Rokokin Rasha sun kashe mutane 11 a Kharkiv

Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman game da yaƙin Ukraine.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Imam Saleh

  1. Kotu ta ƙi bayar da belin Abba Kyari

    Abba Kyari

    Asalin hoton, Other

    Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ki bayar da belin Abba Kyari, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda da aka dakatar.

    A ranar 14 ga Fabrairu, rundunar ƴan sanda ta miƙa Abba Kyari ga Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi (NDLEA) da ayyana tana nemansa ruwa a jallo kan badaƙalar safarar hodar iblis kilo 25.

    Kyari ne ya shigar da kara yana ƙalubalantar gwamnatin tarayya kan keta haƙƙinsa tare da bayyana safarar miyagun kwayoyi da ake yi masa a matsayin ƙage.

    Kyari ya nemi kotun tarayaya ta bayar da belinsa kan dalilai na rashin lafiya, inda lauyoyinsa suka ce yana fama da ciwon suga da hawan jini.

    Kotun bayan watsi da buƙatar belin ta kuma ɗage sauraren ƙarar da Abba Kyari ya shigar kan keta haƙƙinsa zuwa 15 ga watan Maris

  2. Shugaban Ukraine ya buƙaci Tarayyar Turai ta gaggauta amincewa da ƙasarsa mamba a ƙungiyar

    Volodymyr Zelensky

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya buƙaci ƙungiyar Tarayyar Turai da ta gaggauta amincewa da kasarsa a matsayin mambar ƙungiyar Tarayyar Turai.

    "Manufarmu ita ce mu kasance cikin ƙasashen Turai, kuma mafi mahimmanci, mu kasance a kan daidaito. N tabbata yana yiwuwa," in ji shi.

    A cikin sanarwar ta bidiyo Zelensky ya kuma bukaci sojojin Rasha da su ajiye makamansu.

    "Ku watsar da kayan aikinku, ku fice, kada ku yarda da kwamandojinku, kada ku yarda da masu yada farfaganda, ku ceci rayukanku," in ji shi.

    Shugaban na Ukraine ya kuma ce za su saki waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa masu kwarewar yaƙi domin su taimaka wajen kare kasar.

    “Mun dauki wannan matakin da ba shi da sauki, amma mai amfani ta fuskar tsaronmu,” inji shi.

  3. An fara tattaunawa tsakanin Ukraine da Rasha

    A rana ta biyar da sojojin Rasha suka shiga Ukraine, wakilan ƙasashen biyu sun fara tattaunawa domin kawo karshen yakin

    Ana tattaunawar ne kan iyakar Ukraine da Belarus

    Ukraine ta ce babban buƙatarsu sun ce ita ce tsagaita wuta da ficewar dakarun Rasha daga yankunan Ukraine.

    Tun da farko an bayyana cewa an dage zaman tattaunawar saboda batutuwa da suka shafi na tsaro.

    A cikin jawabinsa a ranar Lahadi, shugaban Ukraine Zelensky ya ce ba ya tunanin akwai wani tasiri da tattaunawar za ta yi.

    Ya ce suna son yin amfani da wannan damar ko da ƙarama ce saboda kada daga baya wani ya ɗora laifi kan Ukraine na rashin dakatar da yaƙin.

  4. Yadda ɗalibai ke zanga-zanga kan yajin aikin ASUU a Abuja

    Zanga-zangar Dalibai
    Zanga-zangar Dalibai
    Zanga-zangar Dalibai
    Zanga-zangar Dalibai
    Zanga-zangar Dalibai
  5. Zauren da za a tattauna tsakanin wakilan Rasha da Ukraine

    Belarus

    Asalin hoton, Belarus Foreign Ministry

    Belarus ta ce ta shirya zauren da za a tattauna tsakanin wakilan Rasha da na Ukraine, yayin da aka shiga kwana na biyar da yaƙin da Rasha ta ƙaddamar a Ukraine.

    Ukraine ta amince ta aika da wakilai a yankin kusa da kan iyakarta da Belarus, duk da rahotannin cewa shugaban Belarus Alexander Lukashenko zai aika da dakaru domin taimakawa Rasha.

    "An shirya zauren da za a tattauna tsakanin Rasha da Ukraine a Belarus, ana sa ran zuwa wakilai, kamar yadda ma'aikatar harakokin wajen Belarus ta bayyana, tare da wallafa hoton zauren ɗauke da tutar Rasha da Ukraine.

  6. Ofishin jekadancin Najeriya a Romania ya karɓi ƴan Najeriya 200 daga Ukraine

    Jakadiyar Najeriya a Romania da ke makwabtaka da Ukraine ta ce zuwa yanzu sun karɓi ƴan ƙasar kusan 200 yawancinsu ɗalibai da suka tsallako Bucharest babban birnin ƙasar daga Ukraine.

    Safiya Nuhu ta shaida wa BBC cewa suna kyautata zaton samun adadin ƴan Najeriyar fiye da haka da ke tserewa daga Ukraine.

    “Mun tarbe su kuma mun ba su masauki a otel otel a Bucharest,” in ji ta.

    Ɗaruruwan ƴan Najeriya ne suka tsallaka kan iyakar Ukraine, inda ake sa ran kwashe su zuwa birane mafiya aminci, kafin mayar da su Najeriya.

    Sai dai yawancinsu da sauran ƴan Afirka sun yi ƙorafi kan yadda ake nuna masu wariya a kan iyakar Ukraine da Poland.

