Buhari ya bukaci 'yan Najeriya su rika alfahari da sojojin kasar

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Muhammad Annur Muhammad

  1. Kila jihohi 33 a Najeriya ba za su iya biyan albashi ba saboda bashi

    Ministar kudi ta Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed

    Asalin hoton, TWITTER/@ZAINABAHMEDS

    Bayanan hoto, Ministar kudi ta Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed

    Mai yuwuwa jihohi 33 a Najeriya ba za su iya biyan albashi ba, saboda shirin gwamnatin tarayya na yanke kason kananan hukumomi domin fara yanke kudin da take biya na bashin dala miliyan 418 kwatankwacin naira miliyan 172 na kwararru kan kungiyar masu bayar da bashi ta kungiyar Paris Cub.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, a rahotonta kan matsayin jihohi (‘State of States 2019'), BudgIT, wadda kungiya ce da ke sa ido kan harkokin kudi na gwamnati ta ce gwamnatocin jihohi uku ne kawai - Lagos da Rivers da Akwa Ibom, ne kawai za su iya biyan albashi da sauran harkokinsu na yau da kullum ba tare da samon kason gwamnatin tarayya ba.

    Kungiyar gwamnonin Najeriya da sauran al'ummar kasar na matsa lamba domin daina biyan wadannan kudade da ake gani ba na gaskiya ba ne ga kwararrun.

    Sai dai kuma a wani abu da ke bayar da mamaki, kasa da wata daya bayan da Shugaba Muhammadu Buhari, ya bayar da umarni, ma'aikatar kudi da kasafi da kuma tsare-tsare ta fara zaftare kason kudaden da ake bai wa jihohi na kananan hukumomi domin biyan bashin.

    Babban sakatare na ma'aikatar ya gaya wa taron kwamitin rabon kudade na tarayya a ranar JUma'a cewa, ma'aikatar ta fara yanke kudaden domin biyan bashin.

    Wannan bayani ya harzuka jihohin, suka ki yarda da rabon watan Oktoba da ake ciki, har sai gwamnati ta dakatar da wannan yanka.

  2. Taliban ta yi maraba da kalaman Ayatollah Khamenei a kan hadin kai tsakanin 'yan shi'a da mabiya Sunnah

    Taliban leader

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Jagoran Taliban Mullah Abdul Ghani Baradar

    Kungiyar Taliban ta yi maraba da kalaman Ayatollah Khamenei a kan hadin kai tsakanin 'yan shi'a da mabiya Sunnah a Afghanistan sakamakon hare-haren da ISIS ke kaiwa a kwanan nan.

    Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Taliban Abdul Qahar Balkhi, ya sanya wani sako na Tuwita inda yake cewa, "Daular Musulunci ta Afghanistan ta yi maraba da kalaman Jagoran Jamuhuriyar Musulunci ta Iran, na neman babban hadin kai tsakanin 'yan Sunni da 'yan Shi'a a Afghanistan.

    A kwanan nan yayin wani taro da bakin taron duniya kan hadin kan Musulmi, babban jagoran addinin na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya jaddada magana kan harin da aka kai kwanan nan a masallatan 'yan Shi'a a Afghanistan, yana mai nuna muhimmancin hadin kan 'yan Shia da 'yan Sunnah.

    Ya ce kasancewar jami'an Taliban da karfafa wa 'yan uwa guiwa a wurin taron al'umma wata hanya ce ta kare irin wadannan hare-hare.

  3. Rarara ya ce zai tsaya takarar dan majalisar wakilai

    Rarara

    Shahararren mawaƙin siyasar a arewacin Najeriya Dauda Adamu Kahutu (Rarara), ya bayyana cewa maganar da ake yawo da ita ta batun tsayawarsa takarar zama ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar Ƙananan Hukumomin Bakori da Ɗanja da ke Jihar Katsina gaskiya ce.

    Mujallar Fim ta ce Rarara ne ya tabbatar mata da hakan a wata hira da ta yi da shi.

    Mawakin ya ce kwanan nan zai tsunduma zagaya jihohin Nijeriya domin nuna irin ayyukan da ya gano Buhari ya yi.

