Rufewa
Masu karatu anan zamu rufe shafin namu na kai-tsaye a yau.
Amma ku sake shigowa gobe da safe don karanta sabbin labaran da zamu wallafa muku.
Jabir Mustapha Sambo na ke cewa mu kwan lahiya!
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya.
Umar Mikail and Jabir Mustapha Sambo
Masu karatu anan zamu rufe shafin namu na kai-tsaye a yau.
Amma ku sake shigowa gobe da safe don karanta sabbin labaran da zamu wallafa muku.
Jabir Mustapha Sambo na ke cewa mu kwan lahiya!
Ƴan sanda a kudancin Brazil sun kama wata ƙungiya da ta yanka wasu dawaki da aka sato, kuma ta sayar wa gidajen abinci namansu a matsayin na shanu.
Ƴan sanda sun saurari hirar mambobin ƙungiyar inda suka gano cewa suna amfani da ruɓaɓɓen nama wajen sa wa a biredin burger.
Kungiyar na aiki ne a jihar Rio Grande do Sul, a kan iyakokin Brazil da Uruguay da Argentina, inda ake alfahari da ingancin namansu na shanu da kuma tsayuwa kan al'adar kin cin naman doki.
Sanannun tagwayen mawakannan a Najeriya Peter and Paul da aka fi sani da P-Square sun sanar da cewa sun shirya.
P-Square sun ce sun shirya tsakaninsu, bayan wani rikicin cikin gida da ya raba kansu a shekarar 2017.
A 2015 P-Square suka lashe kyautar mawaka mafi shahara a bikin MTV Africa.
To amma duk da shiryawar tasu, tagwayen basu bayyana ko za su sake fito da sabon kundi wakoki tare ba.
Sai dai magoya bayansu na fatan su tsantsara musu sabbin wakoki tare, kamar yadda suka yi fice da wakoki kamar 'Do me' da 'Chop My Money' da kuma 'Bizzy Body'.
Babu bayani kan ainahin abinda ya haddasa rikici a tsakanin yan biyun, kuma duk wani yunkurin shirya su a baya ya gagara.
A shafinsu na Instagram yau Alhamis Peter da Paul sun rubuta "biyu tafi daya."
Jami'ai a Uganda sun ce jami'an tsaron ƙasar sun harbe wani malamin addinin Musulunci Sheikh Muhammad Abas Kirevu wanda suka ce yana da hannu wajen ɗaukar mutanen da za su shiga cikin kungiyar ta'addanci ta 'yan tawayen Allied Democratic Front.
Hukumomin kasar sun danganta kungiyar ADF da hare-haren ƙunar bakin wake da aka kai a Kampala babban birnin ƙasar.
Kungiyar IS ta ce ita ce ta kai hare-haren na ranar Talata da ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutane hudu.
'Yan sanda sun ce tun daga lokacin an kama sama da mutane 20 - ciki har da mutane da dama da ke kokarin tsallakawa kan iyaka zuwa gabashin Congo yankin da ƙungiyar ADF ke gudanar da ayyukanta.
Ana ci gaba da farautar Sheik Suleiman Nsubuga wanda ake zargi da horar da 'yan tawayen da kuma samar da ababen fashewa.
Gwamnatin Djibouti ta ce yaƙin da aka ɗauki shekara ɗaya ana yi a maƙwabciyarta Habasha ya yi mummunan tasiri kan tattalin arziƙinta.
Kusan kashi casa'in cikin ɗari na kayan Ethiopia na bi ta tashar jirgin ruwa a Djibouti, kuma ƙasashen biyu sun zuba biliyoyin daloli wajen gina hanyar cinikayya.
Ministan kuɗin Djibouti, Ilyas Moussa Dawaleh ya shaida wa BBC cewa dalilin rikicin, kasuwanci ya ragu da kusan kashi 20 cikin ɗari na yadda yake a baya.
Ya ce ƙasar ta yi asarar dala biliyan ɗaya da miliyan ɗari bakwai.
A baya-bayan nan ƴan tawayen Tigray sun yi ta ƙoƙarin ƙwace garuruwa a yankin Afar, matakin da ga dukkan alamu wani yunƙuri ne na datse hanyar kasuwanci mai muhimmanci tsakanin Ethiopia da Djibouti.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjina wa Amurka bisa rawar da take takawa wurin yaki da ta'addanci a kasarsa.
Shugaban ya fadi haka ne yayin karbar bakunci sakataren harkokin wajen Amurkar Antony Blinken, wanda ke gudanar da ziyarar aiki ta kwanaki uku a Abuja.
