Sojojin Rasha sun yi nasarar kutsawa Kherson

Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman game da yaƙin Ukraine.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Imam Saleh

  1. Bissalam

    To jama'a a nan za mu dakata da kawo muku labaran duniyar kai tsaye a wannan rana, sai ku kasance da mu gobe Laraba don ci gaba.

    Za ku iya komawa kasa don saun labaran da muka kawo muku tsawon wannan rana.

    Nine Imam Saleh, mu kwana lafiya daga nan sashen Hausa na BBC.

  2. Majalisun Najeriya sun yi shuri da batun ba wa mata kashi 35 na kujerun siyasa

    Najeriya

    Asalin hoton, NSS

    Majalisun tarayyar Najeriya sun kada kuri’ar kin amincewa da bai wa shugabannin majalisar rigar kariya tare da yin watsi kara yawan mata a majalisun tarayyar kasar.

    An dai kada kuri'ar kan kudurorin yi wa tsarin mulkin kasar na 1999 gyaran fuska ta hanyar na’ura, inda galibin ‘yan majalisun suka sami matsaya kan abubuwan da aka rika ce-ce-ku-ce akansu.

    Tuni kungiyoyin mata suka fara nuna bacin ransu kan kin amincewa da mahimman bukatun da suka shafisu.

    Kudirori sittin da takwas ne aka kada kuri’a akansu, inda ‘yan majalisar suka ki amincewa da batun bai wa shugabannin majalisun tarayyar da cif joji-jojin kasar rigar kariya da kuma kin amincewa da bai wa mata kashi goma sha biyar cikin dari na shugabancin jam’iyyu.

    Sai dai ‘yan majalisar sun amince da bai wa kananan hukumomi ‘yan gashin kansu.

    Al’amarin da ya fi daga hankalin matan dai shi ne, a idon mai dakin shugaban kasa Aisha Muhammadu Buhari ‘yan majalsar suka yi watsi da bukatun na su.

    Nan gaba ne kuma, za a mikawa majalisun jihohi kunshin kudirorin inda suma za su kada kuri’ar amincewa da, kuma tilas sai majalisun jihohi akalla ashirin da hudu sun amince da shawarwarin kafin su zama doka.

  3. Rasha ta kai hari kan babbar hasumiyar tashar talabijin din gwamnatin Ukraine

    Ukraine

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumomin Ukraine sun ce Rasha ta kai hari kan babbar hasumiyar tashar talabijin din gwamnati da ke babban birnin kasar, Kyiv, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyar.

    Hotunan bidiyo da aka sanya a shafukan intanet sun nuna hayaki na tashi daga hasumiyar ta karfe, wadda, tana tsaye har yanzu.

    Harin ya yi sanadiyyar katsewar wasu shirye-shirye, ya kuma lalata wani wuri da ke kusa, na tunawa da wadanda suka rasa rayukansu a lokacin kisan kiyashi na 'yan Nazi.

    Isra'ila ta yi Allah-wadai da harin. Tun da farko ministan tsaro na Ukraine Oleksiy Reznikov ya yi gargadin cewa Rasha na neman ta lalata hanyoyin sadarwa, domin ta rika bayar da labaran karya cewa Ukraine na mika wuya.

    Hotunan tauraron dan-Adam sun nuna doguwar kwambar motocin yaki na Rasha, ta durfafi babban birnin Ukraine din, yayin da shi kuma ministsan tsaro na Rashar yake kira ga mutanen da ke kusa da wuraren da suka shafi harkokin tsaro a birnin na Kyiv da su bar wuraren.

    Wakiliyar BBC ta ce da tafiyar wannan katuwar kwamba da take tunkarar, babban birnin na Ukraine, abin tambaya shi ne nan da zuwa yaushe ne za ta isa bakin birnin?

  4. Shugaban Ukraine ya yi kira ga Putin ya bari a sasanta

    Zelensky

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Ukraine Voladymyr Zelensky ya yi kira ga shugaban Rasha Vladimir Putin ya dakatar da kai wa kasarsa hari.

    Yana magana ne gabanin tattaunawar sulhu ta biyu da ake sa ran bangarorin biyu za su yi gobe Talata.

    Ya ce matsawar ana son nuna wa duniya cewa tattaunawar sulhun na da muhimmanci, to ya kamata a daina kai wa juna hare-hare.

