Mu kwana lafiya
Ƙarshen rahotannin kenan a wannan shafi.
Umar Mikail ke cewa mu haɗu gobe a wani sabon shafin na rahotanni kai-tsaye.
Shafin da ke kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya.
Fauziyya Tukur and Umar Mikail
Ƙarshen rahotannin kenan a wannan shafi.
Umar Mikail ke cewa mu haɗu gobe a wani sabon shafin na rahotanni kai-tsaye.

Asalin hoton, State House
Turkiyya ta saka hannu kan yarjejeniyoyi da dama da Najeriya waɗanda za su haɓaka kasuwancin ƙasashen zuwa dala biliyan ɗaya duk shekara.
Shugaba Recep Tayyip Erdoğan ya kai ziyarar aiki Najeriya ne ranar Laraba inda ya gana da Shugaba Buhari.
Buhari ya bayyana cewa sun tattauna kan abubuwa da dama, ciki har da yaƙi da ta'addanci wanda Turkiyya ta ce za ta tallafa wa Najeriya a kan sa.
A ranar Talata, Mista Erdogan ya faɗa a ƙasar Togo cewa "a shirye Turkiyya take ta kafa ɗambar aikin soja tare da ƙasashen Afirka ta Yamma".

Asalin hoton, KDSG
Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai na Jihar Kaduna ya shawarci gwamnatin Najeriya ta ɗauki matasa 1,000 daga kowace ƙaramar hukuma aikin bayar da tsaro don yaƙar 'yan fashin daji masu garkuwa da mutane.
Da yake magana jim kaɗan bayan miƙa masa rahoto kan matsalar tsaro a jihar ranar Laraba, El-Rufai ya ce babu wata hanyar yaƙi da 'yan fashin daji illa "yi musu ruwan wuta a lokaci guda", abin da ya sa yake son a ɗauki matasa 774,000 aikin.
"Ina kira ga jihohi 36 da su ɓullo da wani shirin gaggawa na ɗaukar mutane aiki a rundunonin tsaro. Gwamnati ka iya sauya halin da ake ciki idan ta ɗauki matasa 1,000 aiki daga kowace ƙaramar hukuma a faɗin ƙasa.
"Hakan zai zama gagarumin adadi na dakaru a fagen daga tun bayan yaƙin basasa. Adadin sabbin dakaru 774,000 a filin yaƙi zai kasance babbar hanyar gamawa da miyagu da kuma samar da aikin yi."
Kazalika, gwamnan ya nemi gwamnatin Shugaba Buhari ta ayyana 'yan bindigar a matsayin 'yan ta'adda "saboda sojoji su samu damar kashe su ba tare da wata matsala ba", in ji shi.
"Mu a Kaduna mun sha neman a ayyana 'yan fashin nan a matsayin 'yan ta'adda. Mun rubuta wasiƙu ga gwamnatin tarayya tun 2017 muna neman a yi hakan saboda ayyana su ne kaɗai zai bai wa sojoji damar karkashe waɗannan 'yan fashin ba tare da wani abu ya biyo baya ba daga ƙasashen duniya."
Sabon rahoton da aka gabatar wa El-Rufai a yau ya nuna cewa mutum 343 aka kashe a Kaduna daga 1 ga watan Yuli zuwa 30 ga Satumban 2021 sakamakon ayyukan 'yan fashi da kuma rikicin ƙabilanci a jihar.
Haka nan, 'yan fashin dajin sun sace mutum 830 cikin wata ukun da rahoton ya bayar da bayanai a kai tare da raunata 210.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin Faransa sun ƙaddamar da binciken "ayyukan ta'addanci da tunzura mutane" abin da ya jawo rufe Masallacin Allones da Paris babban birnin ƙasar.
Shafin intanet na jaridar Le Figaro ya ruwaito cewa hukumomi sun rufe masallacin a ranar 15 ga watan Oktoba.
"Ginin ya ƙunshi makarantar Islamiyya da ke da ɗalibai kusan 110 waɗanda ake koya wa aƙidar martaba 'yan bindiga masu iƙirarin jihadi," a cewar mai shigar da ƙara ta Le Mans.
Ta ƙara da cewa: "Yanzu haka 'yan sanda na gudanar da bincike kan goyon bayan ta'addanci da kuma tunzura mutane su aikata ta'addanci. Mambobin ƙungiyar da ke gudanar da masallacin na fuskantar zargi kan hakan."
A ranar Laraba sashen binciken laifuka na Sarthe ya bayyana cewa ya ƙaddamar da bincike kan masallacin wanda ke da ma'abota kusan 300.