    Ya ce, “Idan Allah ya sa na kammala wannan aikin da ke gabana, to zan tsaya takarar ɗan Majalisar Tarayya na Ƙananan Hukumomin Bakori da kuma Ɗanja.

    "Idan kuma wannan aiki ya sha gabana, sai kuma a duba batun nan gaba.”

  4. Matar da ta Musulunta ta shiga IS ta sha ɗaurin shekara 10 kan kisan yar Yazidi

    Jennifer Wenisch ta ɓoye fuskarta a kotu

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Jennifer Wenisch ta ɓoye fuskarta a kotu

    An yi wa wata mata 'yar Jamus da ta Musulunta sannan ta shiga kungiyar IS a Iraqi daurin shekara goma a birnin Munich na Jamus din a kan laifin kisan wata yarinya 'yar addinin Yazidi, wadda ita da mijinta suka saya a matsayin baiwa.

    Kotu ta ayyana cewa Jennifer Wenisch ta taimaka wajen aikata mugun laifi, a lokacin da ta tsaya tana gani lokacin da mijinta ya bar yarinyar 'yar shekara biyar ta mutu saboda tsananin kishirwa kuma daure da sarka a cikin tsakar rana, a birnin Fallujah a 2015.

    Mijin, mai suna Taha al-Jumailly, wanda mayaki ne na IS yana fuskantar shari'a a halin da ake ciki a birnin Frankfurt, kuma a wata mai zuwa ne ake sa ran yanke masa hukunci.

    Wenisch, mai shekara 30, ta musanta laifin. Kuma lauyoyinta sun ce mahaifiyar yarinyar mai suna Nora, ba sheda ce da za a dogara da ita ba, sannan sun yi zargin cewa babu wata sheda da ta tabbatar da cewa yarinyar ta mutu.

    Kungiyar IS ta mayar da Nora tare da 'yarta da kuma wasu mabiya addinin Yazidi bayi.

    Wannan shari'a ita ce irinta ta farko da aka yi wa 'yan IS a kan 'yan Yazidi, wadanda Kurdawa ne daga arewacin Iraqi, kuma suna daga cikin wadanda suka fi fuskantar akubar 'yan IS.

    A shekara ta 2016 ne aka kama Wenisch a Turkiyya, sannan aka kai ta zuwa Jamus domin fuskantar shari'a a kan dokokin duniya da suka shafi laifukan yaki a wata kasa ta waje.

  5. Shugabannin majalisun jihohi 36 sun nemi Buhari ya ayyana 'yan fashin daji a matsayin ƴan ta'adda

    Shugabannin majalisun jihohi 36 na Najeriya sun yi kira ga gwamnati da ta ayyana barayin daji da ke addabar yankin Arewa maso yammacin kasar a matsayin ‘yan ta’adda.

    Yayin wani taro na shekara-shekara da suke yi, ‘yan majalisar a zamansu na ranar Lahadi a birnin Katsina sun kuma tattauna kan al’amuran cigaban kasa baki Daya.

    Ga rahoton da Usman Minjibir ya hada mana:

    Bayanan sautiRahoton Usman Minjibir kan shugabannin majalisun jihohin Najeriya
  6. Buhari ya bukaci 'yan Najeriya da su rika alfahari da sojojin kasar

    Buhari

    Asalin hoton, Buhari Sallau

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yaba wa dakarun kasar kan yadda ya ce suna tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a kasar, inda ya bukaci 'yan kasar da su rika alfahari da sojojin.

    Mataimaki na musamman ga shugaban a kan harkokin yada labarai Femi Adesina ne ya bayyana haka a wata sanarwa ta lokacin kaddamar da asusun tallafi na tunawa da ranar 'yan mazan-jiya, ta 2022, a ranar Litinin, a Abuja.

    Ana dai bikin ne na shekara-shekara domin yabawa da irin bajinta da sadaukar da kai da tsoffin sojojin na Najeriya suka yi a yakin duniya na daya da na biyu da taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya a wasu kasashe da kuma cikin Najeriyar.

    A wurin bikin Shugaban ya yaba wa tsoffin sojojin da suka sadaukar da kansu wajen kare kasar da duniya, musamman wadanda suka rasa ransu.