    Yayin wata tattaunawar haɗin guiwa da CNN da Reuters, shugaba Zelensky ya ce wa Putin ''Ka dakatar da kai wa jama'a hari, ka zo mu zauna a teburin sulhu a sasanta''

  5. Sojojin Rasha sun yi nasarar kutsawa Kherson

    Kerson

    Asalin hoton, Reuters

    Jami'in Ukraine sun ce dakarun Rasha sun yi nasarar kutsawa Kherson, wani gari da ke kudancin Ukraine.

    Sai dai sun ce har yanzu basu gama kwace shi ba tukunna.

    Mai ba wa ma'aikatar harkokin cikin gida ta Ukraine shawara Vadym Denysenko, ya fadawa wani gidan talabijin din kasar cewa sojojin Ukraine na ci gaba da kokarin ganin garin bai kubce daga hannunsu ba.

  6. Fargaba ta ƙaru a Ukraine bayan ganin ƙwambar motocin sojin Rasha mai tsawon kilomita 64

    motoci

    Fargaba na ƙaruwa a Ukraine a yayin da wata ƙwambar motocin sojin Rasha ta kutsa ƙasar.

    Hotunan da tauraron ɗan adam ya ɗauka a ranar Litinin syn nuna wata ƙwambar motocin sojin Rasha mai tsawon kilomita 64 na tunkaarar shiga birnin Kyiv na Ukraine.

    Wani kamfanin fasaha na Amurka Maxar ya ce hotunan sun nuna ɗaruruwan motocin soji masu sulke da tankokin yaƙi da sauran ababen hawa masu ɗauke da kayan amfani.

    Rasha na ƙara ɗaukar matakan kusten soji bayan da ƴan Ukraine suka ce sun tafka asara sosai a kwanakin farko na yaƙin.

  7. Shugaban Belarus ya tura dakaru Ukraine don taimaka wa Putin

    Alexander Lukashenko

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Ukraine Voladymyr Zelensky, ya ce shugaban Belarus Alexander Lukashenko, ya tura dakarunsa cikin Ukraine don taimaka wa na Rasha, wajen mamaye Ukraine.

    Ita ma shugabar Malalisar Tarayyar Turai Verkhovna Rada ta tabbatar da labarin, inda ta ce Belarusawan sun kutsa kai Ukraine da safiyar Talatar nan.

    Da farko dai Mista Lukashenko ya ce ba zai tura dakarunsa cikin kasar don mamaya ba.

    Rahotanni dai na cewa dakarun Rasha na ci gaba da kusantar babban birnin Kyiv sannu a hankali.

    Akwai babban aminci tsakanin shugaban na Belarus wanda shima yake fuskantar matsi daga asashen Turai da kuma shugaban Rasha Vladmir Putin.

  8. Sama da mutum 660,000 suka tsere Ukraine - MDD

    Ukraine

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce zuwa yanzu sama da mutum 660, 000 ne aka tabbatar sun tsere daga Ukraine tun bayan mamayar da Rasha ta yi wa kasar, wadanda yawancinsu yara ne da mata.

    Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar ta ce akwai rahotannin da ke nuna cewa wasu mutanen kan jira tsawon sa'a 60, a kan iyaka suna neman shiga Poland.

    A iyakar Romania layin jama'a ya kai tsawon kilomita kusan 20, na masu neman tsallakawa.

    Hukumomin Poland suna tsara gagarumin aikin jin-kai na taimaka wa 'yan gudun hijirar da ba su da inda za su zauna.

    Ana ta kafa sansanonin wucin-gadi a filayen wasa da tashoshin kwana-kwana.

    Mai magana da yawun hukumar ta ce yawan masu tsere wa rikicin na ta karuwa sosai.

    Hukumomin Poland sun ce mutum 1000 ne, suka shiga kasar a ranar Litinin yawan da ba a taba samu ba.

    Ukraine

    Asalin hoton, Getty Images

  9. Burtaniya ta ce ba za ta aika dakaru Ukraine don yin gaba da gaba da Rasha ba

    Boris Johnson

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaiministan Burtaniya Boris Johnson ya ce ƙasarsa ba za ta aika dakaru Ukraine don ƙalubalantar Rasha da ke mamayar ƙasar ba.

    Boris Johnson ya ce duk wani mataki da za su ɗauka za su ɗauke shi ne da haɗin guiwar ƙungiyar tsaro ta NATO, kuma shima ɗin bai wuce na girke dakaru a ƙasashen da ke ƙarƙashin ƙungiyar da ke maƙotaka da Rasha ba.

