Sojoji sun dakile hari kan tubabbun 'yan Boko Haram
Dakarun rundunar sojin Najeriya sun dakile wani hari da mayakan ISWAP suka yi yunkurin kai wa sansanonin da tubabbun 'yan Boko Haram ke samun mafaka a karamar hukumar Damboa da ke jihar Bornon Najeriya.
Kafar yada labaran PR Nigeria ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a yau Asabar.
Dakarun sun fatattaki masu ta da kayar bayan ne wadanda suka shiga garin a cikin jerin gwanon motoci masu sulke.
Hakan na zuwa ne kwana guda bayan da mayakan Boko Haram suka tarwatsa mayakan ISWAP a yankin Gwoza.
PR Nigeria ta ce majiyoyi sun tabbatar da cewa bayanan sirri sun gano ISWAP ta shirya far wa sansanin da tubabbun mayan Boko Haram ke zaune ne.
Daruruwan tubabbun 'yan Boko Haram ne ke zaune a wajen tun bayan mika wuyansu.
Majiyar ta ce dakaru sun dakile harin bayan musayar wuta kuma da yawan 'yan ISWAP din sun rasa rayukansu.