Tsohon dan majalisar Malawi ya harbe kansa a wajen majalisar
Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya
Rahoto kai-tsaye
Buhari Muhammad Fagge
Mu kwan lafiya
Masu karanta labarai da rahotanni da muke kawowa kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, a nan muke rufe shafin a yau.
Sai kuma gobe da safe idan Allah Ya kai mu.
Kar a manta a koma kasan shafin don karanta labaran da muka wallafa tun safe.
Asuba ta gari.
An kama tsohuwa 'yar shekara 96 kan laifin kisan mutane da dama a yaƙin duniya na II
Yan sanda a Jamus sun damke wata tsohuwa mai shekara 96 da ta ƙi bayyana gaban kotu don fuskantar tuhume-tuhumen da ake mata na hannu a kisan mutane da dama a sansanin gwale-gwale na yan Nazi a lokacin yakin duniya na biyu.
Irmgard Furchner ta fice daga wani gidan ba da kulawa a kusa da Hamburg cikin tasi, sa'o'i kafin a gurfanar da ita gaban kotu.
Tsohuwar da ake tuhuma da
hannu wajen kashe fiye da mutum 11,000 ta ki halartar shari'ar da za a mata.
Tun da farko, Irmgard
Furchner ta shiga wata tasi daga gidan kula da tsofaffi a wajen birnin Hamburg
kuma ta nausa wani wajen da ya yi hannun riga da inda kotun take.
Daga baya an kama ta - yayin da take tafiya a kafa a wani layi.
Masu shigar da kara sun ce ta taimaka wajen kisan da aka yi wa fiye da
fursunoni 11,000 yayin da take aiki a matsayin mai aiki da keken rubutu a wani
sansanin da ake tsare fursunonin yaki kusa da birnin Gdansk a kasar Poland.
Wata kakakin kotun - Friederike Millhoffer - ta shaida wa manema labarai
cewa an kai Ms Furchner wani wurin na dabam:
“Ina iya tabbatar muku cewa an gano matar da ake tuhuma. Za a kuma kai ta
kotun, kuma wani likita zai duba lafiyarta domin tabbatar da za a iya tsare ta
a gidan yari, kuma kotun za ta yanke hukunci kan ko a tsare ta a kurkuku.“
Shekarun Ms Furchner 18 a lokacin da ta fara aiki a matsayin sakatariya a
sansanin tsare fursunoni na Stutthof inda aka halaka fursunoni 65,000.
Lauyoyin ta sun ce ba ta
da masaniya kan ta'asar da aka tafka a sanasanin.
Angela Merkel ta kira Shugaba Buhari a waya don yin bankwana
Asalin hoton, Getty Images
Shugabar gwamnatin Jamus mai barin gado Angela Merkel da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya sun tattauna ta wayar tarho.
A tattaunawar tasu wacce Merkel ta kira, shugabannin biyu sun yi waiwaye kan dangantakar da ke tsakanin Jamus da kasashen Afirka musamman Najeriya a lokacin shugabancin Merkel.
Wata sanarwa daga fadar shugaban Najeriya ta ce Shugaba Buhari ya yabi shugabar gwamnatin Jamus din kan tsarinta na bude wa 'yan gudun hijira kofa da 'yan ci rani da kuma taimakon da ta dinga bai wa kasashe masu tasowa.
Shugaban na Najeriya ya ce ya gamsu sosai tare da yaba wa Jamus kan hadin kan da ta dinga bai wa Najeriya, da yankin Afirka Ta Yamma baki daya.
Ya kuma ambaci goyon bayan da gwamnatinta ta bai wa shirin farfado da Tafkin Chadi, ta hanyar samar masa ruwa daga wasu tafkunan, wanda "zai taimaka wajen farfado da rayuwar kusan mutum miliyan 30" da suka dogara da tafkin don samun abin rufin asiri.
Sanarwar ta ambato Shugaba Buhari na bayyana shugabar gwamnatin Jamus a matsayin "wata muhimmiyar shugaba mace abar misali wacce ta damu da abubuwan da ke faruwa a duniya da son hadin kai" kamar yadda ya bayyana ta a gaban taron Majalisar Dinkin Duniya.
