Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Sojoji sun dakile hari kan tubabbun 'yan Boko Haram

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau

  1. Sojoji sun dakile hari kan tubabbun 'yan Boko Haram

    Dakarun rundunar sojin Najeriya sun dakile wani hari da mayakan ISWAP suka yi yunkurin kai wa sansanonin da tubabbun 'yan Boko Haram ke samun mafaka a karamar hukumar Damboa da ke jihar Bornon Najeriya.

    Kafar yada labaran PR Nigeria ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a yau Asabar.

    Dakarun sun fatattaki masu ta da kayar bayan ne wadanda suka shiga garin a cikin jerin gwanon motoci masu sulke.

    Hakan na zuwa ne kwana guda bayan da mayakan Boko Haram suka tarwatsa mayakan ISWAP a yankin Gwoza.

    PR Nigeria ta ce majiyoyi sun tabbatar da cewa bayanan sirri sun gano ISWAP ta shirya far wa sansanin da tubabbun mayan Boko Haram ke zaune ne.

    Daruruwan tubabbun 'yan Boko Haram ne ke zaune a wajen tun bayan mika wuyansu.

    Majiyar ta ce dakaru sun dakile harin bayan musayar wuta kuma da yawan 'yan ISWAP din sun rasa rayukansu.

  2. Buhari ya ba da lambar yabo ga dan Najeriyar da ya rasu wajen ceto mutum 14 a jihar Ribas

    Shugaba Najeriya Muhammdu Buhari ya bayar da lambar yabo ta girmamawa ga iyalan wani dan kasar da ya rasa ransa a wajen ceto mutanen da kwale-kwale ya kife da su.

    A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau, shugaban ya ce ya mika lamar girmamawar ne ranar Alhamis ga iyalan marigayi Joseph Blankson.

    Mista Blankson ya rasu ne rabar 28 ga Yulin 2018 bayan da ya ceto mutum 13 amma ya nutse a cikin ruwa a kokarin ceto na 14 a hanyar ruwa ta Abinnema-Bakana a jihar Ribas da ke kudancin kasar.

    Dukkan wadanda kwale-kwalen ya kife da su sun tsira sakamakon taimakonsa sai shi kadai da ya rasu.

    Yayin da yake mika wa matar mamacin Mercy da 'ya'yansa biyu lamabar yabon a fadarsa da ke Abuja, Shugaa Buhari ya ce "Ina gabatar da wannan lamabar yabo ta shugaban kasa ga Mercy da 'ya'yanta biyu saboda jinjinawa gwarzantakar mijinta."

    "Za mu ci gaba da jinjinawa duk wani abin kirki na Najeriya ko dan Najeriya, a yayin da muke fatan samun nasara a kasarmu," in ji Shugaba Buhari.

  3. Jirgin da Turai ta aika ya aiko hotunan duniyar Mercury

    Wani jirgin sama jannati na BepiColombo da Turai ta aika duniyar Mercury ya dawo da hotunan farko na duniyar da ta fi kusanci da rana.

    Jirgin da aka tura don binciken ya dauki hotunan ne bayan da ya kurda ta saman 'yar karamar duniyar a tafiyar kilomita 200 daga saman dandaryarta.

    Masu kula da binciken sun shirya aika irin wadannan jirage biyar, inda a ko yaushe za su yi amfani da maganidisun Mercury don taimaka wa wajen kayyade gudun jirgin sama jannatin.

    Manufar ita ce Bepi zai dinga tafiya a hankali ta yadda a karshe zai iya kammala zagaya duniyar gaba dayanta. Hakan zai kammala ne zuwa karshen shekarar 2025.

    Hotunan farko na Mercury an dauke su ne da kyamarori marasa fitar da kyan hoto sosai da ake sa ido a kansu daga can bangaren masu binciken.

    Zuwa yanzu dai iyakar hotunan da aka iya daukowa kenan. A yanzu jirgin Bepi bai shirya aika manyan kyamarorinsa na kimiyya masu fitar da kyan hoto ba tukunna.

    An boye su a can wata kurya ta cikin jirgin sama jannatin. Bepi dai jirgi biyu ne a cikin daya. Bangare daya Hukumar Sararin Samaniya ta Turai ce ta samar da shi yayin da Hukumar Sararin Samaniya ta Japan ta samar da dayan.

  4. Amsoshin Takardunku: Bayani kan abubuwan da ke haifar da ambaliyar ruwa

  5. Bam ya kashe wata amarya a wurin ɗaurin aurenta a Afghanistan

    Rahotanni daga arewcin Afghanistan na cewa wani bam da ya fashe a wurin daurin aure ya yi sanadiyya mutuwar mutum hudu ciki har da amarya a lardin Jowzjan.