    Ga ƙarin bayanin da Hajiya Safiya Nuhu ta yi wa BBC:

    Bayanan sautiOfishin jekadancin Najeriya a Romania ya karɓi ƴan Najeriya 200 daga Ukraine
  7. Najeriya ta ce ana nuna wa ƴan ƙasarta wariya da ke neman ficewa Ukraine

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda rahotanni suka nuna ana nuna wa wasu ƴan Najeriya wariya da ke yunkurin ficewa daga kasar Ukraine.

    Kimanin ‘yan Najeriya 4,000 ne har yanzu ke maƙale a Ukraine.

    A cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar a Twitter, ta ce jami'an tsaro da 'yan sandan Ukraine sun ƙi barin ƴan Najeriya su shiga bas da jiragen kasa da ke kan iyakar Ukraine da Poland.

    “Wanirukuni na ɗaliban Najeriya da aka hana su shiga ƙasar Poland sun yanke shawarar cewa ba su da wani zabi illa su sake ratsa Ukraine domin yunkurin ficewa daga ƙasar ta kan iyakar kasar da Hungary,” in ji sanarwar.

    Ofishin Buhari ya ce ya kamata a mutunta duk ƴan kasashen waje da ke koƙarin tsallakawa zuwa kasar Poland ba tare da nuna bambanci ba.

    Sanarwar ta ce "Duk waɗanda suka guje wa wani rikici na da 'yancin shiga cikin aminci a karkashin yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kuma bai kamata a nuna bambanci ba kan fasfo dinsu ko launin ba."

    Yan Najeriya

    Asalin hoton, AFP

  8. Ɗalibai na zanga-zanga kan yajin aikin ASUU a Kano

    Dalibai a Kano

    Ɗalibai a Najeriya sun fito zanga-zanga a Kano domin nuna rashin jnn daɗinsu kan yajin aikin da ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU.

    Sun fara tattakin ne daga karkashin kofar Nasarawa, sannan suka shiga gidan Murtala don isar da sakonsu ga Kwamishinayar da ke kula da manyan makarantu.

    Zanga-zangar Dalibai

    An samar da jami’an tsaro na DSS da ƴan Sanda daga ƙofar Nasarawa zuwa dukkan mahaɗa ta zuwa gidan gwamnatin Kano, da karkashin gadar Nasarawa.

    Tun a makon jiya ƙungiyar ɗaliban ta ƙasa NANS ta ce za ta ƙaddamar da zanga-zanga a manyan biranen Najeriya kan yajin aikin ASUU.

  9. Darajar kuɗin Rasha ta faɗi

    Shugaban Rasha

    Asalin hoton, ANADOLU AGENCY VIA GETTY IMAGES

    An soma ganin tasirin takunkuman da Amurka da ƙasashen Tarayyar Turai suka ƙaƙaba wa Rasha.

    A yau Litinin, darajar kuɗin Rasha na rubble a kasuwannin nahiyar Asiya ta faɗi da kashi uku bisa huɗu

    Farashin ɗanyen mai ya yi sama da kusan kashi huɗu cikin 100.

    Hukumomi a Tarayyar Turai sun ce wasu kamfanoni mallakar Rasha da ke cikin ƙasashensu musamman Sberbank wanda banki ne mallakar Rasha na daf da samun karayar arziki.

    Babban bankin Tarayyar Turai ya ce Sberbank wanda yake a Croatia da Slovenia ya shiga mawuyacin hali sakamakon yadda jama'a suka yi ta zare kuɗaɗensu.

    Tuni ƴan ƙasar Rasha ke bin dogayen layuka sakamakon fargabar da suke yi na cewa katin bankinsu zai daina aiki kuma za a iya ƙayyade adadin kuɗin da mutum zai iya cira daga banki.

  10. Dakarun Rasha sun kwace birnin Berdyansk

    Birnin Berdyansk da ke kudancin Ukraine ya faɗa hannun ikon Rasha, kamar yadda magajin garin ya bayyana.

    Dakarun Rasha sun shiga birnin ne da yammacin Lahadi, kuma an gansu suna sintiri a tsakiyar birnin, kamar yadda magajin gari Alexander Svidlo ya bayyana a Facebook.

    A cewarsa; “Rasha sun bayyana mana dukkanin gine-ginen gwamnati suna ƙarƙashin ikonsu.”

    “ƙarƙashin ikon masu riƙe da makamai, manufar da ba mu amince ba, don haka dukkaninmu mambobin da ke hedikwatar, mun fice daga ginin,” in ji shi.

  11. An shiga kwana na biyar na mamayar Rasha a Ukraine

    Yakin Rasha a Ukraine

    Asalin hoton, Reuters

    Biranen Ukraine na ci gaba da kasancewa cikin shirin ko ta kwana a daidai lokacin da ƙasar ake ci gaba da gwabza fada da Rasha kan mamayar ƙasar.

    Rundunar sojin Ukraine ta ce a ranar Litinin sojojin Rasha sun yi ta yunƙurin kutsawa wajen babban birnin kasar, amma sun kasa kama shi.

    Manyan biranen Ukraine na Kyiv da Kharkiv da Chernihiv sun fuskanci hare-hare cikin dare.

    Dukkanin manyan biranen suna hannun ikon dakarun Ukraine, sojojin Rasha sun kutsa a kudanci inda suka karbi wani yanki na Berdyansk.

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi gargaɗin cewa sa’o’i 24 za su kasance masu ‘muhimmanci’

    Ukraine ta ce tattaunawa da Rasha za ta kasance ba tare da wani sharaɗi ba a kan iyakarta da Belarus. A ranar Litinin za a fara tattaunawar, kamar yadda mai magana da yawun shugaban Ukraine da kamfanin dillacin labaran Rasha na Tass suka bayyana.

  12. Maraba

    Muna maku maraba da kasancewa da mu a wannan shafin inda muke kawo maku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.