A nata bangaren, shugabar gwamnatin Jamus mai barin gado Angela Merkel ta yi wa Buhari fatan alheri na samun "gagarumar nasara" kan "babban kalubalen" da ke gabansa - na shugabantar Najeriya - kasar da ta fi yawan al'umma a Afirka tare da gode masa kan "kalamansa na kirki a kanta."
Dubban mutane sun yi zanga-zanga a Sudan don goyon bayan gwamnatin riko
Dubban mutane sun yi zanga-zanga a Khartoum babban birnin kasar Sudan domin nuna goyon baya ga gwamnatin riko ta farar hula da za ta maida kasar kan tafarkin mulkin dimokraddiya.
Wannan na zuwa ne bayan mako guda da aka yi yunkurin juyin mulkin abin da kuma ya sa dangantaka ta kara tsami tsakanin sojoji da jami'an farar hula da ke rike da madafan iko wadanda su ma ya kamata a ce sun gudanar da zabukan kasar.
Kungiyoyin kwadago da kungiyoyi masu fafituka ne suka kira zanga-zangar kuma sun bukaci kafuwar gwamnatin farar hula.
Sai dai jami'an tsaro sun harba hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar.
Shirin da Najeriya ke yi don murnar shekara 61 da samun 'yancinta
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana ranar Juma'a 1 ga watan Oktoba a matsayin hutu don bukukuwan cikar kasar shekara 61 da samun 'yancin kai.
Ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ne ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayyar.
Ya taya 'yan kasar murna yana mai cewa gwamnati ta mayar da hankali wajen kawo karshen dukkan kalubalen da kasar ke fuskanta.
"Kasa mai yawan al'umma kusan miliyan 200 kuma mutanen sun kasance masu basira da kwazo, kuma masu haskawa tamkar daiman. wato matsayin yawan shekarun da kasar ta kai.
"'Yan Najeriya na sheki tamkar daiman a cikin kwali, daga wadanda suke bangaren ilimi zuwa kasuwanci da kirkire-kirkire da wake-wake da fina-finai da nishadi da ado da al'adu.
"Mu ne kasar Afirkan da ke kan gaba a duniya kuma abar alfahari nahiyar Afirka," a cewar Aregbesola.
Najeriya ta samun 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka ne ranar 1 ga watan Oktoban 1960.
Ministan ya jaddada cewa murnar cikar shekara 61 da samun 'yancin Najeriya na da muhimmanci, amma lafiyar 'yan kasar ce gaba da komai a wajen shugaban kasa, musamman ma a wannan lokaci da ake damuwa kan yadda cutar korona nau'in Delta ke ci gaba da bazuwa a kasar.
Don haka ya ce a bana ba za a yi wasu bukukuwa kamar yadda aka saba ba.
Aregbesola ya yi amfani damar wajen yi wa 'yan Najeriya fatan yin bikin wannan rana lafiya.
Ya kuma tunasar da 'yan kasar kan abin da gwarazan da suka yi gwagwarmayar karbo 'yanci suka fada, na cewa duk da bambancin addini da yare da al'ada sun ajiye komai a gefe suka yi gwagwarmayar samun 'yancin kasar tare.
A karshen sanarwar ya ce "dole mu yi aiki tare don ci gaban Najeriya," in ji Aregbesola.
Rahotanni sun ce an fara bukukuwan murnar ranar ne tun ranar Lahadi 26 ga watan Satumba da yin addu'o'i a babban cocin kasa da ke Abuja.
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da matarsa sun halarci taron da sauran manyan shugabannin addinin kirista.
Mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Sudan Ta Kudu na cikin hadari - MSF
Asalin hoton, DAMARIS GIULIANA/MSF
Kungiyar agaji ta Medicins Sans Frontiers ta yi gargadin cewa wadanda ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a Sudan Ta Kudu yanayin lafiyarsu na cikin mummunan hadari, ga shi babu wani taimako.
A farkon wannan watan ne hukumar ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya ta ruwaito cewa kimanin mutum dubu 500 ne ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a cikin yankuna shida daga cikin 10 da kasar ke da su.