Asalin hoton, Bello Mohammad
Rahotanni a Zamfara a arewacin Najeriya sun ce ɗaruruwan mata sun toshe babbar hanyar zuwa Gusau da Sokoto domin nuna fushi kan halin da suke ciki na hare-haren ƴan bindiga.
Wasu hotuna sun nuna mata da yara ɗauke da kayansu saman hanya dab da shiga garin Tsafe.
Mutanen garin waɗanda mafi yawansu mata ne da yara sun tare babbar hanyar ranar Laraba inda suka haddasa cunkoson ababen hawa.

Asalin hoton, Bello Mohammad
Wani mazaunin yankin ya ce matan sun tsere wa hare-haren ƴan bindiga ne da suka addabe su, suna masu fyade. Kuma sun toshe hanyar ne domin janyo hankalin gwamnati kan halin da suke ciki.
Zanga-zangar tasu ta sa babu mai iya ratsawa ya fita ko shiga yankin.

Asalin hoton, Bello Mohammed
Wani direban mota a babbar tashar Gusau ya ce an shafe awanni babu wani direban da ya shigo tashar daga hanyar Funtua.
Mutanen Zamfara sun shafe makwanni babu hanyoyin sadarwa a sassan jihar da hana cin kasuwannin mako, matakin da hukumomin Najeriya suka ce sun ɗauka don magance matsalar ƴan bindiga masu fashi da satar mutane da suka addabi yankin arewa maso yammacin ƙasar.

Asalin hoton, Bello Mohammed

Wata Babbar Kotun Jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya ta zartar wa wasu ɗalibai 19 hukuncin ɗaurin shekara shida kowannensu a gidan yari sakamakon kama su da laifin shiga ƙungiyar asiri.
Kamfanin labarai na NAN ya ruwaito alƙalin kotun da ke Maiduguri Mai Shari'a Umar Fadawu na cewa an samu ƙwararan shaidu cewa dukkan ɗaliban sun aikata laifin haɗa baki da kuma shiga ƙungiyoyin da aka haramta.
'Yan sanda sun kama mutanen ne ranar 21 ga watan Satumban 2019 a wani otel da ke Maiduguri bisa zargin shiga ƙungiyar asiri ta Neo Black Movement wadda aka fi sani da Black Axe.
Bayan ya saurari roƙo daga lauya da kuma wasu daga cikin ɗaliban, alƙalin ya yanke musu hukuncin shekara shida kowannensu kan laifukan biyu.
Bugu da ƙari, an yanke musu hukuncin ne ba tare da zaɓin biyan tara ba kuma za su fara yin zaman gidan yarin daga ranar Laraba 20 ga watan Oktoba.
'Yan Majalisar Dokokin Nijar sun amince da tsawaita dokar-taɓaci a wasu yankuna na kasar da ke fama da matsalolin tsaro.
Tun shekarar 2015 ne gwamnatin ta fara ayyana dokar a jihar Diffa wadda ke fama da hare-haren kungiyar Boko Haram.
A 2017 kuma wani ɓangare na Jihar Tillabery ya fara fuskantar wannan matsala biyo bayan yawaita hare-haren daga kungiyoyin masu iƙirarin jihadi.
Bayan zaman jefa ƙuri'a ne wanda baki ɗayan 'yan majalisar suka halarta suka amince da dokar.

Asalin hoton, Reuters
Daya daga cikin fitatttun 'yan wasan kwallon kafa na Turai, wanda kuma ke taka leda a Faransa da Real Madrid Karim Benzema, ya gurfana a gaban wata kotu da ke wajan birnin Paris.
Ana tuhumarsa da da hadin baki a kokarin karbar kudi daga hannun tsohon dan wasan Faransa Mathiue Valbuena kan wani bidiyon baɗala.
Bezema ya jadada cewa ba shi da alaka da yunkurin karbar kudin amma ya shirya wata ganawa tsakanin abokinsa da dan wasan domin bayar da shawara kan abin da ya kamata ya yi domin ya fitar da kansa daga abin kunya.
Wani kwararre kan komfuta a birnin Marseille ya samu wani hoton bidiyo da ya nuna Valbuena yana jima'i da wata mace kuma ya yi kokarin karbar kudi daga hannunsa kafin ya goge bidiyon.
Dan wasan zai iya fuskantar hukuncin daurin shekara biyar da kuma tarar kudi mai yawa idan aka same shi da laifi.