    Ya ce, ”Kokarin kasarmu tun lokacin da ta samu yancin kai ya gamu da kalubale na tashin hankali na jama'a da yakin basasa da bore da kuma gwagwarmaya da makamai.

    ”Amma kuma duk da wadannan matsaloli, kasar ta ci gaba da zama dunkulalliya kuma burin yan kasar na zama tsare na nan daram.

    ”Kokarin sojojinmu na wanzar da zaman lafiya da kuma matsayinsu a kan hadin kan Najeriya sun taimaka gaya wajen zaman lafiyarmu.'' in ji Shugaba Buhari.

  7. Yarima Charles zai ziyarci Gabas ta Tsakiya don kyautata alakar mabiya addinai

    Charles Prince

    Yariman Wales, Charles da mai dakinsa Gimbiyar Cornwall za su yi ziyararsu ta farko a cikin shekara biyu inda za su je Jordan da Masar a wata mai zuwa.

    A yayin bulaguron nasu za su ziyarci wuraren ibada masu tsarki da tarukan ibada na addinai domin kyautata alaka tsakanin mabiya addinai.

    Haka kuma a yayin ziyarar tasu a kasashen biyu za su nuna muhimmancin mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi sauyin yanayi da ilimin 'ya'ya mata.

    Da wannan ziyara hakan na nufin dawo da ziyarar kasashen waje ta 'yan gidan Sarautar Birtaniya, wadda aka dakatar kafin annobar korona.

    Gwamnatin Birtaniya ce dai ta bukaci samun damar ziyarar, saboda muhimmancin da kasashen biyu suke da wajen wanzar da kyakkyawar alaka tsakanin mabiya addinai da kuma al'adu daban-daban.

    A baya Yarima Charles ya taba yin gargadi kan hadarin nuna wariyar addini da tsattsauran ra'ayi da kuma barazanar da mabiya addinin Kirista ke fuskanta a Gabas ta Tsakiya.

  8. Isra’ila ta ware biliyoyin dala domin inganta rayuwar Larabawan ƙasar

    Larabawan Isra'ila

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Isra’ila ta amince da wani shiri na kashe kusan dala biliyan 10 domin inganta rayuwar Larabawa marasa rinjaye a ƙasar, wadanda suka dade suna korafin an mayar da su saniyar ware.

    Za a kashe kuɗaɗen ne kan ayyukan da za su haɗa da samar da ayyukan yi da inganta ayyukan kiwon lafiya.

    Wata jam'iyyar Larabawa, Raam - wacce ke cikin gamayyar jam'iyyu masu mulki - ta yaba da shirin kashe kuɗin.

    Ta kuma yi maraba da wani shiri na daban don ware wasu ƙarin kuɗi ayaƙi da yawan aikata laifuka a cikin al'ummar Larabawa, inda aka kashe mutum fiye da 100 a wannan shekarar.

  9. Yadda hayaƙi ya turnuƙe Khartoum a zanga-zangar Sudan

    Wasu hotuna sun nuna yadda masu zanga-zanga suka haɗa gangami a Khartoum babban birnin Sudan yayin da hayaƙi ya turnuƙe birnin sakamakon ƙone tayoyi.

    Sudan

    Asalin hoton, Andalous Agency via Getty Images

    Bayanan hoto, Yadda tayoyi ke cin wuta a Khartoum
    Gwamnati ta yi kira ga mutane su yi zanga-zangar lumana

    Asalin hoton, Andalous Agency via Getty Images

    Bayanan hoto, Gwamnati ta yi kira ga mutane su yi zanga-zangar lumana
    Wani daga cikin masu zanga-zanga yana nuna alamar nasara a kusa da inda tayoyi ke cin wuta

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Bayanan hoto, Wani daga cikin masu zanga-zanga yana nuna alamar nasara a kusa da inda tayoyi ke cin wuta
  10. Duk mai son mulkin Najeriya dole ya yi yarjejeniya da arewa - Bakare

    Bakare

    Wani babban malamin coci a Najeriya wanda kuma ya taba yin takarar mataimakin shugaban kasa ga Buhari, Fasto Tunde Bakare, ya ce duk wani mai son ya mulki Najeriya sai ya yi yarjejeniya da yankin arewacin kasar.

