Ana shirin ɗaukar ƴan banga don gadin makarantun Abuja

Asalin hoton, Other
Hukumomin birnin Tarayya Abuja na Najeriya sun ce suna shirin ɗaukar ƴan banga domin gadin makarantu saboda barazanar tsaro da ake fuskanta.
Jaridar The Punch ta ambato daraktan gudanarwa a ɓangaren tsaro na hukumar birnin na tarayya yana cewa an riga an kammala shirin ɗaukar ƴan banga da za su tabbatar da tsaron makarantu a faɗin yankin na Abuja.
Wannan zuwa ne biyo bayan wasu rahotanni na tsaro da ke cewa ƴan bindiga daga jihohin da ke makwabtaka da Abuja na tsallakowa zuwa birnin na tarayya.
Ƴan bindiga sun sha kai hare-hare makarantu suna satar ɗalibai a yankin arewa maso gabashi, kuma ana ganin satar mutane ta dawo a hanyar Kaduna zuwa Abuja.
A makon da ya gabata gwamnatin Neja da ke makwabtaka da Abuja ta yi gargaɗin cewa mayaƙan Boko Haram sun mamaye wasu yankuna na jihar.
