasashen Poland da Ramania da Slovakia da Hungary.
Ƙaramin Ministan Harkokin Waje Zubairu Dada ya faɗa wa manema labarai a yau Laraba jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa cewa za a tura jirage uku don gudanar da aikin.
Jiragen sun ƙunshi na kamfanin Air Peace biyu da kuma na Max Air ɗaya.
Wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin wajen ta ce za a fara gudanar da aikin ɗebo su bayan sun tsallaka maƙota daga Ukraine sakamakon fafatawar da ake yi tsakanin dakarun Rasha da na ƙasar.
Jirgin Qatar Airways ya fara sauka a Kano
Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Qatar Airways ya fara sauka a birnin Kano da ke arewacin Najeriya a yau Laraba cikin murna da annashuwa daga hukumomin ƙasar da kuma kamfanin.
Jirgin Boeing 787 ya sauka a babban filin jirgi na Mallam Aminu Kano (MAKIA) da misalin ƙarfe 11:00 da ɗoriya.
Jekadan Najeriya a ƙasar Qatar, wadda ta mallaki kamfanin, Ahmadu Yakubu Abdullahi na cikin waɗanda suka halarci bikin saukar jirgin karon farko a tarihi.
Kano ce wuri na uku a Najeriya da kamfanin zai dinga sauka bayan Abuja da Legas. A gobe Alhamis kuma zai ƙarasa birnin Fatakwal na Jihar Rivers a kudancin ƙasar.
Jirgin ruwa ya kife da 'yan ƙwallo biyar a Sudan
'Yan wasan ƙwallon ƙafa na Sudan biyar sun rasu bayan jirgin ruwan da suke ciki ya kife da su ranar Lahadi, a cewar wata kafar yaɗa labarai ta ƙasar.
'Yan ƙwallon 'yan wasan tawagar Al-Milaha ne, wata ƙungiya a garin Shendi mai nisan kilomita 150 daga arewacin Khartoum babban birnin ƙasar.
Suna kan hanyarsu ce ta zuwa yammacin yankin don buga wasa da ƙungiyar El-Jiref a garin Al-Matammah.
Kungiyoyin mata sun hana shiga da fita a Majalisar Dokokin Najeriya
Wani dandazon mata ya rufe kofar shiga Majalisar Dokokin Najeriya saboda a cewarsu watsi da aka yi da bukatunsu jiya Talata a zauren Majalisar.
A jiya ne 'yan majalisar suka fara kuɗa ƙuri'a kan wasu ƙudirori da aka gabatar na gyaran kundin tsarin mulki, ciki har da wanda ya nemi a bai wa matan kashi 35 cikin 100 na muƙaman siyasa, amma sai 'yan majalisar suka yi watsi da shi.
Matan da suka taru ƙarƙashin ƙungiyoyi daban-daban, sun ce zaman dirshan za su yi a bakin ƙofar.
"Ba za mu bar wajen nan ba har sai mun ga shugaban majalisa, sai majalisa ta bai wa mata 'yancinsu," a cewar Niri Goyit daga ƙungiyar Action Aid.
Lamarin ya faru duk da cewa Matar Shugaban Ƙasa Aisha Buhari ta je majalisar da kanta a makon da ya gabata don gane wa idonta da kuma tabbatar da cewa ƙudirorin mata sun samu karɓuwa a gyaran kundin tsarin mulkin.
A yau Laraba ne 'yan majalisar za su kammala kaɗa ƙuri'a kan batutuwa kusan 60 da suka shafi gyaran ɓangarori daban-daban na kundin mulkin.
Shugaba Putin ya haramta cire kuɗi fiye da dala 10,000 a Rasha
Shugaban Rasha Vladmir Putin ya ba da umarni na hana cirar kuɗi sama da dala 10,000 a cikin ƙasar.
Wata sanarwa daga Fadar Kremlin ta ce umarnin zai fara aiki daga yau Laraba.
Darajar kuɗin Rasha na ruble ta faɗi da kashi 30 cikin 100 a kan dalar Amurka yayin da tashin hankali ke ci gaba a Ukraine.
A gefe guda kuma, babban bankin Rasha da ke ƙoƙarin guje wa sake karya darajar kuɗin ƙasar, ya ƙara yawan kuɗin ruwa daga kashi 5.9 zuwa 20.
Babban bankin na Rasha ya ware dala biliyan 630 don ba da tallafi wajen hana sayar da kadarori a wajen ƙasar da kuma taimaka wa bankuna da kamfanoni.
Hare-haren Rasha a Ukraine na ƙara tashin farashin man fetur
Yayin da ake ci gaba da fafatawa a fagen daga, faɗan na ci gaba da harzuƙa farashin man fetur a kasuwar duniya duk da ƙoƙarin da ake yi na kwantar da hankalin kasuwar.
Ɗanyen man fetur samfurin Brent - wanda ake ƙiyasta farashin mai da shi a kasuwar duniya - ya kai dala 113 kan kowace ganga ɗaya, farashi mafi yawa kenan tun 2014.
Farashin ya tashi ne duk da cewa hukumar makamashi ta duniya International Energy Agency ta amince ta saki ganga miliyan 60 ta fetur a kasuwa daga rumbunan gaggawa.
Rasha na cikin na gaba-gaba wajen samar da makashi a duniya kuma masu zuba jari na fargabar jigilar fetur da gas za ta iya samun matsala idan aka hana Rasha ci gaba da kawo kaya kasuwar.
Dakarun Ukraine sun yi iƙirarin kashe sojojin Rasha 5,840
Dakarun sojan Ukraine sun ce adadin farko-farko ya nuna cewa sun ragargaji sojojin Rasha tun bayan hare-haren da suka kai musu.
BBC ba ta iya tantance sahihancin iƙirarin nasu ba amma rundunar sojan Birtaniya ta ce dakarun na Rasha sun fusknaci mummunar ɓarna daga na Ukraine.
Jumillar adadin ɓarnar da aka yi wa sojojin Rasha sun ƙunshi abubuwa kamar haka:
- Sojoji 5,840
- Jirage 30
- Jirgin helikwafta 31
- Tanka 211
- Motoci masu sulke 862
- Makaman atilare 85
- Makaman harbo jirgi 9
- Motocin dakon man fetur 60
- Ababen hawa 355
- Maharbar makaman roka 40