Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Sojojin Rasha sun yi nasarar kutsawa Kherson

Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman game da yaƙin Ukraine.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Imam Saleh

  1. Tarayyar Afirka ta yi Allah wadai da wariya da ake nuna wa baƙaƙen fata a Ukraine

    Tarayyar Afrika ta ce ta damu rahotannin nuna wariya da ake nunawa ƴan Afirka a Ukraine a yayin da suke ƙoƙarin tsere wa yaƙi a ƙasar.

    Ƙungiyar ta yi kira ga dukkanin ƙasashen da abin ya shafa su mutunta dokokin duniya tare da bayar da agaji ba tare da nuna wariya ba.

    "Rahotannin wariya ga ƴan Afrika abu ne da ba za a amince ba kuma wariya ce da saɓa dokokin duniya," kamar yadda ƙungiyar ta bayyana a cikin wata sanarwa.

    Ƙungiyar ta yaba wa mambobinta da ofisoshin jekadancinsu a ƙasashen da ke makwabtaka da Ukraine kan yadda suke taimakawa mutanen da ke gujewa yaƙi.

  2. Ɗaruruwan ɗaliban Ghana sun fice Ukraine

    Kimanin ɗalibai 460 ƴan asalin Ghana suka fice daga Ukraine zuwa Poland da Hungary da Romania da Slovakia da Jamhuriyyar Czech domin gujewa yaƙi, kamar yadda ministan harakokin wajen ƙasar Shirley Ayorkor Botchweyya bayyana.

    Ana sa ran za su dawo Ghana nan da kwanaki.

    Gwamnati ta tattauna da iyayen ɗaliban a Accra fadar gwamnatin Ghana.

    Ƴan Ghana sama da 1,000 yanzu haka ke karatu a Ukraine, kuma yawancinsu sun yi ƙorafi kan yadda ake nuna masu wariya yayin da suke ƙoƙarin tserewa daga Ukraine.

  3. Najeriya za ta fara kwaso ƴan ƙasarta da suka tsallaka makwabtan Ukraine

    Najeriya za ta fara kwaso ƴan ƙasarta da suka tsallaka makwabtan Ukraine domin gujewa yaƙi, kamar yadda ministan harakokin waje ya bayyana.

    Ministan ya ce a ranar Laraba jiragen za a fara kwaso ƴan Najeriya da suke son dawowa.

    Ya ce kimanin ƴan Najeriya 5,600 har yanzu ke Ukraine, yawancinsu ɗalibai kuma ana ƙoƙarin ganin yadda za su tsallaka ƙasashe makwabta Romania da Poland da Slovakia da Hungary.

    Ukraine ta rufe filayen jiragen samanta bayan mamayar Rasha.

    Daruruwan ƴan Najeriya tuni suka fice daga Ukraine ta jiragen ƙasa da motocin bas.

    Amma ƴan Afirka sun koka kan yadda ake nuna masu wariya a iyakokin Ukraine inda ake hana masu shiga jiragen kasa da motoci da ke ɗaukar ƴan ƙasashen waje da ke ƙauracewa rikicin.

  4. An shiga kwana na shida a yaƙin Rasha a Ukraine

    An shiga kwana na shida a yakin da Rasha ta ƙaddamar a Ukraine.

    Rasha ta kai hare-hare a Kharkiv wanda ya kashe gomman fararen hula.

    Gwamnatin Ukraine ta bayyana harin na laifukan yaki.

    Kharkiv shi ne birni na biyu mafi girma a Ukraine.

    A ranar litinin wakilan Rasha da Ukraine sun yi tattaunawar sulhu a Belarus amma ba tare da cimma matsaya ba.Ɓangarorin sun amince su sake haɗuwa.

    Mutane sama da rabin miliyan suka tsere daga Ukraine, kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana.

  5. Maraba

    Muna maku maraba da kasancewa da mu a wannan shafin inda muke kawo maku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.