Asalin hoton, KDSG
Sarkin Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna a arewacin Najeriya ya ce zuwa yanzu sun ga amfanin matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka da zummar daƙile ayyukan 'yan bindiga masu garkuwa da mutane.
Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II ya bayyana cewa matakan sun takure 'yan bindigar, abin da ya sa yanzu suke neman abinci daga wajen mutanen da suka sace maimakon kuɗin fansa.
Sarkin ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin taron ƙaddamar da rahoto kan matsalar tsaro da Ma'aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta jihar ta gabatar wa Gwamna Nasir El-Rufai.
"Mun nuna cewa matakan da gwamnati ta ɗauka na toshe layukan salula da hana hawan mashin da hana sayar da man fetur a ko'ina ya yi amfani ƙwarai da gaske domin mun gani a wajenmu kuma muna da labarin sauran wurare," in ji shi.
"Waɗannan matakai sun takura su ta yadda idan suka saci mutane sai dai su ce a ba su abinci ba kuɗi ba. Muna goyon bayan gwamnati kuma muna addu'ar Allah ya kawo ƙarshen wannan abu."
Rahoton ya duba rikice-rikicen da suka faru na 'yan fashin daji da ƙabilanci daga 1 ga watan Yuli zuwa 30 ga Satumban 2021.
Mutum 343 aka kashe sannan aka saci 830 tare da jikkata 210 jumilla sakamakon tashe-tashen hankalin.

Asalin hoton, Daily Trust
Wata ƴar ƙungiyar agaji ta Matasa Musulmai ƴan Najeriya (YMCN) da aka fi sani da Munazzamatul Fityanul Islam ta rasa ranta yayin tattakin murnar ranar Mauludi a Abuja, babban birnin Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne ranar Talata, sannan wasu mutum 10 sun suma.
Dubban Musulmai ne da suka haɗa da ƴan Islamiyya da mambobin ƙungiyoyin agaji da sauransu suka taru daga sassan Abuja suka yi maci a kan tituna don murnar ranar.
Ministan Abuja Muhammadu Musa Bello ne ya wakilci Shugaba Muhammadu Buhari a wajen taron.
A lokacin da take magana kan faruwar lamarin, wata jami'ar ƙungiyar agaji malama Sajida Bala Abdullahi ta ce marigayiyar mai suna Asma'u mai shekara 20 ta je taron ne daga unguwar Kuje.
'Yan Najeriya da dama suna ta bayyana ra'ayoyinsu kan shekara ɗaya bayan zanga-zangar ƙin jinin rundunar ƴan sandan da ke yaƙi da fashi da makami na Sars.
Wasu kuma sun sake fitowa kan tituna don tunawa da ranar.
Ku latsa hoton da ke ƙasa don kallon bidiyon:
Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai yi wani taron gaggawa bayan da Koriya ta Arewa ta tabbatar da cewa ta gwada wani sabon nau'in makami mai linzami da aka harba a karkashin teku.
Kafafen yada labarai na gwamnati a Pyongyang sun ba da sanarwar cewa sabon makamin ya fadada damar sarrafa makaman Koriya ta Arewa, da kuma sake ba ta wata damar ta kai mamaya har zuwa gaba da yankin tsibirin Koriya a duk lokacin da ta so yin hakan.
Gwajin makamin da aka yi cikin nasara ya saɓa wa umarnin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.
Wakiliyar BBC ta ce makamin daya ne daga cikin tarin irinsa da Koriya Ta Arewa ta nuna wa duniya a yayin wani baje kolin tsaro a makon da ya gabata, abin ya haifar da dari darin cewa watakila za ta sake harba wasu.
Amurka ta bukaci Koriya ta Arewa ta guji takalar fada, ta kuma koma teburin sulhu.