    ''Ina son dai in kawo karshen dukkan waɗannan maganganu da ake yi, ba zai yiwu mu yi yaƙi da Rasha ba, matakan da muke ɗauka yanzu na ƙare kanmu ne, ba ma sn mu ɗauki wani mataka da zai iya dagua al'amura'' in ji shi.

  10. Daliban Ghana sun fara isa gida Accra daga Ukraine

    daliban ghana

    Rukunin farko na daliban Ghana da aka kwaso daga Ukraine ya isa gida babban birnin kasar, Accra, kodayake har yanzu akwai sauran daruruwa da ke can kasar sun rasa ta yi.

    Daliban 17 sun yi kokari ne suka tsallaka Romania mai makwabtaka bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.

    Akwai dubban dalibai daga kasashen Afirka daban-daban da suke karatu a Ukraine.

    A ranar Litinin kungiyar Tarayyar Afirka ta yi kakkausan suka bayan wasu rahotanni da ke cewa an hana dalibai 'yan Afirka tsallaka iyaka domin tsira daga yakin da ake yi.

  11. Yadda aka tashi baran-baran tsakanin ministan ilimi da shugabannin ɗaliban Najeriya

    An tashi baran-baran a tattaunawa tsakanin ministan ilimi Adamu Adamu da shugabannin ɗalibai a Najeriya kan batun yajin aikin ƙungiyar malaman jami’a ta ASUU a Abuja.

    Ɗaliban sun zargi ministan ilimi da ficewa zauren tattaunawar bayan sun gabatar da ƙorafinsu.

    A lokacin da yake jawabi, shugaban ƙungiyar ɗaliban na Najeriya Sunday Ashefon ya faɗa wa ministan cewa ya kai ɗansa ƙasar waje karatu.

    Bidiyo ya nuna yadda shugaban yake jawabi da kuma yadda ministan ya bayar da amsa da ficewa daga zauren tattaunawar.

    “Mun gani a kafofin sada zumunta, kana biki ɗanka ya kammala karatu a ƙasar waje."

    “Iyayenmu ba su da kudin kai mu ƙasahen waje, muna son a ware kuɗi domin ci gaban ilimi a ƙasar nan.”

    “Mai girma minista muna son mu koma makaranta,” kamar yadda shugaban ɗaliban ya shaida wa Adamu Adamu.

    Ministan ya ce “abu ɗaya” da ya karba a tattaunawar shi ne batun shigar ɗalibai a tattaunawa da malaman jami’a, daga nan ya fice ya bar ɗaliban a wurin tattaunawar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Yajin aikin na gargadi da malaman jami’a suka shiga suna neman gwamnati ta aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a 2009 kan ƙarin kuɗaɗen da ake kashewa ɓangaren ilimi.

  12. Shugaban Ukraine ya sake jaddada manufar Ukraine ta shiga Tarayyar Turai

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya gaya wa majalisar dokokin Tarayyar Turai cewa kasarsa na kare 'yanci, kuma ta lamunta da duk asarar da za ta yi a yakin da take yi da Rasha.

    'Yan majalisar sun tafa tare da jinjina masa sosai a lokacin da yake jawabin wanda aka gabatar ta bidiyo.

    Mr Zelensky ya kafe cewa mutanensa ba za su karaya ba da mamayar ta Rasha, yana mai kira ga majalisa da ta bayar da dama Ukraine ta shiga Taryyar Turai.

    Ya ce a je a zo a karshe, haske zai mamaye duhu, gaskiya za ta yi galaba a kan karya.

    Tun da farko Shugaban na Ukraine ya zargi Rasha da aikata laifin yakita hanyar kaddamar da hare-haren makami masu linzami a tsakiyar birninKharkiv, inda suka kashe fararen hula dadama.

    Taron Tarayyar Turai

    Asalin hoton, EPA

  13. Shugaban Nato ya zargi Putin da tayar da zaune tsaye a Turai

    Sakatare Janar na kungiyar tsaron ta NATO, Jens Stoltenberg, ya zargi Shugaba Putin da tayar da zaune tsaye a Turai.

    Shi ma Firaministan Birtaniya Boris Johnson, ya bi sahun masu sukan Shugaba Vladimir Putin na Rasha a kan hare-haren da dakarun Rasha ke kai wa kan birnin Kharkiv.