Kungiyar ta ce yawan masu bukatar kulawar ta lafiya ya karu musamman idan aka kwatanta da kafin ruwan ya sauko.
Cutar gudawa ce ta fi zama ruwan dare a biranen, sannan ta matsalar numfashi, ga ta fitsari da Malaria da kuma tamowa.
An yanke wa wani masoyin kwallon kafa hukuncin daurin sati 8 a Ingila
Asalin hoton, PL
Wata kotu a Burtaniya ta yankewa wani mai son kwallon kafa hukuncin daurin Makoni takwas a gidan yari bayan ya ci zarafin wani dan wasan kwallon kafa bakar fata ta hanyar amfani da kalaman batanci don nuna wariyar launin fata a shafin intanet.
Simon Silwood ya yi amfani da kalaman nuna wariyar launin fata akan Romaine Sawyers dan wasan tsakiya a kungiyar kwallon kafa ta West Bromwich Albion a watan Janairun daya gabata.
Sai dai Silwood ya dora alhakin kalaman nasa akan wayarsa wanda ta kasa a cearsa ta kadsa gyara masa kuskuremn da ya yi , sai dai kotun ta gano cewa tun asali shi mutum ne mai nuna wariyar launin fata.
Ana kyautata zaton cewa wannan shi ne karon farko a Ingila da Wales da kotu za ta yanke hukuncin dauri nan take akan wariyar launin fata da ya shafi dan wasan kwallon kafa ta shafin intanet
Labaran duniya cikin minti daya
Bayanan sautiMinti Daya Da BBC Na 30/09/2021
Masu ikirarin jihadi na tilasta wa yara 'yan kasa da shekara 12 yaki a Mozambique
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta ce wata kungiya mai ikirarin jihadi a arewacin Mozambique na yin garkuwa da yara maza wasu daga cikinsu shekararsu 12 kuma suna tilasta mu su fada da dakarun gomnati.
Rahotanni sun ce iyaye a garin Palma da ke yankin Cabo Delgado sun fada kungiyar Human Rights watch cewa sun ga yayansu maza rike da bindigogi lokacinda suka dawo tare da sauran mayaka domin su kai hari.
Mayaka masu alaka da kungiyar IS sun rika kai wa kauyuka da garuruwa hari tun bayan shekarar 2017.
Kasashen da dama a yankin kudancin Afrika ta kudu da Rwanda sun tura sojoji zuwa kasar domin su taimaka wa sojojin Mozambique
Tsohon dan majalisar Malawi ya kashe kansa a wajen majalisar kasar
Asalin hoton, TedX
Tsohon dan majalisar Malawi Clement Chiwaya ya kashe kansa ta hanyar harbi a wajen majalisar kasar.
Mr Chiwaya wanda yake amfani da keken masu matsalar kafa tun yana dan shekara biyu bayan fama da matsalar Polio, ya rike matsayin mataimakin kakakin majalisar a 20214 da 2019.
A wani sako da ya bari kafin ya j majalisar a Lilongwe, ya rubuta rikicin da ke tsakaninsa da majalisar kan rikicin mallakar motoci.
Bayan ya fadi zabe sai ya yi ta kokarin sayan motar da aka ba shi wadda ke ba shi damar tuki duk da matsalar kafa da yake fama da ita.
Ya biya kudin motar amma ya zargi majalisar da gaza ba shi damar mallakar motar.
Jaridun cikin gida sun ruwaito cewa ya shiga ofishin majalisar na karbar koke-koke a ranar Alhamis sannan ya harbe kansa.
Wata Gimbiyar Saudiyya ta rasu
Asalin hoton, SAudi
Fadar masarautar Saudiyya ta sanar da rasuwar Gimbiya Hala bint Abdullah bin Abdulaziz.
Cikin wata sanarwa da fadar ta fitar a ranar Alhamis, ta ce za a yi jana'izarta a yau a masallacin harami.
