Tarayyar Turai za ta bunkasa Afirka da dala biliyan 170

Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman a Najeriya da Nijar maƙotansu.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Rikicin Ukraine: Rasha na shirin fara atisayen soja da Belarus

    Rasha

    Asalin hoton, Getty Images

    Rasha ta fara atisayen soja na kwana 10 tare da Belarus ana tsaka da fargabar girke dubban dakarunta a iyakar Ukraine.

    Ana sa ran sojojin Rasha 30,000 ne za su shiga atisayen, sai dai mataimakiyar ministan tsaro Ganna Malyar ta ce babu alamun sojojin sun zo da niyyar tayar da husuma.

    "Kan halin da ake ciki a bakin iyakarmu, muna iya ganin dandazon sojojin da suka mayar da hankali kan kafa kayan yaki, amma yanzu babu wannan, babu wata alamar barazana," a cewar ministar.

    Belarus babbar ƙawar Rasha ce kuma tana da iyaka mai tsayi da Ukraine ta kudanci.

    Amurka ta bayyana atasayen - wanda ake ganin shi ne mafi girma da Rasha za ta yi a Belarus tun bayan yaƙin cacar baka - a matsayin "na tsokana".

  2. Assalamu alaikum

    Barkanmu da hantsin Alhamis tare da fatan kun tashi lafiya.

    Ku kasance tare da mu a tsawon yinin yau don sanin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da maƙotansu.

    Umar Mikail ne ke tare da a wannan safiya.

  3. Firaministan Libya ya sha da ƙyar bayan harin 'yan bindiga

    Libya

    Asalin hoton, Reuters

    Firaministan Libya Abdulhamid al-Dbeibah ya tsallake rijiya da baya a yunkurin hallaka shi da wasu 'yan bindiga suka yi.

    An yi wa motarsa ɓarin harsasai a lokacin da yake tafiya a birnin Tripoli da safiyar yau Alhamis, amma ba a yi nasarar kama su ba.

    Ana ta samun tashin hankali tsakanin kungiyoyin da ba sa jituwa da juna a Libya kan wanda ya dace ya jagoranci kasar.

    Nan gaba a yau ne 'yan majalisa a gabashin ƙasar za su kaɗa ƙuri'ar wanda zai maye gurbin Mista al-Dbeibah, kodayake ya ce ba zai amince da sakamakon kuri'ar ba.