Sanarwar wadda mai bai wa Shugaban shawara kan yada labarai Femi Adesina ya fitar ta ce "shugaba Buhari na gode wa Amurka da bai wa Najeriya damar mallakar makamai don yakar ta'addanci, da kuma horon da take bai wa sojojinta na sanin dabarun yaki."
Kan batun cire Najeriya daga jerin kasashen da ke hana yancin gudanar da addini, shugaba Buhari ya jinjina wa Amurka, inda ya ce kasarsa na bai wa kowa damar gudanar da addinin da yake so ba tare da tsangwama ba.
A nasa bangaren Mr Blinken ya jinjina wa Shugaban Najeriyar kan alkawarin ba da gagarumar gudummawa wurin yakar matsalar dumamar yanayi, a lokacin taron sauyin yanayi da aka yi na COP26 a birnin Glasgow na Scotland.
Ya kuma ce kan sha'anin tsaro, kasashen biyu za su kara hada hannu don ganin sun gudu tare sun tsira tare.
Ana sa ran sakataren harkokin wajen Amurkar zai shafe kwanaki uku a Najeriya.
Hukumomi a Kenya sun ce an cafke wasu ƴan bindiga uku kwanaki bayan sun tsere daga wani gidan yari mai tsananin tsaro.
Shugaban hukumar binciken kasar ya ce an cafke su ne yayin da suke ƙoƙarin tsallakawa Somaliya.
Cikin fursunonin har da Mohamed Ali Abikar, wanda aka yanke wa hukunci kan hari da aka kai a jami'ar Garissa shekaru shidda da suka gabata.
Harin na jami'ar ya yi sanadin rayuka 150 da kuma jikkatar dalibai da dama.
A Ranar Laraba ne Shugaba Uhuru Kenyatta ya dakatar da shugaban hukumar gidajen yarin Kenya daga aiki.
Kungiyar mata masu wasan ƙwallon tennis ta ce duniya na buƙatar sahihiyar shaidar cewa ƴar wasan ta ƙasar China, Peng Shuai na nan cikin ƙoshin lafiya.
Ƴar wasan ƙwallon teburin ta ɓata ne bayan da ta zargi wani tsohon Shugaba a ƙasar da tursasa mata yin lalata da shi.
To amma har yanzu China ta ƙi cikakken bayani kan lamarin.
A ranar Alhamis mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje ya ce ba shi da masaniya kan lamarin.
Ya ce batun batan Ms Shuai ba batu ne na harkokin kasar waje ba, kuma China ba ta masaniya kan wannan batun da ake yi.
Kungiyar mata masu wasan ƙwallon tennis ta ce ta samu wani saƙon email da ake tunanin Ms Peng ce ta aiko dashi inda ta ce tana nan lafiya.
Sai dai kungiyar ta ce tana da shakku kan ko itace ta rubuta saƙon da kanta.
Wani babban kwamitin Kotun ƙoli a Indiya ya bayar da shawarar naɗa wanda ya fito ya bayyana cewa shi ɗan luwaɗi ne a matsayin alƙali, a wani abin da aka bayyana a matsayin “ci gaba” ga ƴancin masu neman jinsi ɗaya, kamar yadda ƴar jarida mai bayar da rahoto kan harakokin shari’a Suchitra Mohanty ta ruwaito.
Kwamitin da babban mai shari’a na ƙasar ke jagoranta ya bayar da sunan Saurabh Kirpal domin zama alƙalin Babbar Kotun Delhi.
Shawarar babban kwamitin shari’a na daga cikin matakan naɗa Alƙali a India kafin daga baya matakin ya samu amincewar gwamnati.
An yi imanin cewa gwamnatin Firaminista Narendra Modi za ta amince da naɗin Mista Kirpal a makwanni masu zuwa.
A 2018, Kotun ƙolin ƙasar ta ɗage haramcin luwaɗi da Maɗigo a wani hukuncin da aka bayyana babbar nasara ga masu neman jinsi ɗaya. Kuma Mista Kirpal shi ne lauyan da ya kare shari’ar da aka shigar.
Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken, ya yi Allah-wadai da yadda ake muzguna wa masu zanga-zangar goyon bayan dimokraɗiyya a Sudan haka kuma ya yi kira da a mayar da firai ministan da aka hamɓarar da Abdalla Hamdok kan mulki.
A ranar Laraba, an kashe mutum 15 inda aka raunata gwammai a lokacin da jami'an tsaro suka buɗe wuta kan jama'ar da ke zanga-zanga nuna ɓacin rai kan waɗanda suka jagoranci juyin mulki a watan da ya gabata.