    Fasto Bakare wanda ya shaida wa jaridar Thisday hakan ya ce "arewa tana da hanyar mayar da kai shugaban je ka na yi ka."

    Faston ya ce za a iya sauya hakan ne kawai ta hanyar sauya kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya bayyana a matsayin "shaidar mutuwa."

    A cewarsa, "tsarin da kundin mulkinmu yake kai a yanzu, ko ma waye zai mulki kasar, to sai ya yi yarjejeniya da arewa kuma ita arewar nan tana da hanyar dora ka a mulkin amma ba za ka zama raumi da akala ne.

    "Na kan ce kusan duk abubuwan da arewa ke da su a lokacin su Ahmadu Bello a yanzu babu su. Duk masana'antun da ake da su da yanzu babu. Babu dalar gyada da saurans su.

    "Abin da kawai suke da shi yanzu shi ne mulki. Suna da karfin iko," in ji shi.

    Tunde Bakare ya ƙara da cewa "Najeriya ƙasa ce da babu bangaren da zai iya cin zabe a kan kansa. Dan kudu ba zai iya cin zabe ba tare da neman arewa ba haka ma dan arewan."

    Sannan ya ce abubuwa sun taɓarɓare duk da alkawuran da wannan gwamnatin kafin ta hau mulki.

  11. MURIC ta faɗi sunayen Yarbawa Musulmai da ta ce sun cancanci zama shugaban Najeriya

    Fashola da Tinubu

    Asalin hoton, @gazettengr

    Wata ƙungiya mai da’awar kare haƙƙin Musulmi ta MURIC a Najeriya ta jaddada goyon bayanta ga fifita ɗan takarar shugaban ƙasa ya kasance musulmi ɗan ƙabilar Yarabawa.

    Cikin wata sanarwa da jaridun Najeriya suka ruwaito, MURIC ta cebabu wani musulmi Bayarabe da ya taɓa karɓar fadar Aso Rock, ko dai a matsayin shugaban ƙasa ko kuma mataimakin shugaban ƙasa tun samun ƴancin Najeirya a 1960.

    Ƙungiyar ta ce Yarbawa mabiya addinin Kirista uku suka samu wannan damar.

    Kungiyar ta bayyana Yarabawa Musulam iguda takwas da ta kira “wadanda suka cancanta” su jagoranci Najeriya.

    Daga cikin sunayen da ƙungiyar ta zayyana sun haɗa da jagoran APC Bola Tinubu da shugaban Hukumar Jamb Ishaq Oloyede da tsohon mai ba uwar jam’iyyar APC shawara kan harakokin shari’a Muiz Banire da mataimakin gwamnan Legas Dr. Kadiri Obafemi Hamzat.

    Sauran kuma sun hada da tsohon gwamnan Legas kuma ministan ayyuka da gidaje Babatunde Fashola da tsohon gwamnan jihar Osun ministan cikin gida Rauf Aregbesola.

  12. An yi gwanjon takalmin Michael Jordan kan kusan dala miliyan ɗaya da rabi

    Nick Fiorella, wani ɗan kasuwar sayen kayayyaki ne ya saye takalmin

    Asalin hoton, SOTHEBY'S

    Bayanan hoto, Nick Fiorella, wani ɗan kasuwar sayen kayayyaki ne ya saye takalmin

    An yi gwanjon wasu takalmin da fitaccen ɗan wasan kwallon kwando na Amurka Michael Jordan ya yi amfani da su kan dala miliyan 1.47 kwatankwacin fam miliyan 1.1.

    Jordan ya yi amfani da takalmin launin ja da fari na kamfanin Nike Air Ships a farkon kakarsa Chicago Bulls a 1984.

    Wannan shekarar ce da shi da Nike suka fara haɗin gwiwa don ƙirƙirar sa hannunsa a tufafi da takalmi.

    Farashin shi ne mafi girma da aka taɓa biya ga wani takalmin wasa da aka taɓa saka a kowane irin wasanni.

    Mutane da dama na ganin Jordan a matsayin ɗan wasan kwando mafi shahara a tarihin ƙwallon kwando.