    Yana magana ne a yayin wani taron maneman labarai na hadin guiwa tare da Firaministan PolandMateusz Morawiecki a babban birnin Poland din Warsaw.

    Ya ce, a fili take karara, Vladimir Putin a shirye yake ya yi amfani da dabaru na dabbanci da kan-mai-uwa-da-wabi a kan fararen hula wadanda ba su ji ba ba su kuma gani ba a yakin da yake yi da Ukraine.

    Firaministan na Birtaniya ya kuma ceduniya na ganin abin da ya kira bala'in da ke faruwaa nahiyar Turai.

    Shi kuwa Firaministan na Poland cewa ya yi babban abin da za a mayar da hankali a kansa shi ne kara sanya wa Rasha takunkumi, sannan kuma ita NATO ta kara karfafa bangarenta na gabashi, wanda ke da iyaka da Ukraine da Rasha.

    A nasa ɓangaren ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov,ya zargi hukumomin Kyiv ne da laifin keta haddin dan-Adam a yankunan da kabilun Rasha suke a gabashin Ukraine, ba tare da gabatar da wata sheda ba.

    Haka kuma ya ce abu ne da gwamnatin Rasha ba za ta taba lamunta ba a ce Amurka ta ajiye wasu makamanta na nukiliya a wasu kasashen Turai.

  14. Yadda ƴan Ukraine ke ɓuya a ɗakunan ƙarƙashin ƙasa da aka gina a yaƙin cacar baka

    Ukraine

    Mutane sun fara kwarara zuwa ɗakunan ƙarƙashin ƙasa na kariyar harin nukiliya da aka gina a yakin cacar baka.

    Ɗakunan na bayar da mafaka ga ɗaruruwan mutane a Ukraine a wannan lokacin da yaƙin da shugaban Rasha Vladimir Putin ya ƙaddamar ke ƙara ƙamari.

    Ukraine

    Ɗakunan asali na ma’aikatan wata masanata ne amma an daina amfani da ita da daɗewa.Ɗakunan na ƙarfe ne mai kauri, bangon ginin kuma na da kariya.

    Ukraine

    Masu agaji sun yi tanadin kayan abinci

    A dakunan da ke ƙarƙashin ƙasa an jera gado da dama masu nauyi na ƙarfe, da za su iya ɗaukar mutum 700.

    Ukraine
  15. Shugaban sojin Burkina Faso ya amince da tsarin shekara uku ga gwamnatin rikon ƙwarya

    Shugaban soji na Burkina Fasa ya amince da tsarin komawa mulkin dimokaradiya wanda zai ba shi damar ci gaba da mulki tsawon shekara uku.

    Paul-Henri Sandaogo Damiba ya sanya hannu kan tsarin wanda kwamitin da gwamnatin soji ta kafa kuma tattaunawa a wani taron kasa da aka yi a Ouagadougou.

    Yarjejeniyar ta bayyana cewa ba zai tsaya takara ba a zaben da za a yi a shekarar 2025.

    Wani shugaban jam'iyar hamayya Eddie Komboigo ya ce ba kowa ba ne zai ji dadin wannan shirin, amma an yi hakan ne bayan kowa ya amince da yarjejeniyar.

    Ana ci gaba da yi wa tsohon shugaba, Roch Kaboré, daurintalala tun bayan hambarar da shi kan mulki a watan Janairu.

    An dakatar da Burkina Faso daga kungiyar ECOWAS da kuma Tarayyar Afrika

    Paul-Henri Sandaogo Damiba

    Asalin hoton, EPA

  16. Ɗan shugaban Uganda ya bayyana goyon bayansa ga Rasha

    Lt Gen Muhoozi Kainerugaba

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan shugaba Yoweri Museveni na Uganda mai karfin faɗa a ji Janar Muhoozi Kainerugaba, ya bayyana goyon bayan Rasha kan mamayar Ukraine.

    Gen Kainerugaba - wanda kwamandan rundunar sojin Uganda ne - ya wallafa a Twitter yana cewa "yawancin al'ummar da ba fararen fata ba suna suna goyon bayan Rasha a Ukraine."

    Putin ya yi daidai! in ji shi.

    "Lokacin da Daular Soviet ta ajiye makaman nukiliya a Cuba a 1962, ƙasashen yammaci sun yi yunƙurin tarwatsa duniya saboda hakan. Yanzu idan Nato ta yi irin hakan suna tunanin Rasha za ta yi wani abu daban."

