Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Kunamu sun harbi mutum 450 a Masar, uku sun mutu

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita

  1. Ƙwazon 'yan Najeriya a ƙasashen waje saboda ilimin da suka samu a gida ne - Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce 'yan ƙasarsa mazauna ƙasashen waje na da himma sosai sakamakon tarbiyya ko ilimin da suka samu a gida kafin su fita.

    Buhari ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da Ƙaramin Ministan Harkokin Wajen Daular Larabawa (UAE) Shaikh Shakboot Alnahyan a Faransa ranar Juma'a a gefen taron zaman lafiya da suke halarta.

    A cewar wata sanarwa daga kakakin fadar shugaban, Femi Adesina, Buhari ya siffanta 'yan ƙasarsa maza da mata a matsayin "masu gogayya a gida da waje," kuma ya shawarce su da su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda.

    Ya ce: "Akwai 'yan Najeriya a ko'ina, masu ƙwazo. Kuma ƙwazon nasu na farawa ne tun daga gida (Najeriya), inda suke samun ingantaccen ilimi, su shiga sana'o'i sannan kuma su wuce ƙasashen waje."

    Haka nan, shugaban ya nemi 'yan Najeriya "su koya wa kansu bin dokoki da tsarin ƙasashen da suke zaune a ciki ko kuma aiki".

    Yayin ganawar, Buhari ya yi maraba da shirin ƙasashen biyu na haɗin gwiwa a fannin makamashin da ba ya ƙarewa da noma da ayyukan raya ƙasa da kuma samar da rigakafin annobar korona.

  2. 'Yan Sudan na shirin yin gagarumar zanga-zanga a yau

    A yau Asabar an rufe dukkan gadojin da ke danganawa da babban birnin Sudan wato Kartoum, gabanin gagarumar zanga-zangar da 'yan ƙasa ke shirin yi.

    Juyin mulkin da sojoji suka yi a watan da ya gabata karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan ne ya tunzura mutane suka kwarara a titunan kasar.

    Wakiliyar BBC ta ce kungiyoyin masu rajin dimukuraɗiyya sun yi kira ga jama'a su yi fitar farin ɗango don aike wa jagororin gwamnatin sojin kwakkwaran sakon cewa tilas ne a dawo da gwamnatin farar hula.

    Amurka da EU da Birtaniya da Norway da Switzerland sun ce kafa sabuwar majalisar rikon kwarya karkashin jagorancin soja ta dagula shirin dawo da mulkin dimokuradiyya.

    A ranar Alhamis ne Janar Burhan ya sake naɗa kansa a matsayin shugaban gwamnatin ƙasar.

  3. Maraba

    Za ku samu rahotanni kai-tsaye daga sassan duniya a wannan shafi idan kuka kasance da mu har zuwa yammacin wannan rana.

    Umar Mikail ne ke muku barka da hantsin Asabar.