    Wani dan jarida ya ce mutane da dama sun jikkata a yayin bikin wanda ya gudana a wani otel a yankin Aqcha.

    Har yanzu dai ba a san wanda ya kai harin ba.

    Gabanin wannan harin, wani bam na daban da ya tashi a cikin ababen hawa a Jalalabad ya kashe mutum hudu ciki har da wasu 'yan Taliban biyu.

    Shi ma dai babu kungiyar da ta dauki alhakin kai shi.

  6. Ministocin muhalli na duniya sun yi ganawar ƙarshe kafin taron MDD na watan gobe

    Ministocin muhalli da na makamashi na duniya sun kammala tattaunawarsu ta karshe gabanin babban taron MDD da za a yi a Glasgow, inda suka ce har yanzu akwai sauran runa a kaba kan matsalar sauyin yanayi.

    Shugaban taron da za a yi a watan gobe kuma ministan gwamnatin Burtaniya Alok sharma ya ce akwai yarjejeniyar cewa kasashe masu arziki za suka kara himma a wannan tafiya.

    Alok Sharma ya ce damuwar da mata suka nuna kan sauyin yanayi, ina ganin za ta kara zaburar da ministocin nan, kuma a bayani na na rufe taro na fadi cewa dole mu fara sauraren ra'ayoyinsu a yayin taron watan gobe.

    Ministocin sun ce babu jayya kan cewa matsalar sauyin yanayi na yin barazana ga rayuwar duka wani dan adam a fadin duniya.

  7. Shugaba Buhari zai tafi Habasha

    Shugaba Muhammadu Buhari zai je Habasha don halartar taron rantsar da Firai Ministan Habasha Abiy Ahmed a wa'adinsa na biyu ranar Litinin a Addis Ababa.

    Shugaban zai bar Abuja ranar Lahadi zuwa babban birnin Habasha kuma ana sa rai zai gabatar da jawabin fatan alheri a taron rantsuwar.

    Daga nan kuma zai halarci liyafar cin abinci tare da sauran shugabannin ƙasashe.

    Ministan harkokin ƙasashen waje Geoffery Onyeama da Shugaban Hukumar Leƙen Asiri ta NIA, Ambasada Ahmed Rufai Abubakar ne za su yi wa Shugaba Buhari rakiya.

    Zai dawo Abuja ranar Talata.

  8. Yadda ake zaɓen ƴan majalisa a Qatar karon farko

    Al’ummar Qatar na gudanar da zaɓen majalisar Shura a ƙasar, kuma wannan shi ne irinsana farko da za a zabi ƴan majalisa.

    A baya dai sarkin Qatar mai karfin fada a ji, Sheikh Tamim Bin Hamad Al Thani ne yake zaɓar ƴan majalisar Shura.

    Kusan kashi 10 cikin 300 na ‘yan takarar mata ne.

    Masu zaɓe za su zaɓi kashi biyu bisa uku na majalisar Shura.

    Shura ke da haƙƙin kula da kasafin kuɗin kasar, da amincewa ko akasin haka da tsare-tsare da batutuwan da suka shafi ci gaban kasar.

    Sai dai sarki Tamim Bin Hamad ne ke zartar da hukunci na karshe kan kowanne batu.

    A bangare guda kuma babu jam’iyyar siyasa ko daya a daukacin kasar Qatar.

  9. Everton ta riƙe Man Utd a Old Trafford

    Everton ta riƙe Manchester United a karawar Premier League da suka yi a Old Trafford.

    An tashi wasan ne ci 1-1. Anthony Martial ne ya fara ci wa Manchester United ƙwallo a ragar Everton kafin daga bisani Andros Townsend ya farke ƙwallon bayan an dawo hutun rabin lokaci.

    Yanzu Manchester United tana matsayi na uku da maki 14, yayin da ita ma Everton da ke maki 14 amma a matsayi na huɗu a tebur.

  10. Hira da Sarkin Zazzau kan cikarsa shekara daya

  11. Saudiyya ta ƙara yawan masu Ibadah a Masallacin Harami

    Hukumomin Saudiyya sun ƙara yawan masu yin ibadah a masallacin Harami.

    Ma'aikatar kula da harakokin Hajji da Umrah ta ƙara yawan masu Ibadah daga 70,000 zuwa 100,000 kamar yadda Shafin Haramain Sharifain da ke kula da Masallatai biyu mafi daraja na Makkah da Madina ya bayyana.

  12. Ƴan Chadi na zanga-zangar adawa da mulkin soji

    Ƴan sandan Chadisun tarwatsa masu zanga-zanga da hayaƙi mai sa ƙwalla a Ndjamena babban birnin ƙasar, inda daruruwan mutane suka fito suna adawa da shugabannin soji.

    Magoya bayan 'yan adawa sun ce mutane da dama sun jikkata.

