Ƙarin mutum 32 sun kamu da korona a Kaduna
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta Najeriya ta ce ƙarin mutum 161 sun kamu da
korona a ranar Juma’a a ƙasar.
Alƙalumman sun nuna cewa an samu ƙarin mutum 45 da suka kamu da cutar a Lagos, yayin da kuma ƙarin mutum 32 suka kamu a Kaduna.
A jihar Zamfara mai fama da matsalar tsaro an samu mutum biyar da suka kamu da cutar a ranar Juma’a, kamar yadda NCDC ta bayyana.
Jimillar mutum 205,926 cutar ta shafa a Najeriya yayin da ta kashe mutum 2,723.
Ga jerin jihohin da aka samu ƙarin cutar:
Lagos-45
Kaduna-32
Ondo-28
Kwara-12
Rivers-11
Edo-8
Ekiti-5
Niger-5
Zamfara-5
Plateau-4
Nasarawa-3
FCT-2
Oyo-1
