Burtaniya ta hana 'yan kasarta zuwa wasu jihohin Najeriya 12

Shafin da ke kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Fauziyya Tukur and Jabir Mustapha Sambo

  1. Ɗaruruwan mutane sun jeru tsirara a bakin Mataccen Teku a Isra'ila

    Hotuna

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗaruruwan mutane sun yi tsirara a bakin Mataccen Teku wato Dead Sea a Isra'ila don jan hankali kan janyewar da ruwan tekun ke yi ba ƙaƙƙautawa.

    Taron na cikin wani ɓangare na ɗaukar hotuna kai tsaye da wani mai hoto Spencer Tunick, wanda ya taɓa ɗaukar hotuna irin wannan a faɗin duniya don janyo hankali kan kare muhalli.

    Spencer ya ce yin tsiarara hanya ce mai ƙarfi da ke saurin ɗaukar hankali shi ya sa ya bi wannan hanyar don sanar da duniya halin da tekun ke ciki.

  2. Za a rage yawan zirga-zirgar jiragen ƙasa na Abuja zuwa Kaduna tsawon kwana biyu

    Jirgin ƙasa

    Hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya, NRC, ta sanar da cewa za ta rage yawan zirga-zirgar jirage tsakanin Abuja zuwa Kaduna daga ranar 19 zuwa 20 ga watan Oktoba.

    Shugaban hukumar, Fidet Okhiria ya sanar da cewa za a yi hakan ne don gudanar da gyare-gyare.

    Ya bayyana cewa a maimakon zirag-zirga sau goma a rana, za a yi guda huɗu ne kawai ranar 19 ga Oktoba da 20 ga Oktoba.

    Ya ƙara da cewa ranar Alhamis 21 ga Oktoba kuwa, za a yi tafiya takwas ne.

    Sanarwar tasa ta ce za a koma aiki yadda aka sana ranar Juma'a 22 ga Oktoba.

  3. Amurka ta gano Boko Haram da ƴan fashin daji na aiki tare

    BOKO HARAM

    Asalin hoton, AFP

    Wasu shugabanni na Amurka sun gano yadda mayaƙan Boko Haram da ke ayyukansu a Arewa maso gabashin Najeriya ke haɗa kai da ƴan fashin dajin da ke kai hare-hare a arewa maso yammacin ƙasar wajen satar mutane don kuɗin fansa daga hannun gwamnati da fararen hula, kamar yadda jaridar Wall Street Journal ta ruwaito.

    Jaridar ta ƙasar Amurka ta ruwaito cewa Amurka ba ta ganin fashin daji a matsayin barazana a gareta, amma jami'ai sun jima suna sa ido kan kwamandojin ƴan bindiga da yiwuwar alaƙarsu da mayaƙan Boko haram.

    Wani rahoto da jaridar ta wallafa ranar Asabar ya ce "Amurka ba ta wani damu ƙwarai ba da ƴan fashin daji, duk da cewa jami'an gwamnatin Amurka sun ce sun yi kutse kan wani kiran waya daga wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne da ke arewa maso gabashi kuma an ji suna bai wa ƴan bindiga a arewa maso yammacin ƙasar shawara kan garkuwa da mutane da tattaunawa don karbar kuɗin fansa."

    Rahoton ya kuma jaddada kiraye-kirayen da ake yi wa Shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana ƴan fashin dajin a matsayin ƴan ta'adda, duk da cewa ba su da wani buri na siyasa ko addini.

  4. Ɗan takarar ɓangaren hamayya ya yi nasara a zaɓen Cape Verde

    José Maria Neves

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, José Maria Neves

    Sakamakon zaɓe na wucin gadi da ke fitowa daga Cape Verde na nuna cewa babban ɗan takara na ɓangaren goran hamayya, José Maria Neves ya yi nasara a zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasa.

    Ƴan takara bakwai ne suke neman maye gurbin Shugaba Jorge Carlo Fonseca, wanda ba zai iya yin sama da wa'adi biyu ba.

    Mista Neves na da kashi 51 cikin 100 idan aka kwatanta da kashi 43 cikin 100 na ɗan takarar jam'iyya mai mulki Carlos Veiga.

    Idan aka tabbatar da wannana sakamakon, hakan zai tabbatar da nasarar Mista Neves ba tare da zuwa zagaye na biyu na zaɓen ba.

    Mista Veiga ya amince da faɗuwa zaɓen a talabijin kuma ya taya Mista Neves murna kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

  5. Sheikh Zakzaky da matarsa sun kai ƙarar gwamnatin Najeriya

    Zakzaky da Matarsa

    Asalin hoton, OTHERS

    Sheikh Ibraheem Zakzaky da matarsa Malama Zeenah sun maka gwamnatin Najeriya a babbar kotun kasar don ƙalubalantarta kan ƙwace masu fasfo ɗinsu da Hukumar Jami'an Tsaro ta Farin Kaya ta DSS da Antoni Janar na ƙasar suka yi.

    Sheikh Zakzaky da Malama Zeenah, ta bakin lauyan da ke wakiltarsu, Mr Femi Falana sun bayyana wa kotu cewa an yi wa fasfo ɗin nasu gani na ƙarshe ne a hannun Hukumar Leƙen Asiri ta Najeriya, kuma hukumar ta musanta cewa suna hannunta.

    Tuni dai malamin da matarsa suka ayyana cewa fasfo ɗin nasu sun bata, sai dai da suka yi ƙoƙarin sabuntawa a ofishin Hukumar Shige da Fice, an shaida masu cewa Hukumar DSS ta dakatar da fasfo ɗin saboda ana gudanar da bincike a kansa.