    Ƴan sanda sun ce sun yi harbi ne kan masu zanga -zangar saboda sun ƙetara iyaka, ba su tsaya kan hanyar da aka ba su izinin yin zanga-zangar ba.

    Sojojin sun karɓe iko ne a watan Afrilun bana bayan mutuwar shugaba Idriss Deby.

    An naɗa ɗansa, Janar Mahamat Deby, a matsayin shugaban ƙasa.

    A kwanan ne sabon shugaban ya ce za a iya tsawaita wa’adin da aka ɗiba na miƙa mulki watanni goma sha takwas idan ba a cika wasu sharuɗɗa ba.

  13. Ƴan bindiga sun sace Babban Sakatare a jihar Neja

    Ƴan bindiga sun sace babban sakatare a ma’aikatar sufuri ta jihar Neja da ke arewacin Najeriya.

    An sace Dakta Ibrahim Garba Musa ne da asubahin yau tare da ɗansa, kamar yadda sakatariyar watsa labarai ta Gwamnatin jihar, Mary Noel Berje, ta shaida wa BBC.

    Ta ce har yanzu ba su gama tattara bayanai ba game da al’amarin amma ta ce a gidansa da ke Zungeru a ƙaramar hukumar Wushishiƴan bindiga suka abka suka sace shi da ɗansa.

    Wasu rahotanni sun ce an sace shi ne gidansa bayan kammala bikin aure.

    Wannan na zuwa bayan gwamnatin Neja ta tabbatar da mutuwar sojoji biyu da jikkata wasu da dama a harin da ƴan bindiga suka kai a yankin Kagara.

  14. Budurwar Khashoggi ta ƙalubalanci Biden kan Saudiyya

    An gudanar da zanga-zanga a wajen ofishin jakadancin Saudiyya da wajen majalisar dokokin Amurka da ke birnin Washington, domin tunawa da cika shekara uku da kisan ɗan jarida kuma ɗan asalin kasar Saudiyya wato Jamal Khashoggi.

    Wadda zai aura Hateice Cengiz 'yar kasar Turkiyya, ta yaye kyallen da aka rufe wani hoton Mista Khashoggi a jaridar Washington Post da yake yi wa rubutu a kowanne mako gabannin mutuwarsa.

    Ta buƙaci shugaban Amurka Joe Biden ya cika alƙawalin da ya ɗauka.

    “Shugaba Biden da mataimakiya Harris, ba za ku cika alƙawalin da suka ɗauka ba, ba za ku yi aiki da kalamanku ba, duk da alƙawalin da kuka yi?” in ji ta.

    An yi wa Kashoggi kisan wulaƙanci ta hanyar makurushe shi har saida ya daina numfashi, tare da yin gunduwa-gunduwa ta sassan jikinsa a karamin ofishin diflomasiyyar Saudiyya da ke birnin Santambul na kasar Turkiyya.

    An yi zargin cewa wata tawagar mutum 15 daga Saudiyya ne suka aikata kisan dan jaridar da ya yi ƙaurin suna wajen sukar masarautar Saudiyya.

    Kisan ya faru ne bayan ya yi wani rubutu da ya yi suka ga Yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman, wanda ake nuna wa yatsa da alhakin kisan na shi.

  15. Ƴan bindiga sun kashe sojojin Najeriya biyu a jihar Neja

    Gwamnatin Neja a arewacin Najeriya ta tabbatar da mutuwar sojojin Najeriya biyu a wani hari da ƴan bindiga suka kai yankin Kagara a jihar.

    Gwamnnan Neja Abubakar Sani Bello ne ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa daga ofishinsa

    Sanarwar ta ce gwamnan ya ziyarci sojoji 12 da ke kwance a asibitin Ibrahim Badamasi Babangida a Minna waɗanda suka samu rauni a harin.

    Gwamnan ya ce an tafi da wasu sojojin zuwa Kaduna domin kula da lafiyarsu.

    Ya ce ƴan bindiga da dama ne aka kashe amma ba tare da gwamnan ya bayyana adadinsu ba.

    Jihar Neja na cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalolin ƴan bindiga masu fashin daji da satar mutane domin kuɗin fansa.

  16. Lafiya Zinariya: Shin ko teɓa na hana haihuwa?

    Likitoci sun ce kibar da ta wuce kima nau'i biyu ce, ta waje da kuma ta cikin mutum. Sai dai ta cikin ta fi hadari, domin ta kan shafi al'adar mace.

    Hukumar lafiya ta duniya, WHO ta ce an fi samun mutane masu teba, a kan wadanda kibarsu ta wuce kima, a kowane yanki na duniya.

    Amma ban da yankin Kudu da hamadar Sahara Afrika da kuma yankin Asia.

    A cewar hukumar wannan matsalar a baya ta fi kamari ne a kasashen da suka ci gaba.

