Yarjejeniyar Iran da ƙasashen Yamma na barazanar rugujewa

Asalin hoton, AFP
Jami'an diflomasiyya daga Birtaniya da Faransa da Jamus sun yi gargadin cewa yarjejeniyar nukiliya ta 2015 na cikin hatsarin "rugujewa idan aka yi la'akari da yadda Iran ke hanzarta shirinta na nukiliya".
Sun ce suna bai wa Iran ɗin lokaci a tattaunawar da suke yi a Vienna saboda tana aiwatar da wasu abubuwa da suka saba wa yarjejeniyar.
Wakiliyar BBC ta ce a ganinsu Iran na jan kafa ne a tattunawar da suke yi domin ta kara inganta shirin nukliyarta.
Sai dai jakadan Iran a Biritaniya, Mohsen Baharvand, ya shaida wa BBC cewa har yanzu Iran din na da aniyar aiwatar da ka'idojin yarjejeniyar da ta cimma da kasashen Yamma.


