Buhari ya bukaci 'yan Najeriya su rika alfahari da sojojin kasar
Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya
Rahoto kai-tsaye
Awwal Ahmad Janyau and Muhammad Annur Muhammad
Bayanan sautiMinti Ɗaya Da BBC Na Safe 25 10 2021 Kungiyar Kasashen Larabawa ta 'damu' da halin da ake ciki a Sudan
Kungiyar Kasashen Larabawa ta Arab League ta nuna damuwa kan abinda ke faruwa a Sudan.
Rahotanni sun ce yanzu haka sojoji na tsare da Shugabannin farar hula da kuma wasu daga cikin ministoci, a wani yanayi mai kama da juyin mulki.
Sakatare Janar na Arab League Ahmed Aboul Gheit ya yi kira ga bangaroran da ba sa ga maciji a Sudan da su martaba yarjejeniyar da aka kulla da gwamnatin riko.
An shafe kwanaki ana zanga zangar adawa da kuma ta nuna goyon baya ga sojoji a Khartoum, wanda hakan yasa aka fara nuna fargaba kan makomar kasar.

Asalin hoton, Twitter
Abin da muka sani zuwa yanzu kan juyin mulkin Sudan
Sojojin Sudan sun kama mambobin gwamnatin rikon kwarya da dama a Sudan kuma an yi Firaminista Abdalla Hamdok ɗaurin talala.
Abin da muka sani kawo yanzu:
- Firaminista da aƙalla ministoci huɗu na cikin waɗanda sojoji da ba a tantance ba suka kama
- An baza sojoji a Khartoum babban birnin Sudan, yayin da masu zanga-zanga suka fito suna ƙone tayoyi
- An katse intanet
- Wasu rahotanni sun ce sojoji sun mamaye hedikwatar kafofin yaɗa labarai na rediyo da talabijin tare da kama ma’aikata
- Amurka ta ce ta damu da rahotannin juyin mulki a Sudan
An rufe filin jirgin saman Khartoum sakamakon rahotannin juyin mulki
An dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a Khartoum babban birnin Sudan, sakamakon rahotannin juyin mulkin da aka yi.
Rahotanni sun ce an rufe filin jirgin saman na Khartoum kuma an toshe hanyoyin shigarsa, inda rahotanni ke cewa dakarun soji sun kewaye shi.
Babu wata sanarwar gwamnati a hukumance kan matsayin filin jirgin.
Tashin hankali a Khartoum
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya samu hotunan masu zanga -zangar da suka taru a kan titunan birnin Khartoum a safiyar Litinin yayin da rahotanni ke cewa sojoji sun karbe iko.

Asalin hoton, Reuters
Hotunan sun yadda ƴan sudan suka fantsama saman titi suna kone tayoyi a kan tituna.

Asalin hoton, Reuters
An baza sojoji da jami’an sa-kai a fadin birnin kuma suna takaita zirga -zirgar fararen hula, kamar yadda Reuters ya ruwaito

Asalin hoton, Reuters
An ga mata da yara a cikin masu zanga-zangar a Sudan

Asalin hoton, Reuters
Likitoci sun shiga yajin aiki na adawa da 'juyin mulki' a Sudan
Likitocin Sudan sun sanar da aniyarsu ta shiga yajin aikin gama-gari domin nuna adawarsu da abin da suka kira juyin mulki a ƙasar.
Ƙungiyar likitocin ta ce matakin zai shafi dukkanin asibitocin ƙasar, illa ɓangarorin da suka shafi buƙatar aikin gaggawa
Buhari zai ƙaddamar da e-naira a Najeriya

Asalin hoton, Presidency
Ana sa ran Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai ƙaddamar da kuɗin intanet na ƙasar e-Naira ko kuma nairar da ake kashewa ta intanet.
Tun farko an tsara ƙaddamar da kuɗin intanet ɗin ne a farkon wannan wata, amma sai Babban Bankin Nijeriya ya ɗage batun zuwa gaba.
Bankin ya ce ya shafe shekaru yana bincike a kan e-Naira kuma "an ɓullo da ita ne da zummar sauƙaƙa wa kowane ɓangare na al'umma gudanar da harkokin kuɗinsu".
Tun da farko Babban Bankin Najeriya, CBN, ya ce a watan Oktoba 'yan kasar za su soma amfani da kuɗin intanet na e-Naira.
CBN ya bayyana haka bayan ya haramta amfani da kudin Cryptocurrency saboda rashin gamsuwa da yadda tsarinsa yake.
e-Naira kudi ne da zai bai wa mutane damar yin harkokin kasuwanci ta intanet.
Korona ta kama ƙarin mutum 43 a Abuja
Hukumar dakile cutuka masu yaɗuwa ta Najeriya NCDC ta ce ƙarin mutum 165 sun kamu da korona a Najeriya.
Mutum 77 suka kamu da cutur a Legas a ranar Lahadi, yayin da kuma aka samu ƙarin mutum 43 a Abuja.
A jihar Rivers kuma mutum 22 suka kamu.
Alƙalumman sun nuna daga cikin mutum 210,460 da sutar ta shafa, 202,379 sun warke, yayin da cutar ta kashe mutum 2,882 a Najeriya

Asalin hoton, ncdc
Maraba
Muna maku barka da safiya da kuma fatan kasancewa da mu a wannan shaifn da muke kawo labarai kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.