    Janar Kainerugaba shi ne babban mai muƙamin soja na farko daga Afirka da ya fito ya bayyana goyon bayansa ga Rasha.

    Ana jita-jitar shi zai gaji mahaifinsa mai shekara 77, wanda ke mulki tun a 1986.

    Ƙungiyar Ecowas ta fito ta yi Allah wadai da mamayar Rasha a Ukraine, yayin da Tarayyar Afrika ta yi kira ga Rasha ta mutunta ƴancin Ukraine.

  17. Mummunan harin makami mai linzame da aka kai a Kharkiv

    Ukraine

    Asalin hoton, Reuters

    Hotunan bidiyo sun nuna mummunan harin da aka kai a Kharkiv ɗaya daga cikin manyan biranen Ukraine.

    An kai harin ne a wani babban ginin gwamnati.

    Masu aikin agaji a Kharkiv sun ce aƙalla mutum 20 suka jikkata.

    A wani bidiyo da aka wallafa a Facebook, ma’aikatan agaji sun ce an tarwatsa wani ɓagare na ginin, yayin da kuma kuma mutane suka makale a wani ginin da ke kusa.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  18. Ghana ta fara kwaso ƴan ƙasarta daga Ukraine

    Daliban Ghana

    Ghana ta zama ƙasa ta farko daga Afirka da ta kwaso ƴan ƙasarta da suka tsere wa rikicin Ukraine bayan ƙaddamar da yaƙin da Rasha ta yi.

    Rukunin farko na ɗalibai ƴan Ghana 17 sun isa filin jirgin sama na Kotoka a Accra a ranar Talata.

    Ministan harakokin wajen Ghana tun da farko ya ce ɗalibai 460 ke kan hanyar tsallakawa zuwa Poland da Hungary da Romania da Slovakia da Jamhuriyyar Czech, ƙasashen da ke makwabtaka da Ukraine.

    Zuwa yanzu ba a san adadin yawan ƴan Ghana ba da ke Ukraine inda gwamnatin Ghana ke tattaunawa da iyayen ɗaliban domin tantance yawansu

    An ƙiyasta cewa sama da ɗaliban Ghana 1,000 ke karatu a Ukraine.

  19. Buhari yana kan hanyar zuwa Kenya kafin ya wuce London

    Shugaba Buhari

    Asalin hoton, Presidency

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana kan hanyar zuwa Nairobi babban birnin ƙasar Kenya domin halartar taron hukumar kula da muhalli ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNEP da ke cika shekara 50 da kafuwa.

    Fadar shugaban ta ce a yau Talata 1 ga Maris Buhari zai tafi Kenya domin halartar bikin hukumar UNEP na kwana uku tsakanin 3 zuwa 4 na Maris.

    Shugaban zai tafi tare da rakiyar ministocinsa na harakokin waje da na muhalli da kuma mai ba shi shawara kan sha’anin tsaro.

    Daga nan shugaban zai tafi London domin diba lafiyarsa, kuma zai shafe tsawon mako biyu, a cewar sanarwar da fadar shugaban ta fitar.

  20. Amurka ce tushen rikicin Ukraine - Ayatollah Khamenei

    Ayatollah Ali Khamenei

    Asalin hoton, EPA

    Jagoran Iran Ayatollah Ali Khamenei a cikin wani jawabi a talabijin ya taɓo batun yaƙin Rasha a Ukraine.

    A cikin jawabinsa ya ce "Ukraine ta faɗa tarkon manufofi rikici na Amurka. Muna goyon bayan kawo ƙarshen yaƙi a Ukraine, amma maganin ko wane rikici shi ne a gano tushensa. Amurka ce tushen rikici a Ukraine," in ji Khamenei.

    Ya ce “Amurka na ƙirƙirar yaƙi ne a sassan duniya domin neman kasuwar makamanta.”

    Duk da ya shafe tsawon minti ɗaya yana magana kan rikici amma Ayatollah bai ambashi Rasha ba, wadda dakarunta suka abka Ukraine.

    Ya ƙara da cewa Amurka ba abin yarda ba ce – ra’ayin da ake gani cikas ne ga tattaunawar nukiliya da Iran ke yi da manyan ƙasashen duniya kan farfado da yarjejeniyar nukiliya ta 2015.