Gobara ta lakume dukiya mai dimbin yawa a Unguwar-Guragu da ke Abuja

Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman a Najeriya da Nijar maƙotansu.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Korona ta sake kama mutum 58 a Najeriya

    Hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya ta ce an samu ƙarin mutum 58 da suka kamu da cutar korona ranar Talata.

    Jihohin da mutanen suka fito bakwai ne da suka haɗa da Legas (35) da Abuja babban birnin ƙasar (9) da Edo (5) da Delta (4).

    Sauran su ne Kano (2) da Rivers (2) da Kaduna (1). Rahoton na NCDC ya nuna babu wanda cutar ta kashe a Talatar.

    Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 253,833 ne suka harbu da cutar a Najeriya tun bayan ɓullarta a Fabarairun 2020. Kazalika ta yi ajalin mutum 3,139.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  2. 'Yan sandan Kanada sun fara kama masu zanga-zangar dokar korona

    Kanada

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyoyin 'yan kasuwa 60 na Kanada da Amurka sun yi kiran a kawo karshen zanga-zangar da ta haddasa babbar hanyar da ta hada kasashen biyu wajen fuskar kasuwanci da masu zanga-zanga suka rufe.

    'Yan sanda sun fara kama masu zanga-zangar yayin da kashi 25 cikin 100 na motocin da ke cikin cunkoson ababen hawa ke ɗauke da yara ƙanana a cikinsu.

    Da take magana da BBC, mataimakiyar magajin garin Ottawa Laura Dudas ta bayyana matakin da hukumomi ke dauka.

    "Shugaban 'yan sandan Ottawa ya bayyana karara muna bukatar karin jami'an tsaro, muna rokon gwamnatin tarayya ta kawo mana ɗaukin 'yan sanda 18,000 domin shawo kan matsalar masu zanga-zangar nan," in ji ta.

    Lamarin ya fara ne tun ranar 9 ga watan Janairu lokacin da matuƙa manyan motocin suka fara nuna ɓacin rai game da dokar da ta tilasta musu yin rigakafin korona kafin su tsallaka iyakar Amurka da Kanada.

  3. Ina kwananku

    Barkanmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa, wanda zai kawo muku rahotanni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Umar Mikail ne ke muku barka da hantsin Laraba.

    Ku biyo mu!