An kashe wani jagoran Musulmin Rohingya a Bangladesh
Asalin hoton, Reuters
Yan sanda a kudu maso gabashin birnin Bangladesh sun
ce wasu ‘yan bindigan da ba’a san ko suwaye ba sun kashe babban shugaban kungiyar
Rohingya ta musulmai a wani sansanin yan gudun hijira a gundumar Cox’s Bazar.
Wasu yan bindiga hudu sun harbi Mohibullah,shugaban kungiyar Arakan
ta yan Rohingya da ke rajin kare hakkin bil adama da samar da hadin kai yayin
da yake tattaunawa da wasu shugabannin al’umma a sansanin Kutupalong.
Har yanzu ‘yan sanda ba su kama kowa ba game da kisan,
kuma babu wata kungiya da ta yi ikirarin kai harin, amma wasu magoya bayan Muhibullah
sun daura zargin mutuwar a kan sojojin kungiyar Arakan Rohingya.
Ana dai zargin kungiyar da kai hare-hare kan jami’an
tsaron Myanmar a yan shekarun nan.
Sojojin Isra'la sun harbe wasu Falasdinawa biyu
Asalin hoton, ED
Sojojin Isra'la sun harbe wasu Falasdinawa biyu. 'Yan sanda da sun ce da safiyar yau alhamis wata mace ta tunkaro ofishinsu da ke kusa da wurin bauta na Temple Mount.
Sun ce ta na dauke da uka a hannunta, tare da zagin 'yan sanda lamarin da ya janyo daya daga cikinsu ya bude mata wuta ta kuma mutu nan take.
Lamari na biyu ya faru ne a kusa da yamma da gabar kogin Jordan a garin Jenin, inda nan ma sojojin Isra'ila suka harbe wani matashi mai shekara 22 a wata taho mu gama tsakaninsu da Falasdinawa.
Aladun daji sun kai wa Shakira hari
Shahararriyar mawakiyar nan Shakira ta ce aladun daji sun kai mata hari a lokacin da ta ziyarci gandun dajin Barcelona tare da danta mai shekara takwas a duniya.
Mawakiyar yar Colombia tace dabbobin sun kai mata hari ne sannan su ka kwace mata jaka su ka gudu da ita cikin daji.
Ta yada labarin ne a shafin ta na Instagram a ranar laraba .
Yayin da ta ke rike da jakarta da ta baci ta na fadin’’ duba yadda aladun daji biyu suka kai mun hari a gandun inda na bar jaka ta’’.
Sun gudu da jaka ta su ka jefar a daji, kuma wayar salula ta tana ciki, mawakiyar ta ci gaba da cewa . sun lalata mun komai.
An ci tararar kamfanin Aritel saboda bata wa abokan huldarsu rai a Malawi
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar da ke kula da harkokin sadarwa ta Malawi ta ci tarar wasu kamfanonin sadarwa na India da ke karkashin Airtel $2.5m saboda gaza biyan abokan huldarsu katin wayar da suka yi masu alkawari.
Hukumar ta kaddamar da wannan binciken ne bayan da ta karbi korafe-korafe masu yawa daga abokan huldarsu.
Ta gano cewa kamfanin Airtel na Malawi ya daina sanya wa abokan huldarsa katin wayar da suke saya a watan da ya yi wata garabasa - wani abu da ya haifar musu da samun gwaggwabar riba sam da dala miliyan 2.5.
Hukumar ta ci tarar kamfanin kan abin da ta kira "yaudarar abokan hulda".
A wannan lokacin ribar da kamfanin ta ci ta ninka abin da ta saba ci a shekara.
An yanke wa tshon shugaban Faransa hukuncin zaman gidan yari na shekara guda
An yanke wa tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy
shekara daya a gidan yari saboda daukar
nauyin tawagar yakin neman zaben sa da bai yi nasara ba. Mr Sarkozy ya sake
tsayawa takarar shugabancin kasar a wannan shekarar.
Wata kotu da ke Paris ta kama Mr Sarkozy mai shekara 66 da
laifin kashe miliyoyin yuro yayin yakin neman zabensa fiye da yadda doka ta
tanada.
Ba a tsara cewa zai yi zaman gidan yari na dogon lokaci ba,
amma za a yi masa daurin talala ne a gida a hukuncin da kotun ta yanke.
