Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An harbe wani malamin addinin Musulunci a Uganda

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Jabir Mustapha Sambo

  1. 'Tashin farashin kayan abinci ka iya jefa ƙarin 'yan Najeriya miliyan 6 cikin talauci'

    Tashin farashin kayan abinci da sauran kayan amfanin yau da kullum ka iya jefa ƙarin 'yan Najeriya fiye da miliyan shida cikin talauci, a cewar sabon rahoton Bankin Duniya.

    Rahoton wanda aka wallafa a watan Nuwamba game da tasirin annobar korona ya bayyana cewa hauhawar farashin kayan na ingiza mutane cikin talauci, abin da ya sa ya yi kira ga gwamnatin Najeriya ta ƙara girman shirin taimaka wa al'umma.

    "Tashin farashin kaya da aka fuskanta daga watan Yunin 2020 zuwa Yunin 2021 zai iya jefa ƙarin wasu 'yan Najeriya miliyan shida cikin talauci, yayin da abin da zai fi shafar birane; hakan na nufin akwai buƙatar wani shiri na gajeren lokaci domin a tallafa wa walwalar jama'a," kamar yadda rahoton ya nuna.

    A 2019, Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ta ce mutum miliyan 82.9 ne ke cikin talauci a ƙasar. Sai dai a 2021 adadin ya kai miliyan 90.

    Kazalika, rahoton ya yi hasashen cewa hauhawar farashin ka iya ƙara yawan mutanen da ke rayuwa a adadin kuɗi mafi ƙaranci zuwa kashi 42.8 daga 40.1 cikin 100.

  2. Ambaliyar ruwa ta ɗaiɗaita British Columbia na Canada

    An ayyana dokar-ta-ɓaci a lardin British Columbia na kasar Canada da ke fama da mamakon ruwan sama da ya haddasa ambaliya da zabtarewar kasa.

    Firaminista Justin Trudeau ya ce an aike ɗaruruwan sojoji lardin domin ayyukan ceto, yayin da dubban mutane suka maƙale.

    Ma'aikatan agaji sun shafe awa 17 wajen ceto mutum 275.

    Magajin Gari Henry Braun ya ce: "Akwai jan aiki a gabanmu, yanzu mun mayar da hankali wajen ceto rayuka.

    "Ruwa ya lalata Tittuna, hanyoyi sun katse na kai wa ga garuruwan da ke kan tsauni, kuma babu ta inda za a kai ga tashar jirgin ruwa mafi girma ta kasar, Vancouver."

    Kawo yanzu mutum ɗaya aka tabbatar ya mutu, sai dai ana hasashen mutane da dama sun rasa rayukansu.

  3. Ƙarin mutum 82 sun kamu da cutar korona a Najeriya

    Hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya ta ce an samu ƙarin mutum 82 da suka kamu da cutar korona ranar Laraba.

    Cikin rahoton da ta wallafa, NCDC ta ce mutanen sun fito ne daga a jiha takwas.Jihohin su ne:

    • Rivers-52
    • Kano-9
    • Kebbi-6
    • Kaduna-5
    • Plateau-5
    • Enugu-3
    • Bauchi-1
    • Lagos-1

    Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 213,403 ne suka harbu da cutar, sannan ta kashe mutum 2,973. Sai dai an sallami 206,245 daga asibitoci bayan sun warke.

  4. Marabanku

    Barkanmu da hantsin Alhamis.

    Umar Mikail ne ke cewa ku biyo mu a wannan shafi domin samun rahotannin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar maƙotansu.