Mata 'yan zanga-zanga sun toshe babbar hanyar zuwa Gusau da Sokoto

Shafin da ke kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Fauziyya Tukur and Umar Mikail

  1. Ƴan sanda sun kama wasu masu zanga-zangar tunawa da Endsars a Legas

    Endsars protest

    Ƴan sanda a Legas sun kama a ƙalla mutum shidda da suka fita zanga-zangar tunawa da kashe-kashen Lekki.

    Wannan na zuwa ne a lokacin da ƴan sandan suka taru bayan sun yi gargaɗin cewa kada wanda ya fito zanga-zanga a yau amma ana iya yin jerin gwanon motoci.

    Mai barkwanci nan na Najeriya Mista Macaroni da mawaƙi Falz ranar Litinin sun sanar da cewa za a yi zanga-zangar duk da gargaɗin na ƴan sanda.

    Zanga-zangar wadda ake gudanarwa yau Laraba don tunawa ce da abin da ya faru a zanga-zangar Endsars ta bara.

    Zanga-zangar dai ta nuna ƙin jinin abin da aka kira cin zarafin da ƴan sanda ke yi ce, amma daga baya ƴan banga suka shiga zanga-zangar kuma nan da nan lamurra suka rikice.

    Ɗaya daga cikin abubuwan da suka faru kuma ya zama babban lamari ranar 20 ga watan Oktoba 2020, shi ne harbe-harben da aka yi a dandalin Lekki toll gate.

    An yi zargin cewa jim kaɗan bayan faɗuwar rana, sojoji sun je dandalin na Lekki don tarwatsa masu zanga-zangar saboda dokar hana fita da gwamnan jihar ya sa.

    Wasu mutane sun yi ta yaɗa hotunan a shafukan sada zumunta inda suka yi ikirarin cewa sojoji sun kashe mutane da dama a ranar.

    Rundunar sojin Najeriya ta amice ta yi harbi a Lekki a ranar a lokacin zanga-znagar amma sun ce ba su harba harsasai ba kuma ba su kashe kowa ba.

  2. Ƴan sanda sun kama masu sayar wa ƴan bindiga man fetur a Kano

    Ƴan sanda a Kano sun ce sun kama wasu a ƙaramar hukumar Fagge ta jihar Kano da ake zargin suna kai wa ƴan bindiga kayan abinci da man fetur a jihar Katsina.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ƴan sanda ta jihar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ta ce ƴan sanda sun kama mutum biyu, Musbahu Rabi'u da Jmailu Abdullahi a yayin wani bincike ɗauke da jakoki biyar na man fetur, ɓoye cikin buhuna.

    DSP Kiyawa ya bayyana cewa Jamilu ya amsa laifin cewa ya je Kano ne daga Katsina kuma ya sayi man fetur don kai wa Jibiya a jihar Katsina inda zai sayar da tsada.

    Kiyawa ya yi kira ga gidajen mai a jihar su daina sayar da fetur da yawa a cikin jarkoki ga mutanen da ba su sani ba kuma su kai ƙarar masu zuwa sayen ga ofishin ƴan sanda mafi kusa.

  3. Kiristoci sun halarci taron Mauludi a Kaduna

    Mauludi

    Asalin hoton, Daily Trust

    Kiristoci, ciki har da limamai sun taya Musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammadu tsira da aminci su tabbata a gare shi, a Kaduna ranar Talata.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mabiya addinan biyu sun taru a filin wasa na Ranchers Bees a tsakiyar birnin inda suka ce sun yi taron ne don karfafa zumunci da inganta hain kai.

    Shugaban cocin Christ Evangelical Intercessory Fellowship Ministries na unguwar Sabon Tasha, Pastor Yohanna Buru wanda ya jagoranci wata tawagar Kiristoci ya ce ya halarci taron ne don murnar haihuwar Annabi.

    Ya jaddada cewa "Annabi na kowa ne ba tare da la'akari da yare ko al'ada ko kalar fata ko nahiya ko yanki ba saboda ya yi kira ga zaman lafiya a gaba aya rayuwarsa."

    Ya kuma bayyana cewa a matsayinsa na mai son zaman lafiya kuma malamin addinin Kirista, halartar taron tare da Musulmai ba zai sauya masa addini ba.

  4. Yau ake cika shekara 10 da mutuwar Gaddafi

    Muammar Gaddafi

    Asalin hoton, Getty Images

    Yau ne ake cika shekaru goma bayan da 'yan tawaye a Libya suka halaka shugaban kasar Mu'ammar Gaddafi.

    Tun bayan tashin hankalin da ya janyo kisansa, Libya ta gudanar da zabukan 'yan majalisa har sau biyu, abun da ya kara dara kasar gida biyu.

    An samu gwamnatoci biyu da ke yaki da juna, guda a Benghazi guda a Tripoli.

    Ana sa ran Libya za ta sake gudanar da zabe a watan Disamba, duk da cewa mutane kalilan ne ke da kwarin guiwar za a yi shi.

  5. A karon farko an rantsar da mata kusan 100 a matsyain alƙalai a Masar

    Mata a Masar

    Asalin hoton, EPA

    Masar ta naɗa mata 98 a matsayin alƙalai a ɗaya daga cikin manyan hukumomin shari'ar ƙasar wato Majalisar kula da harkokin shari'a ta ƙasar.

    An naɗa alƙalan ne a gaban alƙalin alƙalan majalisar a wani taro a birnin Alƙahira ranar Talata.

    Wanann na zuwa ne watanni bayan Shugaba Abdul Fattah al-Sisi ya yi kira ga mata su shiga manyan hukumomin shari'ar ƙasar biyu - Majalisar kula da harkokin shari'a ta ƙasar da Ofishin Mai Gabatar da Ƙara na gwamnati.

    Tun bayan kafa ta a 1946, maza ne kawai ake naɗawa a majalisar kuma ba a amincewa da mata masu son aiki da majalisar.

  6. Maraba

    Barkanku da safiya. Da fatan kun tashi lafiya.

    Wannan shafin na kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da mawabtanta da ma sauran ƙasashen duniya.