Ana sa ran zai iya daukaka
kara kan hukuncin.
Mr Sarkozy a watan Maris
da ya gabata ya kalubalanci wani hukunci da aka yanke masa a wata kara na
daban.
Wannan dai shi ne karo na farko
da aka tuhumi tsohon shugaban Faransa da laifin cin hanci.
Kim Jung-un ya yi gargadin cewa gwamnatin Biden na matsawa kasarsa
Asalin hoton, AFP
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jung-un ya maida goron gayyar da Amurka ta bada na tattaunawa tsakanin kasashen biyu, inda ya ce ta na son nuna dagawa da mamaya kamar yadda ta saba.
Sai dai Mista Kim ya amince su ci gaba da tattaunawa da makofciyarsa Koriya ta Kudu a farkon mako mai zuwa, a matsayin matakin farko na sasantawa dangantaka tsakaninsu.
Ya shaida wa majalisar ministocinsa cewa, gwamnatin shugaba Biden, na matsawa kasarsa kamar yadda gwamnatin shugaba Donald Trump ta yi a lokacin na ta mulkin.
A karshen Kim y ace Koriya ta Arewa na bukatar kera makamai masu karfin gaske domin maganin kasashen da ke son yin katsa landana harkokinta.
Kotu ta ki bayar da belin Sheik Abduljabbar Kabara
Babbar kotun musulunci ta Jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta ki amincewa da bayar da belin Malamin addinin nan Sheik Abduljababr Nasir Kabara.
Cikin wani zama da aka yi a ranar Alhamis, alkalin kotun Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola, ne ya ki amincewa da bukatar da Barista Umar Muhammad wanda shi ne ke jagorantar lauyoyin Abduljabbar ya gabatar.
Gabanin fara shari’ar lauyoyin Abduljabbar sun bukaci da a ba su kwafin shari’ar, tare da kira ga masu kara da su gabatar da shaidunsu a zama na gaba domin a fara sauraro.
Alkalin ya dage saurar karar zuwa ranar 14 ga watan October na gobe.
Fafaroma ya yi jawabi kan matsalar tsaron Najeriya
Asalin hoton, Getty Images
FaforomaFrancis ya yi kira ga gwamnatin Najeriya ta tabbatar da kare rayukan
al’ummar kasar biyo baya ga mugayen hare-haren da ke faruwa a arewacin kasar.
Fafaroman ya yi addu’a ga wadanda su ka
rasa rayukansu da kuma wadanda su ka ji rauni sakamakon rashi tsaro, ganin
harin da aka kai jihar Kaduna a karshen makon da ya gabata wanda ya jawo
mutuwar gomman mutane.
Ranar Laraba a wani zama da ya ke yi da
magoya bayan sa duk sati a fadar Vatican,ya bayyana rashin jin dadin sa game da
harin da aka kai ranar Lahadin da ta gabata a kauyukan Madamai da Abun da ke
arewacin Nigeria.
Ya
kara da cewa,‘’ina fatan za’a tabbatar da kare rayuwar ko wanne dan kasa.”
Yankin arewacin Najeriya na fama da rashin
tsaro na tsawon shekaru, wanda ya hada da hare-haren yan fashin daji da na masu
garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.
Wajibi gwamnatin Najeriya ta kare makarantu daga hare-hare - Hukumar kare hakkin dan adam
Shugaban hukumar kare hakkin dan adam ta kasa Tony Ojukwu ya shawarci gwamnatin Najeriya kan kare makarantu daga hare-haren 'yan bindiga.
Ya yi wannan kiran ne a ranar Laraba a Abuja a wani taron kasa da kasa na hudu domin tabbatar da tsaron makarantu a kasar.
Ya ce hare hare kan makarantu da musamman kisa da sace dalibai, zai haifar da mummunan tasiri ga lamuran karatu a kasar.
Ya ce za a yi irin wannan taron a karon farko a Najeriya, wanda zai mayar da hankali kan matsalar tsaro da yadda ta shafi ilimi a kuma tattauna kan hanyoyin tsaron da za a inganta ilimi a Najeriya ga yara masu tasowa.