Sakatare Janar na kungiyar tsaron ta NATO, Jens Stoltenberg, ya zargi
Shugaba Putin da tayar da zaune tsaye a Turai.
Shi ma Firaministan
Birtaniya Boris Johnson, ya bi sahun masu sukan Shugaba Vladimir Putin na Rasha
a kan hare-haren da dakarun Rasha ke kai wa kan birnin Kharkiv.
Yana magana ne a yayin wani taron maneman labarai na hadin guiwa tare da
Firaministan PolandMateusz Morawiecki a
babban birnin Poland din Warsaw.
Ya ce, a fili take karara, Vladimir Putin a shirye yake ya yi amfani da
dabaru na dabbanci da kan-mai-uwa-da-wabi a kan fararen hula wadanda
ba su ji ba ba su kuma gani ba a yakin da yake yi da Ukraine.
Firaministan na Birtaniya ya kuma ceduniya na ganin abin da ya kira bala'in da ke faruwaa nahiyar Turai.
Shi kuwa Firaministan na Poland cewa ya yi babban abin da za a mayar da
hankali a kansa shi ne kara sanya wa Rasha takunkumi, sannan kuma ita NATO ta
kara karfafa bangarenta na gabashi, wanda ke da iyaka da Ukraine da Rasha.
A nasa ɓangaren ministan
harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov,ya
zargi hukumomin Kyiv ne da laifin keta haddin dan-Adam a yankunan da kabilun
Rasha suke a gabashin Ukraine, ba tare da gabatar da wata sheda ba.
Haka kuma ya ce abu ne da gwamnatin Rasha ba za ta taba lamunta ba a ce
Amurka ta ajiye wasu makamanta na nukiliya a wasu kasashen Turai.