Asalin hoton, TWITTER/@SHATTAWALEGH
Rundunar ƴan sandan Ghana ta sanar da cafke shahararren mawakin nan na ƙasar Shatta Wale mai janyo ce-ce ku-ce da wasu mutum biyu, bayan ya yaɗa labarin ƙanzon kurege a shafin sada zumunta cewar wasu mutane biyu sun harbe shi.
Mawakin shi ne ya kai kansa wurin ƴan sanda bayan an bayyana shi a matsayin wanda suke nema ruwa a jallo bayan ƙaryar harbin sa da ya yi
A cikin wata sanarwar da rundunar ƴan sandan ta Ghana ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce bayan sun bayyana Shata Wale da wasu mutum biyu yaransa a matsayin waɗanda ake nema ruwa a jallo ne, mawakin ya miƙa kansa.
Sanarwar ta ƙara da cewa an cafke shi ne don ya taimaka wa ƴan sanda a binciken da suke yi an zargin sa da watsa labarin kanzon kuren mutuwarsa don tayar da zaune tsaye da jefa fargaba a zuƙatan jama'a.
Tun dai a wata sanarwar da rundunar ƴan sandan ta wallafa a baya ta yiw a al'umma gargadi da su daina yayata labaran ƙanzon kuregen da ka iya kawo tarnaƙi ga zaman lafiya ko a cafke mutum tare da hukunta shi.
Tun dai a watannin baya ne wani malamin kirista ya yi hasashen cewa za a kashe mawaki Shata Wale mai a ran 18 ga watan Oktobar wannan shekara.
A nasa bangaren mawakin ya ce ya watsa labarin ƙanzon kuregen cewa wasu mutane sun harbe shi a unguwar East Legon da ke birnin Acrra ne, saboda hukumomin tsaro sun gaza ba shi kariya, bayan hasashe wahayin mutuwar da malamin kiristan ya yi a kansa.
Sai dai tuni shi ma wannan malamin kiristan da ya yi harsahen wahayin ƴan sanda suka yi awon gaba da shi don taimaka wa wurin gudanar da bincike.
Al'umma dai sun fara jinjinawa sabon shugaban ƴan sanda George Akufoo wanda ake ganin ya fara aikinsa ba sani sabo inda wasu ma sun fara yi masa laƙabi cinnaka ba ka san na gida ba.
Yayin da da yawa suke cigaba da caccakar shaharren mawakin, wasu ma na ganin ya yi hakan ne don tallatar da sabon kundin wakarsa mai taken Gift of God wanda ake sa ran zai saka kwanan nan.
Sai dai da yawan mabiyansa na cigaaba da ɗaure masa gindi musamman a shafukan sada zumunta.
Yanzu abin jira a gani shi ne irin hukuncin da za a yanke akan wanda ake zargin.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta AC Milan ta taya Musulamn duniya murnar zagayaowar ranar haihuwar Manzon Allah SAW wato mauludi.
A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Talata, ƙungiyar ta ce: "A ranar da aka haifi Annabi Muhammad, muna yi wa dukkan Musulmai magoya bayanmu murnar wannan rana mai albarka kuma barkanku da Al-Mawlid Nabawi."
A ƙalla mutum sama da 66,000 ne suka so saƙon, kuma an yaɗa shi sau fiye da 4,000.

Asalin hoton, G
Kotu ta ƙi bayar da belin ɗan fitaccen jarumin fina-finan Indiya na Bollywood Shah Rukh Khan, kwana 18 bayan kama shi kan zargin mu'amala da miyagun ƙwayoyi a wajen wata liyafa.
An ɗauki Aryan Khan mai shekara 23 a cikin wani babban jirgin ruwa da ke kan hanyarsa ta zuwa jihar Goa daga birnin Mumbai ranar 2 ga watan Oktoba.
Hukunar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta tuhume shi a ƙarƙashin dokokin "mallaka da amfani da kuma sayar da miyagun ƙwayoyi."
Ya yi watsi da dukkan zarge-zargen da ake yi masa.
Lauyansa Satish Manshinde ya sha nanata wa kotun cewa ba a samu komai a tare da ɗan jarumin ba, "kuma babu wata shaida da ke nuna cewa ya sha wata muguwar ƙwaya."
Amma wata kotu a Mumbai a yau Laraba ta yi watsi da batun ba shi beli a karo na biyu. Ta fara watsi da batun ba da belin nasa ne ranar 8 ga watan Oktoba.
Sannan kotun ta ƙi bayar da belin wasu sauran mutum biyu da su ma ake tuhumarsu.
Ana sa ran lauyoyin Aryan Khan za su ɗaukaka ƙarar matakin a babbar kotun Mumbai.