    Sai dai a yanzu matsalar teba na karuwa a kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga, musamman a birane.

    WHO ta bayyana cewa matukar kiba ko teba da kan shafi kiwon lafiya, abu ne da ya kai matakin annoba a duniya.

    Inda kimanin mutane fiye da miliyan hudu ke mutuwa duk shekara, a dalilin hakan.

  17. An cire kilon ƙusoshi da ƙarafa a cikin wani mutum

    Likitoci sun cire kilon ƙusoshi da noti-noti da wuƙaƙe daga cikin wani ɗan ƙasar Lithuania.

    Likitoci sun ce ya shafe wata guda yana haɗiye ƙarafa bayan ya daina shan barasa.

    Wasu daga cikin abubuwan da aka cire yayin aikin tiyata a Asibitin Jami'ar Klaipeda sun kai tsawon inci 4in, a cewar kafar yada labaran LRT ta Lithuania.

    Likitan da ya yi aikin tiyatar Sarunas Dailidenas ya bayyana al’amarin a matsayin ‘abin mamaki’

    Kafar LRT ta wallafa hoton wani faranti cike da ƙarafa da aka cire bayan tiyatar da aka shafe sama da sa’a uku.

    An kawo mutumin ne asibiti cikin motar ɗaukar marar lafiya zuwa yana fama da tsananin ciwon ciki.

    An bayar da rahoton cewa yanzu mutumin yana farfaɗowa a asibiti.

  18. Papua New Guinea za ta yi gwanjon motocin alfarma

    Papua New Guinea ta amince cewa ta yi "babban kuskure" yayin da take ƙoƙarin sayar da motocin alfarma na sama da dala miliyan biyar da rabi da aka saya don a burge ƴan siyasa yayin taron shugabannin yankin Pacific.

    Gwamnatin wancan lokacin ta yi alfahari da cewa motocin ƙirar Maserati za a sayar da su bayan an yi amfani da su don taron Hadin gwiwar Tattalin Arzikin Asiya-Pacific (Apec) na 2018.

    Sayen motocin na alfarma ya haifar da ce-ce -ku-ce, inda wasu shugabanni suka ki amfani da su.

    Yanzu kasar - ɗaya daga cikin matalautan yankin Pacific - za ta sayar da su cikin asara.

    "Idan da muna da hangen nesa, bai ma kamata a sayi Maseratis ba tun da farko," kamar yadda Ministan Kudi na ƙasar Sir John Pundari ya shaida wa kafofin watsa labaraii na cikin gida.

    Ya kara da cewa "Ban san dalilin da ya sa muka saye motocin ba, yanzu ga shi nan mun shiga damuwa.”

    Yanzu za a sayar da ko wace ɗaya kan dala 114,000, kusan asarar kashi 20 na asalin kuɗin da aka sayi motar.

  19. Korona ta kashe fiye da mutum dubu 700 a Amurka

    Jami’ar Johns Hopkins ta Amurka da ke tattara alƙalumman cutar korona a duniya, ta ce adadin waɗanda cutar Korona ta yi ajali daga lokacin ɓarkewarta kawo yanzu a ƙasar ya haura dubu 700.

    Wannan adadi shi ne baki ɗayan yawan mazauna birnin Washington, kuma shi ne mafi yawa da wata ƙasa ta fuskanta a duniya.

    Korona na ƙara yaɗuwa a Amurka musamman sabon nau’in Delta, inda lamarin ya fi kamari a jihohin kudancin kasar.

    Bayan kakkausar sukar da aka fuskanta kan yadda gwamnati ta tunkari annobar korona, a yanzu an yi wa kusan rabin Amurkawa cikakkiyar rigakafin korona.

    A duniya baki daya, sama da mutum miliyan biyar aka tabbatar da mutuwarsu, sanadiyar cutar korona. Sai dai kwararru a fannin lafiya na cewa adadin ka iya fin haka saboda wadanda ke mutuwa a gida ba tare da an san takamaimai abin da ya yi ajalinsu ba.

  20. Zanga-zangar ɗalibai ta sa an rufe Jami’ar Obafemi Awolowo

    Hukumomin Jami’ar Obafemi Awolowo da ke jihar Osun a kudancin Najeriya sun rufe jami’ar har sai ‘baba ta gani’

    An rufe jami’ar ne bayan zanga-zangar da ɗalibai suka gudanar domin nuna fushinsu kan mutuwar wata ɗaliba a asibitin jami’ar.

    Sanarwar da hukumomin jami’ar suka fitar, ta ba ɗalibai wa’adi zuwa 12 na ranar Asabar su fice.

    Daliban jami’ar sun fito saman titi suna zanga-zanga inda suka rufe manyan hanyoyin ababen hawa a yankin.