    Jordan wanda ya yi ritaya a 2003, ya kuma zama hamshakin attajiri a tarihin wasan ƙwallon Kwandon Amurka ta NBA

  13. Gwamnatin Najeriya ta ce an kama fursunoni 500 da suka tsere gidan yarin Oyo

    Ma’aikatar harakokin cikin gida ta Najeriya ta ce an sake kama fursunoni kusan 500 da suka tsere a gidan yarin Oyo a ƙarshen mako.

    Ministan ma’aikatar harakokin cikin gida Rauf Aregbesola wanda ya kai ziyara gidan yarin a ranar Lahadi ya ce an zuwa yanzu an sake kama fursunoni 446 daga cikin sama da 800 da suka tsere.

    Ya ce akwai fursunoni 69 da ba su tsere ba a gidan yarin.

    Daruruwan fursunoni ne suka tsere a gidan yarin Abonlogo a jihar Oyo yankin kudu maso yammacin Najeriya bayan ƴan bindiga sun abka gidan yarin.

    Hukumar da ke kula da gidan yari ta ce maharan sun abka gidan yarin ne ta hanyar amfani da gurneti.

    Kuma hukumomin sun ce an kashe soja ɗaya da ɗan banga ɗaya a harin.

    Ministan cikin gidan Najeriya

    Asalin hoton, Other

  14. Sojojin Sudan 'sun harbi masu zanga-zanga'

    Rahotanni sun ce sojoji sun harba harsasai na gaske kan masu zanga-zanga a gaban hedikwatar sojojin kasa da ke Khartoum, babban birnin Sudan, a cewar shafin Facebook na Ma'aikatar Al'adu da Watsa labarai.

    Sanarwar ta ce mutane da dama sun jikkata sakamakon harbin.

    "Sojoji sun yi harbi da harsasai na gaske kan masu zanga-zanga wadanda suka bijire wa juyin mulkin da sojoji suka yi a Babban Rundunar Sojin Kasa, kuma mutanen da [ba a san adadinsu ba] sun jikkata," a cewar ma'aikatar a wani gajeren sako da ta wallafa a Facebook.

    Dubban mutane ne suka fantsama kan titunan Khartoum domin yin bore bisa kama firaiminista da manyan jami'an gwamnati wadanda ke cikin gwamnatin hadaka.

    Shugaban gwamnatin hadaka JanarAbdel Fattah Abdelrahman Burhan ya ayyana dokar ta-baci a cikin jawabin da ya gabatar, yana mai sanar da cewa an kawo karshen gwamnatin hadaka sannan an rusa gwamnatin farar hula.

  15. An yi 'garkuwa' da Firaiministan Sudan - ma'aikatar gwamnati

    An yi "garkuwa" da firaiministan Sudan Abdallah Hamdok a gidansa da ke Khartoum tare da matarsa a safiyar ranar Litinin, a cewar sanarwar da Ma'aiktar Al'adu da Yada labarai ta wallafa a shafinta na Facebook.

    Ta kara da cewa abin da ya faru ya yi daidai da keta kundin tsarin mulkin kasar da kuma "yin juyin mulki".

    Sanarwar ta yi kira ga 'yan kasar Sudan su fantsama kan tituna domin gudanar da zanga-zangar lumana sannan su yi duk abin da ya dace domin "kare juyin juya halinsu".

  16. Majalisar Ɗinkin Duniya ta buƙaci a gaggauta sakin shugabannin farar hula a Sudan

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kira ga sojojin Sudan su “gaggauta sakin waɗanda aka kama ba bisa ka’ida ba ko kuma aka yi masu ɗaurin talala.

    Firaminista Abdallah Hamdok yana cikin shugaban farar hula da rahotanni suka ce wasu sojoji sun yi wa ɗaurin talala a ranar Litinin.

    Manzo na musamman a Sudan Volker Perthes ya ce “na damu sosai game da rahotannin juyin mulki da kuma yunƙurin yin zagon ƙasa ga dawowa tafarkin dimokuradiyya a Sudan.Rahotannin kama Firaminista da jami’an gwamnati da ƴan siyasa ba abin amincewa ba ne.”

