Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Sojoji sun dakile hari kan tubabbun 'yan Boko Haram

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau

  1. Ƙarin mutum 32 sun kamu da korona a Kaduna

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta Najeriya ta ce ƙarin mutum 161 sun kamu da

    korona a ranar Juma’a a ƙasar.

    Alƙalumman sun nuna cewa an samu ƙarin mutum 45 da suka kamu da cutar a Lagos, yayin da kuma ƙarin mutum 32 suka kamu a Kaduna.

    A jihar Zamfara mai fama da matsalar tsaro an samu mutum biyar da suka kamu da cutar a ranar Juma’a, kamar yadda NCDC ta bayyana.

    Jimillar mutum 205,926 cutar ta shafa a Najeriya yayin da ta kashe mutum 2,723.

    Ga jerin jihohin da aka samu ƙarin cutar:

    Lagos-45

    Kaduna-32

    Ondo-28

    Kwara-12

    Rivers-11

    Edo-8

    Ekiti-5

    Niger-5

    Zamfara-5

    Plateau-4

    Nasarawa-3

    FCT-2

    Oyo-1

  2. Maraba

    Muna maku maraba da kasancewa da mu a wannan shafin inda za mu kawo labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da sauran sassan duniya.

    Sai ku kasance da mu