Buhari ya ce zai hukunta masu daukar ma'aikatan boge da cushen albashi

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Badariyya Tijjani Kalarawi

  1. Korona ta kama ƙarin mutum 21 a Najeriya

    Hukumar ɗakile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya ta ce an samu ƙarin mutum 21 da suka kamu da cutar korona a Najeriya.

    Alƙalumman sun nuna mutum shida suka kamu da cutar a Legas, jihar da cutar ta fi bazuwa, sai a jihar Cross Rivers da aka samu mutum biyar a ranar Litinin.

    A jihar Rivers an samu mutum biyar, sai jihar Ondo mai mutum uku. A Kaduna ƙarin mutum ɗayaaka samu haka ma a Bauchi.

    Yanzu jimillar mutum 214,113 cutar ta shafa a Najeriya amma 207,297 sun warke yayin da cutar ta kashe mutum 2,976 a Najeriya.

    Ga jihohin da aka samu ƙarin cutar a Najeriya a ranar Litinin.

    Lagos-6

    Cross River-5

    Rivers-5

    Abia-3

    Bauchi-1

    Kaduna-1

  2. Maraba

    Muna maku maraba da kasancewa da mu a wannan shafin da za mu kawo maku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.