    Sheikh Zakzaky da matarsa sun buƙaci kotu ta tursasa wa hukumomin su sakar masr fasfo ɗinsu ko kuma a ɗage dakatarwar.

    Haka kuma, sun buƙaci kotun ta sa hukumomin su biya su naira biliyan biyu a matsayin diyya don ɓata masu suna da shiga haƙƙinsu da aka yi.

    Sannan sun ce karɓe masu fasfo ɗin barazana ce ga rayuwarsu tunda an hana su fita Najeriya don samun kulawar likita a asibiti.

  6. Labaran Duniya Cikin Minti Daya da BBC Hausa

    Bayanan sautiMinti Daya da BBC Hausa Na Safe 18/10/2021
  7. Ƴan bindiga sun kashe mutum 31 a makon da ya gabata a Najeriya

    Ƴan bindiga

    Asalin hoton, OTHERS

    Ƴan bindiga sun kashe a ƙalla mutum 31 a hare-hare daban-daban a faɗin Najeriya a makon da ya gabata.

    Alƙaluman sun nuna cewa sojoji 10 da fararen hula 21 ne lamarin ya shafa.

    Jaridar Premium Times a Najeriya ce ta tattara alkaluman wanda ta samo daga rahotannin kafafen yaɗa labarai, don haka ta ce alkaluman ba su shafi hare-haren da ba a bayar da rahotonsu ba.

    Sai dai jaridar ta ce an samu ɗan ragi a yawan mutanen da aka kashe idan aka kwatanta da na wancan makon inda aka kashe a ƙalla mutum 41.

    Sai dai an samu karuwa a yawan jami'an tsaron da aka kashe.

    Ta ce mafi yawan hare-haren da aka yi a makon da ya gabata ƴan bindiga ne suka kai su a arewa maso yammacin Najeriyar.

    Yayin da ta ce ba a ruwaito mutuwar mutum ko ɗaya ba sanadiyyar ayyukan yan bindiga a yankunan kudu maso kudu da kudu maso yammacin ƙasar.

  8. Za a ci gaba da tattaunawa kan sabon kundin tsarin mulkin Syria

    Bayan shafe watanni 9 ba tare da an sake tado batun sake sabon kundin tsarin mulkin kasar Syria, a yau shugabanni da wakilai za su sake komawa kan teburi a birnin a Geneva.

    Wannan tattaunawa wani dadadden kokari ne na Majalisar Dinkin Duniya, domin hada dukkan bangarorin al'ummar Syria a kokarin samar da sabon kundin tsarin mulki, ta gudanar da zabe, da gina dorarriyar hanyar tabbatar da zaman lafiya a kasar bayan shafe sama da shekaru 10 ta na cikin yaki.

    Wani jami'in Majalisar Dinkin Duniya kenan ya ke cewa ba wai kawai za mu shirya yin sauye-sauye a kundin tsarin mulki ba, a'a za mu shirya da fara rubuta sabon kundin tsarin mulkin.

    Kwamitin mai mambobi 45 sun gana har sau 5, amma ba su cimma matsayar azo a gani ba. A jiya Lahadi MDD ta yi nasarar gayyato wakilan bvangaren gwamnati da na 'yan adawa tare da rokon su fara shirin samar da sabon kudurin.

    Sama da Siriyawa dubu 500, ne yakin basasar kasar ya hallaka, ya yin da kusan rabin al'ummar kasar suka rasa muhallansu.

  9. Ana ci gaba da aikin ceto a Indiya bayan ambaliyar ruwa

    Indiya

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyoyi daban-daban, da sojoji da hukumar kare hauɗrra da bala’i na Indiya su na ci gaba da aikin ceton wadanda suka tsira daga mummunar ambaliyar ruwan da jihar Kerala ta fuskanta a dan tsakanin nan.

    Sai dai aikin na fuskantar cikas, koguna sun tumbatsa, ya yin da nan da sa’o’I hudu masu zuwa ake sa ran za a bude madatsun ruwan jihar.

    Hukumomi sun ce daruruwan iyalai daga yankunan matalauta aka kwashe zuwa tudun mun tsira.

    Ruwan saman da aka kwashe kwanaki ana shekawa shi ya haddasa ambaliyar ruwan, wadda ta yi sanadin mutuwar mutuwar sama da mutum 26 ciki har da yara, ya yin da ake has ashen adadin mamatan ka iya fin haka.

  10. Har yanzu ba a san inda Mishan ɗin Amurka da aka sace a Haiti suke ba

    Rahotanni daga Amurka na cewa gwamnati ba ta san inda aka kai kungiyar Kiristocin Mishan da iyalansu da 'yan bindiga suka sace a kasar Haiti a ranar Asabar din karshen mako.

    Masu satar mutane sun sace su ne a lokacin da suka dawo daga wata ziyara gidan marayu, kuma sha shida daga cikinsu Amurkawa ne sai kuma dan Canada daya.

    Kungiyar agaji ta Amurka mai suna Christian Aid Ministries, ta tabbatar da sace mabobin na ta, tare da cewa a cikin wadanda aka sacen akwai yara biyar, shi ya kawo adadin mutanen 21.

    Hukumomi a Haiti ta ce kungiyar masu satar mutane ta 400 Mawozo ta sace su, wadda ako a watan Afirilu sun sace wani malamin darikar Katolika, Satar mutane don neman kudin fansa ta zama ruwan dare a kasar Haiti,m ya yin da lamarin tsaro ya kara tabarbarewa a kasar sun bayan kashe shugaba Jovenel Moïse a watan Yuli.

  11. Maraba

    Barkanku da kasancewa da mu a wannan shafin wanda ke kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Ghana da sauran makwabtanta.

    Kun karya kumallo?

    Abinci

    Asalin hoton, Getty Images