A wata hira da BBC Mista Blinken wanda a halin yanzu yake wata ziyarar aiki a anhiyar Afrika wadda irinta ce ta farko, ya yi kira da a saki fursunonin siyasa haka kuma akwai buƙatar shugabannin sojojin ƙasar su saurari jama'a.
Shugaban hukumar kare haƙƙin ɗan Adam na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ya yi Allah wadai da amfani da harsashi mai kisa da sojojin Sudan suka yi a kan masu zanga-zanga.
Rahotanni na cewa jami'an tsaro sun kashe mutum 15 ranar Laraba daga cikin 'yan zanga-zangar, yayin da suke ci gaba da nuna ƙin jinin gwamnatin sojan ƙasar.
"Abin kunya ne matuƙa a ce an sake yin amfani da harsashi mai kisa jiya (Laraba) a kan masu zanga-zanga," kamar yadda Michelle Bachelet ya bayyana a cikin wata sanarwa da AFP ya ruwaito.
A ranar 25 ga watan Oktoba ne Janar Abdel Fatah Al-Burhan ya jagoranci juyin mulki na baya-bayan nan, inda ya hamɓarar da gwamnatin riƙon ƙwarya ta farar hula ƙarƙashin jagorancin Abdalla Hamdok.
Gwamnatin Najeriya ta yi lale marhabin da matakin gwamnatin Amurka na cire kasar daga sahun wadanda take yi wa kallon masu tauye ‘yancin yin addini.
A cikin wata sanarwa, Ministan Yaɗa labaran Najeriya Lai Mohammed ya kira matakin na Amurka a zaman na adalci.
A jiya ne Amurkar ta cire sunan kasar daga jerin ƙasashen da take zargi da tauye yancin addini kwana ɗaya kafin Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya isa Najeriyar a yau Alhamis.
'Yan sanda da ke yaƙi da ta'addanci a Indonesia sun kama wani babban malamin Musulunci, Ahmad Zain An-Najah, da ake zargi na tarawa wata kungiyar ta'addanci da ke da alaka da al-Qaeda kudade.
An daura alhakin harin bam da aka kai a wani gidan rawa a shekarar 2002 wanda ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 200 da sauran kazaman hare-hare kan kungiyar Jemaah Islamah.
'Yan sanda sun ce an kama Ahmad Zain An-Najah a kusa da birnin Jakarta, wanda mamba ne a majalisar malaman Indonesia.
Yana yi wa wata kungiyar agaji wadda kungiyar Jemaah ta kafa kan ilimi da ayyukan walwala jama'a aiki, sai dai 'yan sanda na zargin kudaden da yake tarawa ana amfani da su wajen ayyukan ta'addanci.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken, ya yi tir da murkushe masu zanga-zangar neman tabbatar da mulkin dimokuradiyya an Sudan kuma ya jaddada kira domin mayar da firaiministan da aka hambarar, Abdalla Hamdok, a kan mulki.
Ranar Laraba an harbe mutum 15 sannan aka jikkata da dama daga cikin masu zanga-zangar lokacin da jami'an tsaro suka bude wuta kan dandazo masu gangamin adawa da juyin mulkin da sojoji suka yi a watan jiya.
A wata hira da BBC Mr Blinken, wanda yake ziyararsa ta farko tun bayan hawa kan mulki, ya yi kira a saki fursunonin siyasa sannan ya ce ya kamata shugabannin sojoji su saurari bukatun 'yan kasar Sudan.
Nan gaba kadan ne za a yi jana'izar mutanen da suka mutu.
An kammala gasar karatun Alkur'ani mai girma da Rundunar 'Yan sanda ta Jihar Kano ta shirya tsakanin jami'anta.
Shugaban Ofishin 'Yan Sanda na Takai, DPO Mahi Ahmad Ali, shi ne ya zo na ɗaya a ajin izu 60, inda ya samu kyautar sabon firji da sauran kyautuka.
Musabaƙar wadda aka fara ranar Laraba, ta ƙunshi dakaru kuma mahaddata da suka fafata a matakin izu 60 da 40 da 5 da 2.
Sai kuma ASP Salihu Ismail, wanda ya zama gwarzo a ajin izu 40.
Ɗan Amar ɗin Kano Aliyu Harazumi wanda ya wakilci sarkin Kano a wurin taron, ya bai wa Kwamishinan 'Yan Sandan Kano Samaila Dikko kyauta ta musamman kasancewar a ƙarƙashin jagorancinsa ne aka gudanar da gasar karon farko.
Shugaban hukumar yaƙi da rashawa a Najeriya (EFCC) ya musanta rahotannin da ke yawo cewa akwai rigar mama ta gwal a cikin kayan da hukumar ta ƙwace daga hannun Diezani Alison-Madueke, tsohuwar ministar man fetur ta Najeriya.