    Sudan

    Asalin hoton, Getty Images

  17. Tarayyar Afirka ta yi mamaki kan juyin mulki a Sudan

    Shugaban hukumar Tarayyar Afirka ya yikira da a "gaggauta komawa kan teburin sulhu" tsakanin farar hula da sojoji a yayin da ake tsaka da batu juyin mulki a Sudan.

    A cikin wata sanarwa Moussa Faki Mahamat ya ce ya yi matukar mamaki game da abubuwan da ke faruwa sannan ya yi kira da a "saki dukkan shugabannin siyasa da kuma matukar mutunta hakkin dan adam".

  18. Janar Burhan ya ayyana dokar ta-baci a Sudan

    Janar Burhan

    Asalin hoton, Nichola Mandil

    Shugaban gwamnatin hadaka JanarAbdel Fattah Abdelrahman Burhan ya ayyana dokar ta-baci a cikin jawabin da ya gabatar.

    Ya kuma rusa gwamnatin kasar da ke shirin mayar da Sudan tafarkin dimokuradiyya.

    Ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a kafar talabijin asar.

    Ya kuma kuma tuɓe ministoci da gwamnoni daga muƙaminsu.

    Ya ce za a kafa gwamnatin riƙon ƙwarya kafin ƙarshen watan Nuwamba, tare da ayyana cewa za a gudanar da zaɓen da zai mayar da ƙasar turbar dimokuradiyya a watan Yulin 2023.

  19. Za a yi da na-sanin ayyana ƴan fashin daji ƴan ta’adda – Sheikh Gumi

    Sheikh Gumi

    Fitaccen malamin addinin Islama a Najeriya da ke da’awar yi wa ƴan fashin daji masu satar mutane wa’azi, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi gargadin cewa za a yi da na-sanin ayyanasu a matsayin' yan ta'adda.

    Malamin ya faɗi haka ne cikin wata sanarwa da aka wallafa a wani shafinsa na Facebook.

    Tuni dai ƴan majalisa a Najeriya suka nemi gwamnatin Tarayya ta ayyana ƴan fashin da suka addabi arewacin Najeriya a matsayin ƴan ta’adda.

    A cikin sanarwar, Sheikh Gumi ya yi gargaɗin cewa “da zarar an ayyana ƴan fashin daji a matsayin ƴan ta’adda ƙungiyoyi masu da’awar jihadi na ƙasashen waje za su samu gindin zama.

    Ya kuma ce wannan zai iya janyo ra’ayin matasan da ke fama da rashin aikin yi.

    "Babu wanda ke shakkar cewa son raine a yau ya mamaye siyasarmu. Don ci gaba, dole ne wasu su fito su yi magana,” a cewar Sheikh Gumi.

    Sai dai kuma a cikin bayanansa malamain ya ce ayyukan da ƴan fashin daji ke aikatawa sannu a hankali sun zama na ta’addanci – “saboda duk inda ake kashe mutanen da ba su ji ba su gani ba, ta’addanci ne tsantsarsa.”

  20. Ƴan Nijar sun koka kan bazuwar ƴan fashin daji a ƙasarsu

    Yan bindiga

    Asalin hoton, Other

    Mahukunta a Jamhuriyar Nijar sun koka a kan ƙara fantsama da 'yan fashin daji suka yi, tun bayan ɗaukar matakan murƙushe su da wasu jihohin arewa maso yammacin Nijeriya mai maƙwabtaka da ita suka yi.

    A baya-bayan nan hare-hare da satar mutane don neman fansa na ƙaruwa a yankin MadaRumfa na jihar Maradi.

    Ko a ƙarshen mako, 'yan fashin sun abka wani gari inda suka saci mutum biyar ciki har da mace huɗu bayan sun harbi mutane.

    Sadissou Sani magajin garin Safo a cikin yankin na Maradi mai makwabtaka da jihar Zamfara ta Najeriya ya shaidawa wakiliyar BBC cewa ƴan bindigar sun daina satar dabbobi sun koma satar mutane a yankin.

    Ya ce daga cikin mutane biyar da suka sace, hudu daga cikinsu mata ne.

    Magajin garin na Safo ya yi kiran ƙara daukar matakai domin magance abin da ya kira babbar matsala