Mun kashe tirliyan 8.9 kan manyan ayyuka a 2020 - Osinbajo

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya

Rahoto kai-tsaye

Imam Saleh and Buhari Muhammad Fagge

  1. 'Yan sanda sun kama mutum uku da ake zargi da sace dalibai a Kaduna

    Police

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan sanda a Najeriya sun ce sun cafke mutum uku da ake zargi su na da hannu a sace sama da dalibai 120 na wata makaranta da ke jihar Kaduna a arewa maso yammacin kasar.

    Akallah 'yan bindiga ashirin da biyar ne suka sace daliban makarantar Bethel Baptist a watan Yuli da ya wuce.

    A ranar lahadi 20 daga cikin daliban da ake tsare da su suka kubuta, sai dai har yanzu, 'yn bindigar na ci gaba da rike dalibai 20 a hannunsu.

    Rahotanni sun bayyana cewa. Iyayen yaran sai da suka biya kudin fansa kafin a sake su, ko da yake ba a bayya ainahin adadin abin da suka ba da ba.

  2. Maraba

      • Marubuci, Imam Saleh
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

    Barkanku da kasancewa da mu a wannan shafin, wanda ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta kamar Nijar da Kamaru da Ghana da ma sauran kasashen duniya.

    Sunana Imam Saleh, da fatan za ku kasance da mu tsawon wannan rana.

    Muna kwarya..

    Asalin hoton, Gett

    Bayanan hoto, Muna kwarya..