Ana zargin Diezani wadda ta fice daga Najeriya a 2015 da satar kuɗin da suka kai dala biliyan biyu da rabi daga asusun gwamnatin ƙasa a lokacin da take minista, kodayake ta musanta zargin.
A watan Mayu ne Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa ya faɗa wa Majalisar Wakilai cewa darajar sarkoki da awarwaro da sauran kayan ƙawa da aka ƙwace daga wurin Diezani ta kai naira biliyan 14.
A watan Oktoba gwamnatin tarayya ta lissafa wasu kadarorinta da ta ƙwace waɗanda suka haɗa da gidaje a Banana Island da ke Ikoyi ta Jihar Legas.
Sai dai da ya bayyana a kafar talabijin ta TVC ranar Laraba, Abdulrasheed Bawa ya ce labarin rigar mama ta gwal da aka ce akwai ta a cikin kayan na ƙanzon kurege ne.
"Babu wani abu mai kama da rigar mama ta gwal, maganar 'yan kafafen sada zumunta ce," in ji shi.
"Zan iya faɗa muku a kyauta saboda ni ne jagoran wannan binciken. Ban san da ita ba. Idan da akwai ta ya kamata a ce na sani. Ya kamata na sani saboda ni na jagoranci binciken da sauransu."
Likitoci a Sudan sun ce jami'an tsaro sun harbe mutum 14 ranar Laraba yayin da dubban 'yan ƙasar ke ci gaba da hawa tituna domin yin zanga-zangar ƙin jinin gwamnatin soja.
'Yan gwagwarmaya sun yi kira ga mutane da su fito gagarumar zanga-zangar a ranar Laraba, wadda ya kamata sojojin su miƙa mulki ga Majalisar Mulki ta Farar hula kamar yadda aka tsara tun farko.
Janar Abdel Fattah al-Burhan ne ya jagoranci juyin mulkin a watan da ya gabata, inda ya kori gwamnatin riƙon ƙwarya kuma ya kama gwamman jami'anta tare da naɗa kansa a matsayin shugaban sabuwar gwamnati ta sojoji.
Hujjoji na ƙara fitowa kan irin rashin imanin da sojojin Sudan ke nunawa.
Likitoci a birnin Khartoum na cewa an harba hayaƙi mai sa hawaye a asibitoci sannan sojoji sun hana a kula da wasu da aka raunata.
Kazalika, an kama mutane da dama a unguwannin da aka katse wa wutar lantarki.
Dubban ma'aikatan hukumar zirga-zirgar jiragen ƙasa a Najeriya sun tsayar da ayyuka cak a faɗin ƙasar domin matsa wa gwamnati ta ƙara musu albashi da kuma kula da walwalarsu.
Tuni tashoshin jirgin suka kasance a rufe, yayin da wakilin BBC Umar Rayyan ya tarar da ma'aikatan ɗauke da kwalaye suna zanga-zanga a tashar jirgi ta Idu da ke Abuja wadda ke danganewa da Jihar Kaduna.
Ana sa ran hukumar Nigeria Railway Corporation (NRC) za ta yi asarar miliyoyin naira yayin yajin aikin na kwana uku.
Ma'aikatan sun ce za su fara yajin aikin ne daga safiyar yau Alhamis, 18 zuwa 21 ga watan Nuwamba a matsayin gargaɗi ga gwamnati.
Sai dai hukumar ta ce yanzu haka tana kan tattaunawa da ƙungiyoyin ma'aikatan domin sasantawa.
A yau Alhamis ake sa ran Sakataren harkokin Waje na Amurka Anthony Blinken zai isa Abuja, babban birnin Najeriya.
Albarkacin zuwan nasa, an wayi gari Amurkar ta cire Najeriya daga jerin kasashen da take zargi da tauye 'yancin addini.
Labarin cire Najeriya daga cikin ƙasashe shida wadanda a shekara ta 2020 Amurkar ta yi musu lamba ta kasancewa wadanda suke tauye 'yancin addini labari ne da zai dadada wa hukumomin kasar.
Mista Blinken na ziyara ne karon farko a nahiyar Afirka, inda yake ziyartar Kenya da Senegal da Somalia.
Babu dai wata sanarw karara da ta bayyana matakin ƙasashen suka ɗauka kan abin da ya kai ga zare sunan Najeriyar daga kasashen da Amurkar ta sanya a cikin jerin.
Sanarwar da Amurkar ta fitar ranar Laraba ce ta tabbatar da cire ƙasar sakamakon zare sunanta daga jerin ƙasashen da Amurkar ta sa cikin kundinta na 2021 na masu tauye hakkin addinai.