Tsohon dan majalisar Malawi ya harbe kansa a wajen majalisar

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge

  1. Za a daina yi wa marasa NIN Fasfo da lasisin tuki - NCC

    VH

    Asalin hoton, KH

    Hukumar dake lura da harkokin sadarwa ta Najeriya NCC ta shawarci masu amfani da harkokin sadarwa su hada layukan wayarsu da lambarsu ta katin dan kasa nan da ranar 31 ga watan Oktoba, wanda shi ne wa'adin da aka sanya.

    Hukumar ta ce nan ba da jimawa ba za a fara hana wadanda ba su da lambar NIN damar samun wasu abubuwa na gwamnati ciki har da lasisin tuki da fasfo.

    Da yake bayani cikin wani shiri na kai tsaye daraktan kula da harkokin jama'a Dr. Ikechukwu Adinde, ya shawarci mutane da su yi amfani da wannan dama ta kara lokacin rijistar da aka yi zuwa ranar 31 ga watan Oktoba domin hada NIN da layikan wayarsu.

    "Kwanan nan za a fara hana mutanen da ba su da NIN damar samun wasu abubuwan da suke da bukata a rayuwarsu ciki har da lasisin tuki da na fasfo.

  2. Mutum 116 ne suka mutu a ricikin gidan yari a Ecuador

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Ecuador, Guillermo Lasso, ya tabbatar da mutuwar fursunoni 116 a tarzomar da ta barke a gidan kasoda ke birnin Guayaquil da ke gabar teku a ranar Talata.

    An yankewa da dama daga cikin fursunonin ko dai hannu ko kuma kafafu, a tarzoma mafi muni da aka taba yi a wani gidan kaso da ke kasar. Inda akai mfani da bindiga, da aduna da gurneti da aka hada a gida da sauran muggan makamai a lokacin yamutsin.

    Tuni shugaba Lasso ya ayyana dokar ta baci a birnin, ya kara da shan alwashin daukar matakan da suka da ce domin tabbatar da hakan ba ta sake faruwa ba.

    Da zuba miliyoyin daloli domin inganta rayuwa a gidan kason da wannan na daga cikin dalilan da ake yawan samun tashin hankali tsakanin fursunoni lamarin da ke kaiwa ga hasarar rayuwaka.

  3. A yau Isra'ila take bude ofishin jakadancinta a Bahrain

    Reuters

    Asalin hoton, Reuters

    Ministan harkokin tsaron Isra'ila Yair Lapid zai je Bahrain a yau domin bude ofishin jakadancin kasarsa a Manama.

    Wannan ce ziyarar farko da ministan zai yi a masarautar ta Bahrain tun bayan sabunta alakar diflomasiyyar kasashen biyu a bara.

    Bude ofishin jakadancin na daga cikin wasu yarjejeniyoyin da aka cimma a lokacin tsohon shugaban Amurka Donald Trump.

    Karkashin sabunta alakar da kuma yarjejeniyar da aka cimma, Isra'ila za ta bude ofishin jakadancinta a kasashen Morocco da Sudan da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa.

  4. Me yasa kasashen Afrika ba su damu da yi wa mutanensu rigakafin korona ba?

    WHO

    Asalin hoton, WHO

    Hukumar lafiya ta duniya ta ce kasashen Afurka 14 ne kacal suka yi wa sama da kasha 10 cikin 100 na al’ummarsu rigakafin cutar korona duk da tarin jama’ar da suke da ita.

    World Health Organization has said that only fourteen African countries have vaccinated more than ten per cent of their populations against Coronavirus.

    Cikin kasashen Seychelles, Mauritius da Morocco ne kadai suka yi rawar gani, ind suka yi wa kasha 40 cikin 100 rigakafin cutar.

    Baki daya dai a nahiyar Afurka, kasha 40 ne suka yi cikakkiyar rigakafin cutar korona, idan aka kwatanta da kasha 60 na Tarayyar Turai.

    Manufar shirin Covax dai shi ne taimakawa kasashe masu karamin karfi da allurer rigakafin korona kusan miliyan dari 3, said ai hakan ba ta samu ba sakamakon yadda kasashe masu karfi suka saye ta.

  5. Siyasantar da harkokin tsaro ne ke ta'azzara al'amura a Najeriya - Zulum

    Zulum

    Asalin hoton, Zulum

    Gwamnan jihar Borno da ke arewacin Najeriya Babagana Umara Zulum ya yi zargin cewa siyasa da aka sanya wajen daukar jami'an tsaro a kasar ita ke kara dagula al'amura, abin da ya jefa harkokin tsaron kasar a hannun masu neman aiki.

    Zulum ya bayyana haka a ranar Laraba lokacin da yake gabatar da wata makala Kuru da ke jihar Plateau.

    Zulum ya kara da cewa matukar ba muyi abin da ya dace ba, babu abin da zai tafi dai-dai.

  6. Karin mutum 437 sun kamu da korona a Najeriya

    BBC

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 437 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar a ranar Litinin.

    Hukumar ta ce akasarin waɗanda suka kamu da cutar a jihar Legas suke inda aka samu ƙarin mutum 126 da suka kamu da cutar a jihar yayin da jihar Ribas aka samu mutum 76 da suka kamu da cutar sai kuma jihar Kwara da aka samu mutum 44.

    Ga jerin jihohin da aka samu bullar cutar ranar Litinin:

    •Lagos-126

    Rivers-76

    Kwara-44

    FCT-37

    Edo-32

    Kaduna-30

    Anambra-22

    Delta-22

    Osun-12

    Benue-7

    Abia-6

    Nasarawa-6

    Kano-5

    Ekiti-3

    Plateau -3

    Bayelsa-2

    Ogun-2

    Oyo-2

    A jumullance, adadin mutanen da suka kamu a faɗin ƙasar sun kai 205,484 sai dai 193,482 sun warke.

    Akwai kuma mutum 2,701 da suka mutu

  7. Barkan da Hantsi

    Masu bibiyarmu a wannan shafi Buhari Muhammad Fagge ne ke fatan an wayi gari lafiya, ni ke fatan kasancewa da ku a wannan yini domin kawo mulu labarai da rahotanni daga sassan duniya daban daban.

    Labarai masu ilimantarwa da nishadantarwa a wasu lokutan masu ban haushi, ku kasance da mu.