Asalin hoton, State House
Shugaban Turkiyya Raceb Tayyib Erdogan ya isa fadar shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a wani bangare na ziyarar kwanaki biyu da yake yi kasar.
A karshen tattaunawar da suke yi a halin yanzu ana sa ran Shugabannin biyu su yi nazari kan wasu yarjeniyoyi 24 da ke tsakannin kasashensu kana su rattaba hannu kan wadanda suka yi mawafaka a kai.
Fadar Shugaban dai ta ce Najeriya na daukar Turkiyya a zaman abokiyar hulda ta kut-da-kut kuma wannan ziyarar za ta kasance wani muhimmin mataki na kara dankon danganta tsakanin kasashen biyu.

Asalin hoton, State House

Asalin hoton, State House
Wannan dai shi ne karo na biyu da shugaban na Turkiyya ke kawo ziyara Najeriya a zamanin mulkin Shugaba Buhari.
A watan Maris na 2016 Shugaba Erdogan ya ziyarci na Najeriya a wani bangare na rangadin kasashe 4 na yammacin Afrika da yayi a lokacin; yayin da watanni 19 daga bisani shi kumu Shugaba Buhari ya ziyarci kasar ta Turkiyya.
Duka dai kasashen biyu wakilai ne a kungiyar kasashe masu tasowa guda takwas wato D-8 wadda aka kafa a shekara ta 1997 da kuma taron kasashe 4 da ake sa ran su samu bunkasar tattalin arziki a gaba ta MINT.

Kimanin mutane arba'in da shida ne aka tabbatar da mutuwarsu, sakamakon ambaliyar da aka shafe kwanaki biyu ana yi a jihar Uttarakhand da ke arewacin Indiya.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya ne ya haifar da ambaliyar. Masu aiko da rahotanni sun ce gidaje da dama sun nutse, hanyoyi da gadoji sun rufta.
Wani babban jami'in 'yan sanda Nilesh Bharne, ya shaida wa BBC cewa ana ci gaba da aikin ceto a yankunan da abin ya shafa.

Gwamnatin Najeriya ta ce babu wata tartibiyar shaida da ke nuna cewa an kashe masu zanga-zanga a dandalin Lekki ranar 20 ga watan Oktoban 2020.
Ministan bayanai da al'adu Lai Muhammed ya shaida wa manema labarai a Abuja cewar binciken da masana kan harkokin makamai da rahotannin da Hukumar Kare Haƙƙin Dan Adam ta Amurka sun jaddada iƙirarin sojoji na cewa ba a harbi mai zanga-zanga ko ɗaya ba.
Ya ce gwamnatin Najeriya za ta yi aiki tare da hukumomin jihohi wajen biyan kuɗin fansa ga mutanen da yan sanda suka ci zarafinsu a ƙasar.
Ya kuma ce Majalisar Zartarwar ƙasa ta umarci jihohi su miƙa rahotonnin kwamitocin bahasinsu ga Antoni janar na jihohinsu don gaggauta gurfanarwa da yanke wa masu laifi hukunci.
A yau Laraba ne kuma ake gudanar da wata zangar-zangar don tunawa da 'harbe-harben' na Lekki da ake zargin sojoji sun yi a rana irin ta yau bara.




Asalin hoton, Reuters
Wani bom ya tashi a wata motar bas ta sojoji a Damascus inda ya kashe a ƙalla mutum 13 a cewar kafar yaɗa labarai ta Syria.
An sa wa motar abubuwan fashewa biyua lokacin da ta ke wucewa ta ƙasan gadar Jisr al-Rais jin kaɗan bayan asubaa cewar kamfanin dillancin labarai na Sana.
Duk da cewa an kwashe tsawon shekaru goma ana yaƙin basasa a Syria, ba a cika ganin irin waɗannan hare-haren ba a babban birnin.
A wani ɓangaren kuma, wani luguden wuta da sojoji suka yi ya kashe a ƙalla mutum takwas a yankin arewa maso yammaci da ke hannun ɓangaren hamayya.
Ƙananan yara ɗalibai na cikin mutanen da harin ya shafa a garin Ariha a lardin Idlib.